Hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta sake yi kan rikicin masarautar Kano

Asalin hoton, Mai Katanga/Facebook
A ranar Juma'ar nan ne kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta jingine hukuncin da ta yi a ranar 10 ga watan Janairun 2025 kan rikicin masarautar Kano, har zuwa lokacin da kotun ƙoli za ta yanke hukuncin ƙarshe dangane da rikicin.
Wannan dai ya biyo bayan ɗaukaka ƙara da Alhaji Aminu Babba Ɗan'agundi ya yi a kotun kan neman a dakatar da hukuncin kotun na watan Janairu, wanda ya shafi hukunce-hukunce biyu da aka yanke a kotuna biyu da ke birnin Kano, na babbar kotun tarayya da kuma babbar kotun jihar.
Rikicin ya shafi nadin Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16 da kuma soke masarautun Kano biyar da dokar masarautun Kano ta 2019 ta naɗa.
'Rikicin masarautu ba hurumin kotun tarayya ba ne'
A hukunci na farko, kotun ta yanke cewa babbar kotun gwamnatin tarayya ba ta da hurumin tsoma baki a rikicin masarauta.
Kotun ta ce babbar kotun Kano ce kawai take da damar yanke hukunci kan duk wani ruɗani da ya shafi sarauta a jihar.
Sai dai an samu saɓani tsakanin alƙalai uku da suka yanke hukunci kan lamarin.
Mai shari'a Gabriel Kolawale, wanda shi ne ya karanto hukuncin, ya umarci a mayar da ƙarar zuwa kotun da ta dace, wato babbar kotun Kano domin ci gaba da sauraro.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai sauran alƙalan biyu sun ƙi amincewa da batun mayar da ƙarar zuwa babbar kotun jihar Kano, inda suka bayar da umarnin watsi da batun shari'ar baki ɗayanta.
Watsi da hukuncin kotun Kano
A hukunci na biyu kuma, kotun ɗaukaka ƙarar ta yi watsi da matakin Babbar kotun Kano na haramta wa Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu na jihar bayyana kansu a matsayin sarakuna.
Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Mohammed Mustapha ta bayyana cewa akwai kuskure a hukuncin Babbar kotun Kano na ranar 15 ga watan Yulin 2024, kuma ya saɓa wa ƙa'idar jin ta-bakin kowane ɓangare.
Kotun ta kuma umarci alƙalin kotun ta Kano ya miƙa shari'ar ga wani alƙalin na daban domin a sake sauraron ta daga farko.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce hukuncin kotun ta Kano na cike da "rashin adalci da saɓa ƙa'idar bai wa kowane ɓangare dama".
Kotun ta ce Babbar kotun Kano ta ci gaba da sauraron ƙarar ne ba tare sanar da Aminu Ado Bayero game da ƙarar ba, kuma ba a ba shi damar gabatar da nasa hujjojin ba.











