Dalilin da ya sa miliyoyin yara za su fuskanci matsalar gani zuwa 2050

Yarinya ta rufe idonta

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Philippa Roxby
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health reporter
  • Lokacin karatu: Minti 4

Lafiyar idon yara na ci gaba da taɓarɓarewa inda ɗaya cikin uku ke fama da matsalar rashin gani daga nesa, kamar yadda wani bincike ya bayyana.

Masu bincike sun ce kullen korona ya yi mummunan tasiri ga lafiyar ido inda suke shafe lokaci suna kallon kwamfuta amma lokaci kaɗan suke yi a waje.

Matsalar da ake kira myopia a turance, babbar damuwa ce ta lafiya a duniya wadda aka ce za ta shafi miliyoyin yara zuwa 2050, kamar yadda binciken ya yi gargaɗi.

Yankin Asiya ne matsalar ta fi ƙamari - Japan ke da kashi 85 na yara, sai Koriya ta Kudu da ke da kashi 73 yayin da kuma China da Rasha ke da kashi 40.

Paraguay da Uganda da ke da kashi ɗaya su ne ƙasashen da matsalar ta fi sauƙi, yayin da Birtaniya da Ireland da Amurka ke da kashi 15.

Binciken wanda aka wallafa a mujallar lafiyar ido ta Birtaniya, ya yi nazari ne kan yara sama da miliyan biyar da matasa daga ƙasashe 50 a nahiyoyin duniya shiga.

Adadin girman matsalar ya lunka har sau uku tsakanin 1990 zuwa 2023 - ƙarin kashi 36.

An samu ƙarin ne musamman bayan annonar korona, kamar yadda masu binciken suka bayyana.

Matsalar idon yawanci takan fara ne daga matakin firamare kuma za ta iya girma har sai idon ya gama girma, kusan idan mutum ya kai shekara 20.

Akwai abubuwan da za su iya sa haddasa matsalar - rayuwa a gabashin Asiya na ɗaya daga cikinsu.

Sannan akwai gado - yara kan iya gadar matsalar daga iyayensu - amma akwai wasu dalilan, kamar lokacin yarinta (shekara biyu) lokacin da yara ke fara kartun boko kamar a ƙasashen Singapore da Hong Kong.

Wannan na nufin suna shafe lokaci a littafansu da kuma a hasken kwamfuta a idonsa a yarintarsu, wanda ke illa ga ido da zai iya haifar da myopia, kamar yadda binciken ya nuna.

A Afrika, inda ake fara karatun boko a shekara shida zuwa takwas, za a fi kaucewa matsalar kusan sau shida idan aka kwatanta da yankin Asiya.

Yarinya ta sanya gilashi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yara mata sun fi hatsarin kamuwa da matsalar lafiyar idon fiye da yara maza, a cewar binciken.

Lokacin kullen korona a duniya, inda miliyoyin mutane suka fi zama a gida a lokaci mai tsawo, hakan ya shafi lafiyar idon yara.

"Wasu hujjojin da suka bayyana sun nuna alaƙar annobar da kuma matsalar lafiyar ido ga yara, kamar yadda binciken ya bayyana.

Zuwa 2050, matsalar za ta iya shafar sama da rabin yara a duniya, kamar yadda binciken ya yi hasashe.

Yara mata da ƴan mata ne suka fi fuskantar barazanar fiye da yara maza da matasa, saboda sun fi yawan zama gida, a cewar binciken.

Girman mace da balagarta, na farawa da wuri wanda hakan ke nufin sun fi fuskantar matsalar lafiyar idon.

Kodayake a yankin Asiya ne aka fi yin hasashen matsalar za ta yi ƙamari idan aka kwatanta da sauran yankunan duniya zuwa 2050, inda kashi 69 za su samu matsalar, a ƙasashe masu tasowa kuma kashi 40 kamar yadda binciken ya bayyana.

Ta yaya za ka kare lafiyar idon yaro?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ana son yaro ya kasance a waje aƙalla tsawon sa'a biyu a kowace rana, musamman tsakanin shekara bakwai zuwa tara, domin rage hatsarin samun matsalar ido, a cewar masanin lafiyar ido a Birtaniya.

Babu tabbaci ko kasancewa a hasken rana, ko wasanni a waje ko yawan kasancewar yara a wani abu zai iya haifar da wani sauyi

"Akwai wani abu game da kasancewa a waje wanda yana da amfani ga yara, in ji Daniel Hardiman-McCartney, wani masanin lafiyar ido a Birtaniya.

Ya kuma bayar da shawara ga iyaye su dinga kai ƴaƴansa gwajin ido idan suka kai shekara 10 ko da kuwa an yi masu gwaji lokacin da suna ƙanana.

Sannan iyaye su sani cewa matsalar myopia ana gadonta - idan har ba ka iya ganin nesa akwai yiyuwar ƴaƴanka za su kamu kusan sau uku fiye da wasu.

Ba a iya magance matsalar amma ina iya gyarawa ta hanyar amfani da gilashi.

Gilashi kan hana cigaban matsalar ga yara amma yana da tsada.

Damuwar ita ce, girman matsalar myopia kan haifar da matsalolin ido a shekarun tsufa.

Alamomin matsalar

  • Gaza yin karatun daga nesa, kamar karanta abin da aka rubuta a allo a makaranta
  • Zama kusa da talabijin ko kwamfuta ko riƙe waya kusa da fuska
  • Ciwon kai
  • Susar ido akai-akai