Masana kimiyya sun ƙirƙiri siffar ɗan tayin mutum babu maniyya ba ƙwai

Embryo model

Asalin hoton, WEIZMANN INSTITUTE OF SCIENCE

Bayanan hoto, Ɗan tayin misalin daga ƙwayar halittar gangar jikin bishiya na nuna shuɗayen ƙwayoyin halitta (ɗan tayi), ƙwayoyin halitta ruwan ɗorawa (rigar ƙwanduwa) sai ƙwayoyin halitta ruwan hoda (mabiyiya).
    • Marubuci, James Gallagher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin harkokin lafiya da kimiyya

Masu ilmin kimiyya sun ƙago wata halitta da ta yi kusa da kamanni irin na ɗan tayin mutum a farko-farkon kasancewarsa, ba tare da sun yi amfani da maniyyi ko ƙwan mace ko kuma mahaifa ba.

Jami'an kimiyya a Cibiyar Weizmann sun ce sun ƙirƙiro "siffar ɗan tayin" nasu, ne daga ƙwayoyin halittu na gangar jikin bishiya, kuma ya yi kama da sigar ɗan tayi na haƙiƙa mai kwana 14 a ciki.

Ta ma fitar da bayani a kan sinadaran halitta (hormones) da ke mayar da gwajin juna biyu ya zama tabbatacce a ɗakin gwaje-gwaje.

Burin masu ƙirƙirar siffa ko misalin ɗan tayin shi ne samar da hanya wadda cikin sanin ya kamata za a yi amfani da ita wajen fahimtar lokutan na farkon halittar rayuwarmu.

Makonnin farko bayan maniyyi ya ƙyanƙyashe ƙwai, wani ƙanƙanin lokaci ne da ake samun gagarumin canji - daga tarin ƙwayoyin halitta marasa taƙamaiman fasali zuwa wani abu wanda daga bisani ake iya ganewa a hoton jariri a cikin ciki.

Wannan muhimmin lokaci kan zama wani gagarumin sanadin ɓarin ciki da samun tawaya tun a cikin ciki amma an yi masa raunin fahimta.

"Wani al'amari ne mai sarƙaƙiya da ba a san kansa ba, kuma ba zance ne da za a ce ya zama kamar cin ƙwan makauniya ba - ilminmu ɗan taƙaice ne," Farfesa Jacob Hanna, daga Cibiyar Nazarin Kimiyya ta Weizmann, ya faɗa mini.

Matakin farawa

Bincike kan halittar ɗan tayi a shari'ance da bisa doron sanin ya kamata da kuma ci gaban kimiyya cike yake da yiwuwar haifar da abin da ba a fata. Sai dai yanzu cikin hanzari ana samun bunƙasar fannin kwaikwayon halittar ɗan tayi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jami'an kimiyyar Isra'ila sun bayyana wannan bincike, da aka wallafa a mujallar Nature, a matsayin "cikakken" misalin ɗan tayi na farko da ake kwaikwayar muhimman siffofin da ke bayyana a farkon halittar ɗan tayi.

"Wannan haƙiƙa wani misali ne na ɗan tayin mutum da ya kai tsawon kwana 14 a ciki" cewar Farfesa Hanna, abin da "ba a taɓa yi ba a baya".

Maimakon maniyyi da ƙwai, abubuwan da ake amfani da su, akwai tsagwaron ƙwayoyin halitta daga gangar jikin bishiya waɗanda ake sake wa tsari ta yadda za su kasance masu yiwuwar zama duk wani nau'in tsoka a cikin jiki.

Daga nan, ana amfani da sinadarai a shawo kan waɗannan murɗa-murɗan ƙwayoyin halittar su koma nau'o'i guda huɗu na ƙwayar halittar da ake samu a matakan farko-farkon na ɗan tayin mutum:

  • Ƙwayoyin halitta na epiblast, da ke komawa cikakken ɗan tayi
  • Ƙwayoyin halitta na trophoblast, da ke zama mabiyiya
  • Ƙwayoyin halitta na hypoblast, da ke koma wa rigar tallafa wa ƙwanduwa.
  • Ƙwayoyin halitta na extraembryonic mesoderm suna da muhimmanci wajen kare ɗan tayi da kuma sadarwa.

Jimillar waɗannan ƙwayoyin halitta 120 ne ake cakuɗawa gwarwadon wani daidan adadi – sannan sai, masana kimiyyar su koma gefe su zuba ido.

Kimanin kashi 1% na ƙwayoyin halittun da aka cakuɗa ba zato ba tsammani sai su fara harhaɗa kansu zuwa wata siga da ta yi kama, amma ba iri ɗaya da ɗan tayin mutum.

"Ɗumbin godiya ga waɗannan ƙwayoyin halitta – abin da kawai za ka yi shi ne ka cakuɗa adadi daidai sannan a samu muhallin da ya dace, shi kenan sai komai ya fara kankama," in ji Farfesa Hanna. "Wannan lamari ne mai ban ta’ajibi."

Ana barin misalan ‘yan tayin su girma, su bunƙasa har sai sun kai munzalin da za a iya kwatanta su da ɗan tayin mutum da ya kai kwana 14 bayan. A ƙasashe da dama, wannan mizani ne halastacce ga binciken halittar ɗan tayi.

Duk da yake cikin tsakiyar dare muka yi magana da shi ta bidiyon waya, ina iya jin shauƙi a lokacin da Farfesa Hanna yake ba ni bayani dalla-dalla ta hanyar fayyace zanen "ɗanɗasheshiyar fasaha mai kyau" ta siffar ɗan tayin.

Ina iya ganin ƙwayoyin halittar, da galibi su ne suka saba zama mabiyiyar, da ke lulluɓe ɗan tayi. Kuma tana ƙunshe da kwararo – da ke cika da jinin mahaifiya don kai abincin da jariri ke buƙata.

Ga kuma rigar ƙwanduwa, wadda ke aiki irin na hanta da ƙoda, ga shimfiɗar da ta haɗa ƙwayoyin halittun da ke koma wa ɗan tayi da na rigar ƙwanduwa - ɗaya daga cikin muhimman alamomi na wannan matakin bunƙasar ɗan tayi.

Scientists

Asalin hoton, getty images

'Abu ne mai azanci'

Fata dai, shi ne misalan ɗan tayin za su iya taimaka wa masu ilmin kimiyya fayyace yadda mabambantan nau’o’in ƙwayar halitta ke bayyana, da shaida matakan farko-farko na ginuwar gaboɓin gangar jiki ko kuma fahimtar cutukan da ake gado.

Tuni dai, wannan nazari ya nuna yadda sauran sassan ɗan tayi, za su ƙi tsirowa har sai ƙwayoyin halittun mabiyiya na farko-farko sun bayyana sun zagaye ta.

Akwai ma batun inganta yawan nasarorin da ake samu wajen ƙyanƙyasar ɗan tayi a kwalba ta hanyar taimakawa don fahimtar dalilan da ke sa ‘yan tayi su gaza kai labari ko kuma a yi amfani da misalan ‘yan tayin wajen gwada ko magunguna suna da aminci ga mai goyon ciki.

Farfesa Robin Lovell Badge, wanda ya gudanar da bincike-bincike a kan girman ɗan tayi a Cibiyar Francis Crick, ya faɗa min cewa misalan ‘yan tayin "a ido suna da kyawun gani" kuma "da gani suna cikin yanayin ƙoshin lafiya".

"Ina jin abu ya yi kyawu, ina jin an yi aikin da ya dace sosai, duk azancin abin yana fitowa kuma gaskiya an yi matuƙar burge ni," in ji sh.

Sai dai akwai buƙatar inganta matakai game da gazawa har kashi 99% da ake samu yanzu, a cewarsa. Abu ne mai wahala a fahimci abin da ke faruwa ba daidai ba har ake samun ɓari ko rashin haihuwa idan ɗan tayin misalin ya gaza haɗa kansa a mafi yawan lokaci.

A shari'ance akwai bambanci

Binciken ya kuma taso da batun ko ana iya kwaikwayon ɗan tayin da ya girma ya kai matakin sama da kwana 14.

Wannan ba zai kasance haramtaccen bincike ba, hatta a Birtaniya, saboda misalan ɗan tayi a idon shari’a sun bambanta da ‘yan tayi na aihini.

"Wasu za su yi maraba da wannan – amma wasu ba za su so haka ba," Farfesa Lovell-Badge ya ce.

Waɗannan misalan ‘yan tayi na ƙara kusa da ‘yan tayin haƙiƙa, kuma suna taso da ƙarin tambayoyi game da dacewarsu bisa doron ya kamata.

Ba ‘yan tayin ɗan’adam ba ne na ainihi, su misalan ‘yan tayi ne, ko da yake suna matuƙar kama da na ainihi.

"To ko ya kamata a kafa musu dokoki tamkar yadda ake da su a fannin bincike-binciken ɗan tayin bil’adama ko kuwa kana iya ɗan ƙara sassauci game da yadda ake ta’ammali da su?"

Prof Alfonso Martinez Arias, daga sashen kimiyyar lafiya da gwaje-gwaje a Jami’ar Pompeu Fabra, ya ce "wani ɗan bincike ne mafi muhimmanci".

"Nazarin, a karon farko, ya yi nasarar samar da wani gangariyan gini na cikakkiyar siga [ta ɗan tayin bil’adama] daga ƙwayoyin halittun bishiya” a ɗakin gwaje-gwaje, "abin da ke nufin buɗe ƙofa ga nazarce-nazarcen al’amuran da za su kai ga ɓullo da tsarin gangar jikin ɗan’adam," ya ce.

Masu binciken sun nanata cewa zai kasance rashin dacewa, haramun kuma haƙiƙanin gaskiya ma dai a ce ba zai yiwuwa ba a yi nasarar samun juna biyu ta hanyar amfani da waɗannan misalan ‘yan tayi.