Tinubu ya sanar da sabon albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikatan Najeriya

Asalin hoton, PRESIDENCY NIGERIA
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da naira 70,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikatan gwamnatin ƙasar.
Tinubu ya sanar da sabon albashin ne a ganawarsa da wakilan ƙungiyoyin ƴan ƙwadago na ƙasar a ranar Alhamis.
Ministan yaɗa labaru na Najeriya, Mohammed Idris ya sanar da manema labaru cewa "ina farin cikin shaida muku cewa a yau (Alhamis) ƙungiyoyin ƴan ƙwadago na Najeriya da Gwamnatin Tarayya sun amince da wani ƙari a kan naira 62,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta.
Sabon albashin mafi ƙanƙanta da ake sa ran shugaban ƙasa zai gabatar wa Majalisar Dokokin Tarayya shi ne naira 70,000."
Wannan na zuwa ne bayan kwashe tsawon lokaci ana taƙaddama tsakanin ƴan ƙwadago da gwamnatin Najeriya game da sabon albashin mafi ƙanƙanta ga ma'aikata.
Wannan dai ya gaza a albashi mafi ƙanƙanta da ƙungiyoyin ƙwadagon suka gabatar na naira 250,000.
Sai dai wannan sabon albashin ya nunka tsohon albashin mafi ƙanƙanta na 30,000, wanda aka kwashe tsawon lokaci ana amfani da shi.
Tashin farashin kayan masarufi ya yi ƙamari a ƙasar mai yawan al'umma sama da miliyan 200.
Cire tallafin man fetur da shugaban ƙasar ya yi a ranar da ya karɓi mulki cikin watan Maris na shekara ta 2013, ya sanya farashin kayan masarufi ya nunnunka, lamarin da ya jefa al'ummar ƙasar cikin mummunan hali.
A watan Yuni, alƙaluma daga Hukumar ƙididdiga ta Najeriya sun nuna cewa hauhawar farashi ta kai 34.2%, mafi yawa a cikin kusan shekara talatin.
Ƙungiyar ƙwadago ta dage kan cewa wajibi ne gwamnatin ƙasar ta yi wa ma'aikata ƙarin albashi domin yin daidai da halin da ake ciki na rayuwa.
Baya ga ƙarin albashin mafi ƙanƙanta zuwa 70,000, shugaban na Najeriya ya kuma yi wa ma'aikatan wasu alƙawurra.
Kamar yadda ministan yaɗa labaru Mohammed Idris ya faɗa, "gwamnatin Najeriya za ta narkar da maƙudan kuɗaɗe a ɓangaren samar da kayan more rayuwa.
Gwamnatin za ta kuma ƙara zuba kudi a ɓangaren makamashi mai tsafta, tare da samar da ƙarin motocin bas masu amfani da man CNG."
Martanin ƙungiyar ƙwadago
A lokacin da yake jawabi ga manema labaru, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC, Joe Ajaero ya ce "a halin da ake cikin yanzu an tsaya ne kan naira 70,000, amma wani abin jin daɗi shi ne ba za mu tsaya har sai nan da shekara biyar kafin a sake duba albashin mafi ƙanƙanta ba.
A maimakon mu jira sai bayan shekara biyar kafin a sake yin ƙari, yanzu za a iya yin ƙari sau biyu a cikin shekara biyar."

Asalin hoton, STATE HOUSE
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Batun samar da matsaya kan albashi mafi ƙanƙanta a Najeriya ya daɗe yana tayar da ƙura a Najeriya tun bayan zuwan sabuwar gwamnatin Bola Tinubu.
Lamarin da ya sanya shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya kafa kwamitin da zai zauna domin samun matsaya.
Kwamitin ya ƙunshi wakilai daga ɓangaren Gwamnatin Tarayya, da ƙungiyar ƙwadago, sai kuma gwamnonin jihohi da wakilan ɓangaren ƴan kasuwa masu zaman kansu.
Duk da haka, a ranar 3 ga watan Yuni, ƙungiyoyin ƙwadagon na Najeriya sun gudanar da wani yajin aiki a faɗin ƙasar, inda suka dakatar da ayyuka cak, bisa zargin cewa gwamnati na jan ƙafa wajen cimma matsaya kan sabon albashin mafi ƙanƙanta.
A wannan lokaci ne suka rufe ma'aikatun gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, sannan suka datse babban layin lantarki na ƙasar, wani abu da ya jefa ƙasar baki ɗaya cikin duhu.
Sai dai a zaman ƙarshe da kwamitin ya yi a cikin watan Yunin, ƙungiyar ƙwadago ta tsaya a kan cewa ya kamata sabon albashi mafi ƙanƙanta a Najeriyar ya kasance naira 250,000, sai dai ɓangaren gwamnati ya tsaya ne a akan naira 62,000.
Daga ƙarshe kwamitin ya miƙa rahoto ga shugaban ƙasa, domin yin nazari tare da ɗaukar matsaya.
Tun wancan lokaci ne ba a ji wani abu ba daga ɓangaren gwamnati da kuma na ƴan ƙwadagon har sai wannan Alhamis ɗin, lokacin da shugaban na Najeriya ya kira jagororin ƙungiyar ƙwadago domin tattaunawa.











