Waɗanne ma'aikata ne suka cancanci albashi mafi ƙanƙanta na 70,000 a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya ce dukkan ma'aikatan Najeriya da ke aiki a ma'aikatun gwamnati ko masu zaman kansu sun cancanci cin moriyar ƙarin albashi mafi ƙanƙanta na naira dubu 70 da majalisar dokokin ƙasar ta amince.
Akpabio wanda ya bayyana hakan a zaman majalisar na ranar Talata bayan amince wa da ƙudirin albashin mafi ƙanƙanta ya zama doka, ya ce:
“Idan maɗinki ne kai sai ka ɗauki wasu mutane aiki, ba za biya su abin da ya gaza naira dubu 70 ba. Haka idan ke uwa ce da ke da sabon jaririn da ki ke son ɗaukar wadda za ta kular miki da shi, to ba za ki biya ta albashi ƙasa da abin da doka ta amince shi ne mafi ƙanƙanta ba... dokar ta shafi kowa da komai.
Haka ma idan ka ɗauki direba ko mai gadi, to ba za ka biya su ƙasa da naira dubu 70 ba. Ina matuƙar jin daɗin cewa wannan abu ya zama doka, kuma yanzu mun bar wa masu ɗaukar aiki su yi aiki da dokar." In ji Sanata Akpabio.
Me doka ta ce kan ma'aikatan da za su ci moriyar 70,000?
Saɓanin abin da shi shugaban majalisar ya faɗa a zauren majalisar, dokar albashi mafi ƙanƙanta ta 2019 wadda aka yi wa kwaskwarima a 2024 ta bayyana cewa:
"Dukkan wani mai ɗaukar ma'aikata dole ne ya biya ma'aikatan da ke masa aiki abin da bai gaza naira dubu 70 ba a kowane wata, sai idan wannan doka ta bayar da damar biyan wani abu na daban" Kamar yadda ƙaramin sashen na ɗaya na babban sashe na uku na dokar ya tanada.
Ƙaramin sashe na biyu na babban sashe na uku na dokar kuma ya yi ƙarin haske cewa " albashi mafi ƙanƙanta shi ne kuɗi mafi ƙanƙanta da mai ɗaukar aiki doka ta buƙaci ya biya ƙaramin ma'aikaci a kowane wata da ke ƙarƙashinsa."
Shi ma ƙaramin sashe na uku na babban sashen na ukun na dokar ya yi gargaɗi cewa "duk wata yarjejeniyar biyan albashin da bai kai ƙimar albashin mafi ƙanƙanta na ƙasa (Najeriya) ba to haramtacce ne."
Ma'aikatan da doka ta keɓe daga 70,000
Sai dai kuma ƙaramin sashe na ɗaya na babban sashe na huɗu na dokar ya ce biyan albashin mafi ƙanƙanta na naira dubu 70 bai shafi wasu ma'aikatu ba da ya lissafa kamar haka:
- Ma'aikatun da ke da ma'aikatan wucin-gadi.
- Masu dillanci waɗanda ma'aikatu ke biyan su daidai da aikin da suke yi a wani ƙayyadadden lokaci.
- Ma'aikatun da masu yi musu aiki ba su kai mutum 25 ba.
- Ma'aikatan da ke aiki na lokaci zuwa lokaci kamar masu aikin ƙwadago a gona.
- Ma'aikatan jirgin sama ko na ruwa waɗanda dokokin aikinsu suka shafa
Fashin baƙin masana shari'a
Masana shari’a sun fara sharhi kan dokar tun bayan wani bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta na Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godswill Akpabio da ke cewa, ko mai raino mutum ya dauka sai ya rika biyanta naira 70,000 a kowanne wata a matsayin mafi ƙarancin albashi.
"Gaskiya ne sashen dokar na uku cewa ya yi duk wanda yake maka aiki kuma kake biyan sa wata-wata, to dole ne ka ba shi daidai da abin da dokar ta ce na mafi ƙanƙantar albashi na naira 70,000. Ko da mai shara ne ko mai kula da yara ne." In ji Barista Isma’il Ashir lauya mai zaman kansa a jihar Kadunan Najeriya.
Mene ne abu na gaba?
Yanzu haka dai majalisar dokokin Najeriyar ta aike da wannan ƙudirin dokar ga shugaban ƙasa domin saka hannu, inda za ta zama doka wadda kuma saɓa mata ka iya janyo hukunci.
Idan ya zama dokar ƙasa to duk ma'aikacin da ya cancanci cin moriyar wannan ƙayyadadden albashi amma bai samu ba ka iya garzaya wa kotun ƙwadago ta ƙasa domin kai koke wato National Industrial Court.
"Yanzu muna jiran shugaba Tinubu ya saka wa dokar hannu sannan mu kuma za mu fito da tsare-tsare da yadda za mu tabbatar da cewa mun sanya ido domin ganin ma'aikata su karɓi albashin da ya dace da su. Musamman za mu bibiyi jihohi da kamfanoni masu zaman kansu." In ji kwamared Nasir Kabir na kungiyar ƙwadago ta Najeriya.











