Da wahala Kwankwaso ya goyi bayan Tinubu a 2027 - Buba Galadima

Tinubu da Kwankwaso

Asalin hoton, Kwankwaso/Twitter

Lokacin karatu: Minti 3

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Buba Galadima ya ce zai yi wahalar gaske Kwankwaso ya haɗa hannu da jam'iyyar APC domin samun nasarar Bola Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027.

Buba Galadima ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da tashar Channels a shirinta na Politics Today wanda aka yi a ranar Litinin, inda ya ce gwamnatin Tinubu tana takalar Kwankwaso, musamman wajen goyon bayan Sarki Aminu Ado Bayero, duk da gwamnatin jihar ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta cire shi.

Da aka tambaye shi cewa akwai yiwuwar NNPP ta haɗu da APC, sai ya ce, "ni yanzu ma nake jin wannan maganar. Kwankwaso ne ɗan siyasar mai ƙarfin tsaya da ƙafarsa saboda ya ja daga a APC a Kano kuma ya doke ta," in ji shi, inda ya ƙara da cewa shi dai Kwankwaso bai faɗa masa cewa zai mara wa Tinubu baya ba a zaɓen 2027.

Fitaccen ɗansiyasar, ya ce zai so a ce dukkan ƴansiyasar Najeriya za su zama kamar Kwankwaso.

Da aka ce masa wataƙila ana maganar haɗewar Kwankwaso da Tinubu amma bai sani ba, sai ya ce, "Na san da a ce wani ya same shi, sun yi maganar, da dole zan sani. Ba dole ba ne in zama wanda ya fi zama na kusa da shi, amma a siyasa, muna magana da shi sosai, amma kuma bai faɗa min wannan maganar ba."

"Ta yaya ma Kwankwaso zai zama abokin APC bayan duk abin da suke mana a Kano. Naɗa sarakuna biyu a gari ɗaya? Akwai sarkin tarayya da na jiha. Wane ne ke da alhakin naɗa sarki da biyansa albashi?"

Ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya na da sarkinta, sannan ya ce akwai "aƙalla motocin ƴansanda 40 da ke tsare sarkin".

Da aka tuna masa cewa gwamnatin tarayya ba ta naɗa sarki ba, sai ya ce babu dalilin da kotun tarayya za ta yanke hukunci game da batun sarauta, sannan ya ce tun a farko, Tinubun ne ya dage sai Sanusi ya zama sarki.

Ya ce gwamnatin tarayya ta ajiye Sarki Aminu ne domin tana tunanin zai taimaka mata a zaɓen 2027, inda ya ce babu wani sarki a Kano da zai iya taka rawar gani wajen sauya ƙuri'a.

Ya ce Kanawa sun aminta da Kwankwaso ne domin sun gani a ƙasa, wanda a cewarsa hakan ya sa suke binsa a siyasance.

A game da makomarsu a siyasa, musamman ta fuskar zaɓen 2027, Buba Galadima ya ce ba su yanke shawara ba, "amma ina tabbatar maka duk inda ka ganmu, to nan ne za a kafa gwamnati."

Wane muhimmanci Kwankwaso yake da shi a siyasa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tsohon gwamnan jihar Kanon, Rabi'u Musa Kwankwaso na ɗaya daga cikin ƴan siyasa a arewacin Najeriya da suka daɗe suna jan zarensu kuma suka shiga cikin zuciyar matasa.

Masana na cewa tun bayan Malam Aminu Kano ba a sake samun wani ɗansiyasa ba da ya fito da wani tsari na siyasa da ya sa wa suna wanda kuma yake da mabiya na ga-ni-kashe-ni, sai tsohon gwamnan na Kano wanda ya samar da aƙidar siyasa mai suna Kwankwasiyya da mabiyanta ke saka jar hula.

Sannan kuma Rabi'u Musa Kwankwaso shi ne gwamnan da bayan ya faɗi a ƙoƙarin neman wa'adi na biyu ya sake komawa kujerar bayan shekaru huɗu, inda ya kayar da ɗantakarar gwamna mai barin gado na lokacin.

Har ila yau, Kwankwaso ya tsayar gwamnan Kano mai-ci, Abba Kabir Yusuf inda ya kayar da ɗantakarar gwamna mai barin-gado, Nasiru Yusuf Gawuna.

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar NNPP a 2023, inda ya samu kuri'u fiye da 900,000 a jihar Kano, wadda ta fi yawan ƙuri'ar da kowanne daga sauran ƴan takarar jam'iyyun suka samu a jiha ɗaya tilo, ciki kuwa har da jam'iyya mai mulki ta APC.