Yadda za ku gane idan ƙananan 'ya'yanku na da matsalar gani

Asalin hoton, Getty Images
Shin kun san cewa, ana samun ƙarin yara masu yawa da ke fama da matsalar rashin iya ganin abubuwa tangararau daga nesa? A cewar Vismita Gupta-Smith, wata jami'ar sadarwa ta Hukumar Lafiya ta Duniya.
Gani, in ji Hukumar Lafiya, mafi ƙarfin tasiri a kafofin ɗan'adam na fahimtar rayuwa da su, na da gagarumar gudunmawa a dukkan wani mataki da zango na rayuwarmu.
Duk da yake, ba mu cika damuwa da baiwar gani da Allah ya hore mana ba, amma idan babu shi, mukan yi fama wajen koyo da tafiya da karatu da kuma shiga makaranta, har ma da zuwa aiki.
To ta yaya za ku gane idan ganin idon 'ya'yanku na cikin hatsari, kuma me za ku iya yi don kare ganinsu?
Da kuma waɗanne ne alamomin farko-farko cewa 'ya'yanku na da matsalar gani?
Domin gano muku amsa, mun bibiyi wani shirin kimiyya na mako-mako daga Hukumar Lafiya ta Duniya:
Alamomin farko-farko na matsalar gani
Dr. Stuart Keel, wani ƙwararre a shirin kare lafiyar ido da gani na Hukumar Lafiya ta Duniya, ya ce ba shakka mai yiwuwa ne akwai alamomin farko-farko na rashin gani ko kuma nakasar gani a wajen ƙananan yara.
Alamomin kuma in ji shi, suna iya bayyana cikin sigar yawan mutsuttsuka ido da micincina ido wajen ganin wani abu da kanne ido kafin a iya ganin wani abu.
Ƙwararren kuma ya ce mai yiwuwa ne kuma 'ya'yanku na riƙe abin karatunsu kusa da idanuwansu saosai, ko kuma sai sun matsa kusa da talbijin don ganin wani abu tangararau.
Mai yiwuwa ne kuma matsalar na iya faruwa cikin sigar ƙarancin ƙwazo a makaranta.
Dr Stuart Keel ya ce idan an lura da irin wannan matsala, to yana ba da shawarar a kai yaro asibitin ido, don yi masa cikakken gwaji, ta yadda za a gano abin da ke faruwa a kan lokaci.

Asalin hoton, Getty images
Me ke janyo ƙaruwar matsalar gani a wajen yara?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da farko, zan ce idan kuna da matsalar ganin nesa, to tabbas ba ku kaɗai ba ne, in ji Dr Stuart Keel.
Ya ce kimanin kashi 20% na al'umma ko kuma a ce kusan mutum biliyan biyu a faɗin duniya, ba sa iya ganin abin da ke nesa sosai.
Daga cikin abubuwan da ke haddasa matsalar, wanda kuma babu abin da za mu iya da shi, akwai batun ƙwayoyin halittun gado.
Idan mahaifi ko mahaifiya ko kuma dukkansu, na da matsalar ganin nesa, mai yiwuwa ne 'ya'yansu ma za su samu wannan matsala.
Sai dai, sauran rukuni na hatsarin samun matsalar rashin iya ganin nesa, na da ƙarin ban sha'awa a cewar Dr Stuart Keel. Kuma yana da muhimmanci mu san su, saboda suna da alaƙa da salon rayuwa.
Bincike a yanzu na matuƙar nuna cewa harkokin aiki da ke buƙatar ƙura ido a kurkusa, kamar kallon na'urori na tsawon lokaci da kallon abin karatu tsawon lokaci da kuma raguwar lokacin da akan shafe a waje dukkansu haɗurra ne da ke haifarwa da kuma girmama matsalar rashin ganin nesa.
Me iyaye za su yi, su kare 'ya'yansu?
A wannan zamani, iyaye kan bai wa 'ya'yansu na'urorin dijital da wurwuri a rayuwarsu. An tambayi Dr Stuart Keel shin ko hakan na da alaƙa da ƙaruwar matsalar ganin abin da ke nesa dishi-dishi?
Ƙwararren na Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce e, hakan na ba da gudunmawa.
Sai dai ya ce muhimmin abin da iyaye za su iya yi, shi ne su kai 'ya'yansu, a yi musu cikakken gwajin ido, ko da kuwa tuni an yi masa gilashi.
A cewarsa, yanayin larurorin ido kamar rashin ganin nesa ko rashin ganin kusa garau a shekarun yarinta, na nufin gwajin ƙarfin ido yana canzawa a tsawon lokaci, don haka akwai buƙatar sabunta gilashi a duk 'yan shekaru.
Abu na biyu kuma, shi ne akwai 'yan wasu abubuwa da iyaye ko magabata za su iya yi don kare ganin 'ya'yansu daga samun matsalar rashin ganin nesa.
Dr Stuart Keel ya ce bincike ya nuna cewa shafe tsawon minti 90 a waje cikin wunin rana, wani matakin kariya ne da ke hana yara kamuwa da matsalar rashin ganin nesa.
Don haka ƙarfafa gwiwar yara su fita waje su yi wasa, wani muhimmin abu ne.
Ya ce yanzu haka akwai gagarumar shaida da ke nuna cewa wasa a wajen gida, yana kare idon yara daga larurar rashin ganin nesa.
Sai dai haƙiƙanin dalilin ne babu tabbaci a kai. Amma ɗaya daga cikin dalilan shi ne yawan hasken Allah da ke shiga idanu, yana tabbatar da cewa idanun yara sun bunƙasa cikin madaidaicin tsari.
Abu na gaba kuma shi ne rage lokacin da yara ke kwashewa suna ƙura ido ga ayyukan da ke buƙatar matsawa kurkusa, kamar kallon kwamfuta ko tabulet.
Dr. Stuart ya ce abu na ƙarshe kuma shi ne idan yaranku na tabaran ƙara gani, a riƙa ƙarfafa musu gwiwa suna sanya shi sosai da sosai.
Akwai wani kuskuren tunani a wajen mutane masu yawa, in ji shi, na cewa yawan sa tabaran gani na iya ƙara dakushe ganin yara.
Dr Stuart ya ce wannan ba gaskiya ba ne. Ya ƙara da cewa sanya tabaran gani na tabbatar da cewa yaranku ba sai sun mitsi-mitsi da idanu kafin su iya ganin wani abu sosai ba.











