Albashi mafi ƙanƙanta: Shin ma’aikatan Najeriya gaba suke yi ko baya?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Hausa
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
A wannan watan ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da naira 70,000 a matsayin albashi mafi kanƙanta ga ma'aikatan Najeriya, bayan shafe watanni ana kai ruwa rana tsakanin ɓangaren gwamnati da na ƙungiyoyin ƙwadago.
A cikin watan Janairun dai gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti mai mambobi 37 da zai sake nazarin albashi mafi ƙanƙanta a ƙasar.
Hakan na zuwa ne bayan da shugaban ya alƙawarta wa ma'aikatan ƙari a albashinsu tun cikin watan Janairu, bayan koken da ƴan ƙwadago suka yi kan tsananin rayuwa.
Wannan dai ya gaza a albashi mafi ƙanƙanta da ƙungiyoyin ƙwadagon suka gabatar na naira 250,000.
Sai dai wannan sabon albashin ya nunka tsohon albashin mafi ƙanƙanta na 30,000, wanda aka kwashe tsawon lokaci ana amfani da shi.
Batun samar da matsaya kan albashi mafi ƙanƙanta a Najeriya ya daɗe yana tayar da ƙura a Najeriya tun bayan zuwan sabuwar gwamnatin Bola Tinubu, wanda ya kama aiki a watan Mayun 2024.
Sai dai masana da dama na ganin cewa ƙarin sabon albashi mafi kanƙantar ba zai yi wani tasiri ba, idan aka yi la'akari da hauhawar farashin kayan masarufi da faduwar darajar kuɗin ƙasar.
A Najeriya gwamnatin ƙasar ta jima tana yi wa ma'aikatan ƙasar ƙarin albashi, lamarin da ya sa wasu ke ɗora ayar tambayar cewa shin ƙarin albashin yana yin wani tasiri ga rayuwar ma'aikatan?
Tarihi ƙarin albashi a Najeriya

Asalin hoton, CBN
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙarin albashin ma'aikata a Najeriya ya samo tarihi ne tun a shekarar 1959, lokacin da ƙasar ke a ƙarkashin ikon turawan mulkin mallaka, kamar yadda Kwamared Ayuba Wabba tsohon shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya.
''A wancan lokacin, gwamnan yankin kudu maso yammacin ƙasar, Obafemi Awolowo ne ya bayar da shawarar daidaita albashin ma'aikatan ƙasar na kowane yanki'', in ji shi.
Baya ga wannan ƙarin albashin da aka yi wa ma'aikatan Najeriya da za a iya tunawa shi ne na zamanin mulkin Janar Yakubu Gawon a shekarar 1979, kamar yadda Wabba ya bayyana.
''A lokacin tattalin arziƙin Najeriya ne ya bunƙasa shi ya sa gwmnati ta ce ya kamata ta yi wa ma'aikata ƙarin albashin domin su ɗanɗani bunƙasar tattalin arzikin ƙasar''.
Ya ƙara da cewa ''an yi wa ƙarin laƙabi da 'Udoji', sannan kuma sai da aka haɗa wa kowane ma'aikaci albashinsa na kusan shekara guda, sannan aka ci gaba da biyan su ƙarin da aka yi'', in ji Kwamared Wabba.
Ƙarin albashin da aka yi ƙarƙashin tsarin dimokuraɗiyya na farko - wanda aka yi a matsayin doka shi ne wanda aka yi a 1981 zamanin mulkin shugaba Shehu Shagari.
''Wannan dokar ita ce har yanzu ake yi wa gyaran fuska a duk lokacin da ka zo batun albashi mafi ƙanƙanta'', kamar yadda Kwamared Wabba ya yi bayani.
''A lokacin ƙarin da ka yi shi ne aka mayar da albashi mafi ƙanƙanta zuwa naira 120, (kimanin dala 220)'', in ji Wabba.
Kwamared Wabba ya ce daga nan sojoji suka riƙa ƙari har zuwa lokacin mulkin Abdussalami Abubakar a 1999, inda ya mayar da mafi ƙanƙantar albashi zuwa naira 3,500(kimanin dala 166 a lokacin).
Sai kuma a shekarar 2000 lokacin da Olusegun Obasanjo ya zo da zaɓi biyu kan albashi mafi ƙanƙanta, wato naira 5,500 da 7,500, (kimanin dala 63 da 87), kamar yadda Wabba ya bayyana.
A shekarar 2011 ne tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan ya mayar da albashi mafi ƙanƙanta zuwa naira 18,000, kimanin dalar Amurka 116 a wancan lokacin).
Sai kuma a shekarar 2016 lokacin da Muhammadu Buhari ya mayar da albashi mafi ƙanƙanta zuwa 30,000(Kimanin dala 90).
Sai yanzu kuma da Bola Tinubu ya mayar da shi naira 70,000 ( kimamin dala 42).

Ci gaba ko akasin haka?
Tsowan wannan lokaci da ma'aikatan Najeriya suka kwashe ana yi musu ƙarin albashi, shin ci gaba ma'aikatan suka samu ko akasin haka?
Wannan ita ce tambayar da mutane da dama ke yi a duk lokacin da aka yi ƙarin albashi.
Kwamared Ayyuba Wabba ya ce za a iya cewa ci gaba aka samu, sai dai ya ce ba irin ci gaban da ake tunani ba, saboda a cewarsa hauhawar farashin kaya da faɗuwar darajar kuɗin ƙasar su ne ke kawo wa ma'aikata tarnaƙi wajen amfana da ƙarin albashi a duk lokacin da aka yi shi.
''Idan ka duba a shekarar 1981 lokacin da albashi ya koma naira 120, a lokacin ana canja kowace dala a kan kimanin naira 0.61, to ka ga ko naira ɗaya darajar dala ba ta kai ba''.

Asalin hoton, Getty Images
'Kuɗin sayen mota a 1979 ba zai sayi burodi ba a 2024'
''Don haka abubuwa suna cikin sauki komai za ka same shi a arha da rahusa, a lokacin idan ma'aikaci ya nemi bashin banki na naira 1,500, to zai iya sayen mota ƙirar Beetle (wadda ita ce motar yayi a wancan lokaci) har ma ya yi ragi, saboda a lokacin motar ba ta wuce naira 1,250 ba, amma ka ga wannan kuɗin a yanzu ko burodi mai kyau ba zai saya maka ba'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa ''amma a yanzu wannan naira 70,000 ɗin da aka amince da shi kuɗin buhun shinkafa ɗaya ne, to ka ga ai ba za mu ce ci gaba ma'aikacin Najeriya ya samu ba, la'akari da faduwar darajar kuɗin ƙasar.
Amfanin ƙarin albashi
Ƙarin albashi na da matuƙar alfanu domin kuwa sai ma'aikata na da kuɗi sannan ake samun walwalar kudi tsakanin al'ummar kamar yadda kwamared Wabba ya yi ƙarin bayani.
''Ko su ƴan kasuwa za su gaya maka idan ma'aikata ba su cikin kuɗi, ko ba sa samun ciniki a kasuwancinsu, saboda babu kuɗi a hannun ma'aikata.''
Kwamared ɗin ya kuma ƙara da cewa albashi na daga cikin abubuwan da ke kawo zaman lafiya tsakanin al'umma a duniya.
''Wannan shi ne dalilin da ya sa lokacin da duniya ke cikin matsin tattalin arziki tsohon shugaban Amurka Barrack Obama ya ƙara wa ma'aikata albashi, domin idan ya kara albashi, kamfanonin sarrafa abinci za su yi aiki, kuɗi za su wadata cikin al'umma, tattalin arziki kuma zai bunƙasa'', in ji shi.
Ya ce idan ma'aikata ba sa samun wadataccen albashi, to kudi ba za su zagaya cikin al'umma ba, don haka tattalin arziƙi zai tsaya cak, kamar yadda tsohon shugaban ƙungiyar ƙwadagon ya bayyana.
Gwamnoni da kamfanoni masu zaman kansu

Asalin hoton, .
Wani abu da ke ta muhawara a kansa shi ne ko gwamnonin jihohi da kamfanoni masu zaman kansu za su iya biyan sabon mafi ƙanƙantar albashi.
To amma tsohon shugaban ƙwadagon ya ce yana da yaƙinin cewa gwamnonin jihohin za su iya, duba da irin kason da suke samu daga asusun tarayya.
''Idan muka duba lokacin da Obasanjo ya mince da sabon mafi ƙanƙatar albashi a 2000 na 5,500 ya ce gwamnonin za su iya biyan fiye da hakan ma idan sun ga dama, kuma ba na mantawa a lokacin gwamnan Zamfara na biyan naira 6,500 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta,''
''Kuma idan ka duba jihar Zamfara ba ta cikin jihohin ƙasar da ke samun kaso mafi tsoka daga asusun tarayya, amma duk da haka gwamnatin jihar a lokacin ta biya sama da albashi mafi ƙanƙanta'', in ji Kwamared Wabba.










