'Na ga yadda ake harbin Falasɗinawa a wuraren karɓar abinci a Gaza'

An sha sukar ayyukan GHF saboda ake tilasta wa mutane zuwa wuraren da ake tafka yaƙi domin karɓar abinci

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An sha sukar ayyukan GHF saboda ake tilasta wa mutane zuwa wuraren da ake tafka yaƙi domin karɓar abinci
    • Marubuci, Lucy Williamson
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC a Gabas ta Tsakiya
    • Aiko rahoto daga, Jerusalem
  • Lokacin karatu: Minti 4

Wani tsohon ma'aikacin agaji da ya yi aiki a Zirin Gaza tare da ƙungiyar raba kayan tallafi wadda Amurka da Isra'ila ke ɗaure wa gindi ya faɗa wa BBC cewa ya ga abokan aikinsa na buɗe wa Falasɗinawa wuta waɗanda ba su ɗauke da makami.

Ya ce a wani lokaci, wani mai gadi ya buɗe wuta daga kan wani tsauni da bindiga mashinga (mai sarrafa kanta) saboda wani rukunin mata da yara da tsofaffi na ba su matsawa da sauri daga wurin karɓar tallafin.

Da aka tambaye ƙungiyar mai suna Gaza Humanitarian Foundation (GHF), ta amsa da cewa zargin ƙarya ce tsagwaro.

Sun ce mu duba wata sanarwa da suka fitar da ke cewa babu wani farar hula da aka taɓa harbi a wurin raba kayan agajin na GHF.

Ma'aikacin agajin ya aiko wa BBC wani bidiyo da aka ɗauka a cikin sansanin da GHF ke raba kayan tallafi a Zirin Gaza

Asalin hoton, SUPPLIED

Bayanan hoto, Ma'aikacin agajin ya aiko wa BBC wani bidiyo da aka ɗauka a cikin sansanin da GHF ke raba kayan tallafi a Zirin Gaza

GHF ta fara aikinta a Gaza ne a ƙarshen watan Mayu, inda take raba kayan marasa yawa a wasu keɓantattun wurare da ke tsakiya da kuma kudancin zirin. Matakin ya biyo bayan datsewar da Isra'ila ta yi na hana shiga da komai Gaza tsawon mako 11.

An sha sukar tsarin saboda yadda yake tilasta wa mutane bi ta wuraren da ake ɓarin wuta zuwa sansanonin 'yan ƙalilan.

Tun bayan da GHF ta fara aiki, dakarun Isra'ila sun kashe sama da Falasɗinawa 400 da ke yunƙurin karɓar abinci a wuraren, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya da mazauna yankin.

Isra'ila na cewa an ƙirƙiri sabon tsarin ne saboda hana dakarun Hamas samun abincin.

Da yake ci gaba da bayyana abin da ke faruwa a wuraren, tsohon ɗankwangilar ya ce: "Yayin da hakan ke faruwa, wani mai gadin da ke tsaye kan wani tudu da ke kallon hanyar fita daga wurin, ya buɗe wuta da harbi kamar 15 zua 20 a kan mutane.

"Take wani Bafalasɗine ya fadi ƙasa a sume. Sai kuma wani mai gadin da ke tsaye shi ma ya zo yake cewa, 'kai, ina ganin ka kashe ɗaya'. Sai kuma suka fashe da dariya."

Mutumin da ya nemi mu ɓoye sunansa, ya ce shugabannin GHF sun ce abin da ya faru tsautsayi a lokacin da ya kai rahoto, suna cewa wai ƙila mutumin "tuntuɓe kawai ya yi", ko kuma "gajiya ce ta saka ya suma".

GHF ta yi iƙirarin cewa mutumin da ya ba mu labarin "tsohon ɗankwangila ne da ya tafi da fushi" saboda sun kore shi daga aiki sakamakon rashin ɗa'a, iƙirarin da ya musanta. Ya nuna mana shaidar karɓar albashinsa na mako biyu da ke tabbatar da cewa an ci gaba da biyansa har bayan ya bar aikin.

Wani hoto da aka bai wa BBC na nuna dogon layi na masu karɓar abinci a wani wuri da aka kewaye da waya

Asalin hoton, SUPPLIED

Bayanan hoto, Wani hoto da aka bai wa BBC na nuna dogon layi na masu karɓar abinci a wani wuri da aka kewaye da waya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mutumin da muka yi magana da shi ya ce ya yi aiki a duka wuri huɗu da GHF ke bayar da abincin, kuma ya bayyana cewa ana zalinci sosai ba tare da bin wasu dokokin kirki ba.

Ya ce ba a bai wa masu gadin wasu dokokin aiki da suka kamata a bi wajen hulɗa da farar hula, kuma wani jagora ya taɓa faɗa musu cewa: "Idan kuka ga ana yi muku barazana ku kashe mutum kawai, daga baya sai a yi bincike".

Ɗabi'un da ake nunawa a wurin ya yi kama da kamar a ce "ai nan Gaza ce saboda babu wasu ƙa'idoji."

"Idan wani Bafalasɗine na ficewa daga sansanin ba tare da nuna wata alamar barazana ba amma duk da haka muna yi musu harbin gargaɗi kuskure ne, mun aikata laifi ciki sakaci," a cewarsa.

Ya faɗa mana cewa kowane sansani na da kyamarar tsaro da ke ɗaukar abubuwan da ake yi, kuma iƙirarin da GHF ke yi cewa ba a taɓa kashe kowa ba a wurin "zallar ƙarya ce".

GHF ta ce harbin bindigar da aka ji a bidiyon da aka aika wa BBC na sojojin Isra'ila ne.

Jagororin na kiran 'yan Gaza a matsayin wani "garken dabbobi", in ji tsohon ma'aikacin, "suna nuna cewa mutanen ba su da wata daraja".

Ya ƙara da cewa akan cutar da Falasɗinawan ta wasu hanyoyin daban a wuraren GHF. Misali, ɓurɓushin gurneti kan fado musu, ko a fesa musu sinadari, ko kuma a dinga matse su a jikin wayar shinge.

Ya ce ya sha ganin Falasɗinawan da aka jikkata, ciki har da wani mutum da aka fesa wa kwalaba guda ta sinadari mai yaji, da wata mace da ƙarfen makamin gurneti ya faɗo mata bayan an harba shi cikin jama'a.

"Ƙarfen ya faɗa mata kai-tsaye a ka kuma ta faɗi ƙasa nan take a sume," a cewarsa. "Ban sani ba ko ta mutu, amma dai a tabbata ba ta motsi kuma a sume take."

A farko makon nan ƙungiyoyin agaji fiye da 170 suka yi kiran a haramta ayyukan GHF. Ƙungiyoyin ciki har da Oxfam da Save the Children, sun ce dakarun Isra'ila da 'yan bindiga "na yawan" buɗe wa Falasɗinawa wuta a wurin karɓar abinci.

Isra'ila ta musanta cewa sojojinta na kashe masu neman abinci da gangan, kuma ta ce tsarin GHF na tallafa wa mutanen da ke buƙatar abinci ba tare da Hamas ta kawo cikas ba.

GHF ta ce ta rarraba ƙunshin abinci miliyan 52 cikin mako biyar, inda ta yi iƙirarin cewa sauran ƙungiyoyin suna kallo ake sace musu kayayyaki na tallafin.

Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi a Zirin Gaza ne a matsayin martani kan harin da mayaƙan Hamas suka kai cikin ƙasarta ranar 7 ga watan Oktoban 2023, wanda ya jawo kashe kusan mutum 1,200 da kuma sace wasu 251 zuwa cikin Gazan.

Tun daga lokacin, Isra'ilar ta kashe aƙalla Falasɗinawa 57,130, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Gaza ta bayyana.