Nawa ya kamata ma'aikaci ya ɗauka a matsayin albashi mafi ƙaranci a Najeriya?

...

Asalin hoton, Getty Images

Wasu jihohi da kamfanoni masu zaman kansu da masana a Najeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu kan maganar da shugaban ƙungiyar ƙwadago na kasar, Joe Ajaero ya yi kan albashi mafi ƙaranci da ƙungiyar ke son a bai wa ma'aikata a kasar.

Mista Ajaero dai ya yi wata hira da gidan talbijin na Arise Television a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce akwai yiwuwar su nemi albashi mafi ƙaranci ya zama naira miliyan ɗaya idan dai har darajar naira ta ci gaba da taɓarɓarewa.

A watan da ya gabata ne dai gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti domin yin duba kan albashi mafi karanci a ƙasar.

A watan Disamba ne kuma ministan yaɗa labaran kasar, Mohammed Idris ya shaida wa 'yan jarida cewa sabon tsarin albashin mafi ƙaranci zai fara aiki ranar 1 ga watan Afrilun 2024.

Nawa ne ya dace da ƙaramin ma'aikaci?

Ibrahim Abubakar Walama, mamba ne a kwamitin ƙoli na ƙungiyar ƙwadago, NLC na ƙasa, kuma ya shaida wa BBC cewa yana goyon bayan neman biyan naira miliyan ɗaya a mtsayin albashi mafi ƙaranci a ƙasar.

Ya ce idan aka yi la'akari da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki da ake samu tun bayan janye tallafin mai da kuma faɗuwar darajar kuɗin ƙasar, naira, idan aka kwatanta da dalar Amurka, naira miliyan ɗaya ne ya dace ya zama albashi mafi ƙaranci ga ma'aikata a ƙasar.

Idan kika duba kayan abinci nawa naira miliyan ɗaya za su saya? Nawa shinkafa take? nawa masara? yadda abinci ke ci gaba da tsada a ƙasar. A cewarsa.

Walama ya ce: "ba wai gwamnatin ba ta da kuɗin biya ba ne, sai dai ta ƙi biya, amma mun san akwai kuɗin."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jami'in na NLC ya ambato wani babban lauya a ƙasar, Femi Falana na cewa a watan Aprilun shekarar da ta wuce, ƙasar ta rabawa gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi sama da naira biliyan 600.

Amma bayan an janye tallafin mai, a watan Yunin 2023 kuɗaɗen da aka rarraba sun ƙaru zuwa 1.9 tiriliyan naira. Haka ma a watan Disamba, gwamnatin tarayyar ta raba naira tiriyan 1.7 ga jihohi da ƙananan hukumomi. Kamar yadda ya ce lauya Falana ya bayyana.

Sai dai ya ce naira miliyan ɗaya ta yi ne kawai da NLC ta ke son miƙa wa kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa don duba sabon albashi mafi ƙaranci a ƙasar. "Amma ba duk abin da mutum ke so yake samu ba," don haka a cewarsa "akwai yiwuwar a sauko zuwa wani mataki da za su daidaita a nan gaba."

"Ƙungiyoyin ƙwadago na da wakilai shida zuwa bakwai a kwamitin, kuma za a bi abin cikin gaskiya da fahimtar juna, za a duba tsadar rayuwar da mutane ke ciki a ƙasar. " In ji Walama.

Inda ya bayyana cewa wakilansu da ke cikin kwamitin da mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya ƙaddamar a ƙarshen watan Janairun da ya gabata, za su kawo rahoton abin da ya faru a kwamitin ga ƙungiyar ta NLC, wadda za ta kira taro na ƙasa don cimma matsaya a kan sabon albashin mafi ƙaranci.

Ra'ayin masana

To sai dai masana sun fara bayyana ra'ayoyinsu kan batun albashi mafi ƙaranci ga ma'aikatan ƙasar ta Najeriya.

Dokta Bashir muhammed Achida, malami ne a sashen ilimin tsimi da tanadi na jami'ar Usmanu Ɗanfodio da ke Sokoto a arewacin ƙasar kuma ya bayyana cewa akwai abubuwan da ake dubawa idan ana maganar albashin mafi ƙaranci na ma'aikaci.

Ya ce ana duba irin aikin da ma'aikaci ke yi sannan a biya shi abin da ya dace na haƙƙinsa a matsayin albashi.

Idan ma'aikacin kamfani da ke kawo kuɗi ne ya zamo aikin da yake yi na taimakawa wajen samun riba, idan ma'aikacin gwamnati ne ya zama aikinsa na amfanar al'umma.

Yayin da hauhawar farashin kayayyaki kuma da faduwar darajar kudin ƙasar, masanin ya alaƙanta su da yawan ayyukan da ake yi da kuma irin ƙirƙire-ƙirƙiren da ake yi a cikin ƙasa. Waɗanda a cewarsa su suke taimakawa wajen gina arzikin ƙasa.

Inda ya ƙara da cewa hauhawar farashi da faɗuwar darajar kudin da ake samu a Najeriya na nuni da cewa abinci da ake da shi a cikin ƙasar da ayyukan da ake yi ba su kai yawan kudin da ke zagayawa ba.

Ƙarin albashi ne mafita ko daƙile hauhawar farashi?

Dokta Bashir na ganin ƙarin albashi mafi ƙaranci ba shi ba ne mafita daga matsalar tsadar rayuwar da ake fuskanta. Yana mai nuni da cewa batun tayin naira miliyan ɗaya da ƴan ƙwadago ke magana, a ina gwamnatin za ta samu kuɗin?

"Yana iya yiwuwa a buga kuɗaɗen, amma babu daraja. Yanayin zai iya zama sai ka kashe kuɗaɗe masu yawa wajen sayen abu ƙalilan."

Ya buga misali da cewa gwamnatocin da suke wuce a ƙasar kama daga ta Obasanjo zuwa Jonathan da Buhari dukkansu sun yi ƙarin albashi mafi ƙaranci, amma ya zuwa yanzu ma'aikaci na cikin wani hali.

Sai dai ya bayar da shawarar cewa ma'aikata suna da rawar da za su taka wajen riƙe ayyukansu cikin gaskiya tare da tafiyar da ayyukansu yadda suka kamata.

Haka kuma akwai buƙatar ƙungiyoyin ƙwadago su zauna da gwamnati domin neman mafita ba wai batun samar da albashi mafi ƙaranci ba. Masanin tattalin arzikin ya ce kamata ya yi bangaorin biyu su duba matakai da za su taimaka wajen magance tashin farashin kayayyaki ta yadda ma'aikaci zai iya tafiyar da rayuwarsa cikin sauƙi.

Abubuwa uku da ya ce suke lashe kaso mafi tsaoka na albashi su ne: ilimi da lafiya da kuma abinci, waɗanda ya ke ganin idan gwamnati ta samar da su cikin sauƙi rayuwar ma'aikaci za ta inganta.

Ya ce idan gwamnati ta inganta makarantu tare da bayar da ilimi kyauta da inganta kiwon lafiya ta hanyar sanya kowa cikin shirin inshora ta yadda duk ɗan ƙasa ba shi da matsala a wannan fannin za su taimaka.

"Wadatar abinci a cikin ƙasa ita za ta karya farashin abinci a cikin ƙasa. Najeriya muna da ƙasar noma mai albarka duk da cewa ana ɗora rashin noma a wasu bangare kan matsalar tsaro, amma akwai wuraren da ke da ƙasar noma amma ba a noman." A cewarsa, "idan gwamnati ta ƙara inganta samar da abinci a cikin kasa farashi zai karye. "