Yadda asibiti ya haramta wa ma'aikatansa yin mining a Gombe

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Gombe wato Federal Teaching Hospital ya fitar da wata sanarwar hana dukkannin wani abu mai kama da mining da zai ɗauke hankalin ma'aikaci daga kula da mara lafiya.

Sanarwar dai wadda mataimakin darektan gudanarwa na asibitin ya sanya wa hannu ta ce:

"An umarce ni da na gargaɗi ma'aikata su guji yin mining ko kuma duk wata hanyar neman kuɗin kirifto a lokacin da suke bakin aiki..."

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa " za a ɗauki tsattsauran mataki ga duk ma'aikacin da aka samu yana karya wannan umarni."

..

Asalin hoton, Getty Images

Me ya janyo ɗaukar matakin?

Sanarwar ta bayyana cewa "an ɗauki matakin ne sakamakon irin ƙorafe-ƙorafen da hukumar asibitin ke samu daga marasa lafiya da danginsu da ke nuna irin yadda mining ɗin da ma'aikatan ke yi yake ɗauke hankalinsu daga marasa lafiya."

Wani ma'aikacin asibitin da BBC ta tattauna da shi dangane da hanin, ya shaida cewa al'amarin kam ya yi muni yadda ma'aikata ke yin mining a bakin aikinsu.

"Gaskiya dukkan ma'aikatan na yin mining babu babba babu yaro sannan babu wani ɓangare da za ka cire. Likitoci da ma'aikatan jinya da sauransu kowa na ciki." In ji ma'aikacin.

'Lokuta biyu da mining ya haddasa rikici a asibitinmu'

Ma'aikacin na asibitin koyarwar na gwamnatin tarayya da ke Gombe ya shaida wa BBC cewa akwai wasu lokuta guda biyu da suka ba shi mamaki inda ma'aikatan asibitin suke mining har marasa lafiya suka fusata.

"Akwai wata rana da mara lafiya ya zo wurin wata a ɗakin bayar da magani zai karɓi magani to amma ita mai bada maganin tana mining abin da ya sa marar lafiyar na yi mata magana ba ta ji ba. Wannan ya sa an samu rashin jituwa. Kuma na san za su kai ƙorafi."

"Na biyu kuma shi ne wani lokaci da ruwan da ake ƙara wa wani marar lafiya ya ƙare amma jami'ar jinyar ba ta kula ba saboda tana yin mining. Shi ma wannan abin ya janyo matsala tsakanin iyalan marar lafiyar da jami'ar lafiyar.

Me ma'aikatan ke faɗi?

Ra'ayoyi sun banbanta a tsakanin ma'aikatan da muka zanta da su inda wasu suka amince da hukuncin cewa ya kamata yayin da wasu kuma suke ganin kamar ya yi tsauri.

"Har ga Allah ni ina yin mining amma wannan hukuncin ya yi min daidai domin abin da shafar marasa lafiya yadda ba ka tsammanin. Tuntuni ma ya kamata a ɗauki wannan matakin ba yanzu ba.

Ni yanzu zan ci gaba da yin mining idan na tashi daga aiki na je gida sai na yi ko kuma a lokacin da ba na aiki kamar idan na fita cin abinci.: In ji wani ma'aikaci.

To sai dai wani ma'aikacin na daban ya shaida wa BBC cewa shi kam bai ji ɗaɗin hana su ba.

"Saboda idan ka dubi tsawon lokacin da muke kashewa a asibiti ya fi wanda muke yi a gida. Kuma ai sai lokacin da babu mara lafiya ne muke danna waya domin yin mining."