Yajin aiki: Me ya sa gwamnati ke yi wa ma'aikata barazana da albashi?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist
- Lokacin karatu: Minti 6
A farkon wannan makon ne Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya, NARD ta tsunduma yajin ne gargaɗi na kwana bakwai, don matsa wa gwamnatin ƙasar lamba wajen ceto abokiyar aikinsu, Dokta Ganiyat Popoola, da aka sace a jihar Kaduna, cikin watan Disambar 2023.
To sai dai gwamnatin Najeriyar ta yi barazanar ɗaukar matakin tsarin 'ba aiki, ba albashi,' na tsawon kwanakin da likitocin suka ɗauka suna yajin aikin..
Hakan na nufin za a yanke musu albashi na tsawon kwanakin da suka ɗauka ba sa zuwa aiki.
A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar, Ado Bako, ya fitar, ya ce gwamnatin ta sanar da aiwatar da dokar “ba aiki, babu albashi” na tsawon kwanakin yajin aikin, ma'ana gwamnati za ta riƙe albashin likitocin da ke yajin aiki har tsawon kwanakin da suka ɗauka suna yajin aikin, kamar yadda dokar ƙwadago ta tanada.
Bako ya ƙara da cewa, ma’aikatar tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro suna bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an sako Dakta Popoola, kuma a halin da ake ciki, akwai tattaunawa mai ƙarfi da ake yi don ganin a kuɓutar da ita daga hannun masu garkuwa da mutanen.
Wannan ba shi ne karon farko ba da gwamnatin Najeriya ke ɗaukar irin wannan matakin na 'ba aiki, ba albashi ba' a kan ma'aikata.
A baya can an yi amfani da dokar a kan malaman jami'a, lokacin da Ƙungiyar ASUU ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.
Dakatar albashin malaman jami'ar a lokacin ya jefa da dama daga cikinsu cikin ƙuncin rayuwa.
Ko bayan janye yajin aikin, an cigaba da kai ruwa rana a albashin nasu da aka riƙe.
Tsari 'ba aiki ba albashi' barazana ce kawai - Likitoci

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
BBC ta tuntuɓi Likitocin Masu Neman ƙwarewar, NARD, wadda ta ce snarwar gwamnatin ba komai ba ce face barazana.
Shugaban ƙungiyar reshen Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano, Dokta Isa Tijjani Dawaki, ya ce irin wanan mataki na gwamnan ba yau suka fara jin sa ba.
"Wannan barazana ta babu aiki babu albashi dama ba yau muka saba ji ba, kuma ni a ganina, wannan barazana farfaganda ce, saboda a nuna mana kamar mun yi abin da bai dace ba. Kuma wannan yajin aiki da aka yi ba wai an yi shi ne a kan rashin ƙa’ida ba'', in ji shi.
"Sannan kuma me ya sa ma aka shiga wannan yajin aikin, yajin aikin nan na gargaɗi ne kuma ana yajin aikin gargaɗi ne idan abu ya ci tura, sai a ɗan nuna fushi a kan abin da ya kamata a yi, ba a yi ba. ita wannan baiwar Allah da aka kwashe su a gida a wajen aikinsu wato a gidajen da aka ba su na asibiti aka kwashe su tsawon wata takwas ke nan,'' kmar yadda ya shaida wa BBC.
Ya ce saboda yadda aka yi duk mai yiwuwa domin ganin an yi abin da ya dace, amma ba a yi ba, shi ya sa suka yi yajin aikin domin nuna fushinsu.
A game da maganar da ake yi cewa sun bar marasa lafiya a asibiti, alhali sun yi rantsuwa kuwa, Dokta Isa cewa suma suna buƙatar lafiyarsu da tunaninsu su cika, kafin su iya kula da marasa lafiya.
"Idan ka ga likitoci suna yajin aiki, suna yi ne saboda kishin ƙasa. Duk likitan da ka yana aiki a Najeriya, to yana da kisin ƙasar ne saboda ana neman likitoci musamman ƴan Najeriya a ƙasashen waje, inda za a biya su kuɗaɗe masu yawa. Burinmu shi ne mahukunta su yi gyara," in ji shi.
A game da rantsuwar da suka yi na kare rayuka kuwa, likitan ya ce tsaron lafiyarsu shi ma yana da muhimmanci.
“Ai Hausa na cewa sai da ruwan ciki ake jan na rijiya. Rantsuwar ma da aka yi akwai cewa sai ka fara samun lafiyar kanka da kuma wurin da kake aiki saboda idan aka ce ba ka da natsuwa, hankalinka ba a kwance yake ba. Kana tunanin yau ko gobe abu kaza zai iya faruwa, ai ba zai samu natsuwar da yake buƙata wajen kula da ma’aikata ba."
Me doka ta ce kan ƙin biyan albashi saboda yajin aiki?

Ana yawan kai ruwa rana tsakanin ma'aikata da gwamnati idan an tafi yajin aiki, da kuma yadda a lokuta da dama rashin biyan albashin yake jefa wasu ma'aikatan cikin wani hali.
Wannan ya sa BBC ta tuntuɓi Barista Abba Hikima, wani lauya mai zaman kansa a Kano, domin ko doka ta amince da wannan matakin na gwamnati.
Barista Abba ya ce gwamnati na da damar ƙin biyan ma'aikaci albashi idan ma'aikacin bai zo aiki ba.
A cewarsa, "Ita wannan doka ta 'ba aiki, ba albashi' tsohuwar doka ce da ta samo asali daga dokokin Turawa. Waɗannan dokokin an zo an saka su a dokokinmu na Najeriya. Kamar sashe na 43 na dokar da take nuna yadda za a tafiyar da taƙaddama tsakanin ƴan ƙwadago da gwamnati ta nuna cewa idan ana yajin aiki, to ba lokacin aiki ba ne ke nan, don haka ba za a biya albashi ba tunda ba a yi aiki ba."
Barista Abba Hikima ya ce yawanci bayan yajin aikin, idan aka zo matakin janye yajin aikin, "a kan buƙaci a dawo da albashin da ba a biya ba a cikin sharaɗin janye yajin aiki."
Ya ƙara da cewa, "Amma lallai akwai shi a cikin doka, duk da cewar dokar ta ba da dama idan an zo za a yi sulhu, a tattauna a ga mafitar da za ta yi wa kowa daɗi."
Game da ko doka ta ba ma'aikata damar gudanar da yajin aiki, Barista Abba ya ce lallai doka ta ba ma'aikata dama idan sun bi wasu ƙa'idoji, su gudanar da yajin aiki.
"Wannan ya sa bai kamata a yi wani abu da zai cutar da su ba saboda tafiya yajin aikin. Amma ita ma kuma gwamnati doka ta ba ta dama ba za ta biya albashi ba idan ba a yi aiki ba."
Lauyan ya ƙara da cewa ba ma iya gwamnati ba, duk wani wanda ya ɗauka aiki, idan ma’aikatan suka janye daga aiki, shi ma yana da dama ya ƙi biyan albashi.
Sai dai Barista Abba ya ce a fahimtarsa ba doka ba ce mai kyau, "saboda sau tari za ka ga idan ma’aikata sun tafi yajin aiki, to tura ce ta kai bango."
Sai dai ya ce masu tafiya yajin aikin, musamman likitoci da suka yi rantsuwar kare lafiyar al'umma, akwai matsala a tafiyarsu yajin aiki.
"Duk da cewa suma akwai buƙatar a kula da nasu haƙƙoƙin, amma matakan da ake bi wajen tafiya yajin aiki ni ban gamsu cewa sun cika ba, wanda hakan ya sa nake ganin za a yi ɗaukar mataki a kansu, musamman idan sakamakon hakan an samu cutuwa ko rasa rai, to za a iya ɗaukar matakin shari’a a kansu," kamar yadda ya shaida wa BBC
Wace ce Dokta Popoola da aka sace?
A watan Disamban 2023 ne wasu 'yan bingida suka sace likitar, wadda take aiki a Asibitin Ido na ƙasa, wato 'National Eye Center' da ke Kaduna.
Ƴan bindiga sun sace Dokta Popoola ce tare da mijinta, wanda hafsan sojan sama ne da wani ɗan uwanta mai suna AbdulMugniy Folaranmi, wanda ɗalibi ne a makarantar Airforce Institute of Technology da ke Kaduna.
Kodayake 'yanbindigar sun sako mijin nata, amma sun cigaba da riƙe ta, da ɗan uwanta bayan biyan kuɗin fansa.
Shugaban Ƙungiyar NARD, Dokta Dele Abdullahi ya ce bayan ƴan uwan likitar sun yi nasu, shi ne suma a ƙungiyance suka ga ya dace su ɗauki nasu matakin a madadin abokiyar aikinsu ɗin da take hannun masu garkuwa, wanda hakan ya sa suka tsunduma yajin aikin na gargaɗi.










