Yadda na zaɓi ceto ran ɗana a maimakon iyayena a ƙarƙashin ɓaraguzai

Tayeb ait Ighenbaz ya tsinci kansa cikin tsaka mai wuya na ya ceci ɗansa mai shekara 11 ko kuma iyayensa da suka maƙale a ƙasan ɓaraguzai bayan girgizar ƙasar da aka samu a Morocco.
Makiyayin, wanda ke zaune a ƙauyen da ke kusa da tsaunin Atlas Mountain ya ce ya shiga tsaka mai wuya a zaɓin da yake da shi a gabansa.
Tayeb na tare da matarsa da 'ya'yansa biyu da kuma mahaifansa a wani gidan ginin dutse lokacin da wannan gagarumar girgizar ƙasa ta afku, mafi girma a ƙasar cikin shekaru 60.
Ya kai wakilin BBC gidan nasa wanda yanzu haka ya zama kufai.
Za ka iya ganin alamun gini, sai ya nuna min wasu ɓaraguzai a gefe ya ce "nan ne inda suke".
"Cikin gaggawa duka abubuwan suka faru. Girgizar na farawa muka ruga zuwa ƙofa. Mahaifina na barci lokacin, sai na yi ihu na cewa mahaifiyata ta taho, sai ta maƙale tana jiran shi".
A gefe ɗaya kuma matarsa ya gani da ƴarsa.
Haka ya ƙara kutsa kai cikin ginin, yana shiga ya tarar da mahaifansa da ɗansa ginin ya rutsa su. Sai ya ga hannun ɗansa a maƙale a jikin ginin.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ganin haka ya sa ya gane akwai buƙatar duk abin da zai yi, ya kamata ya yi shi cikin gaggawa, nan da nan ya yi wajen inda ɗansa yake, Adam, nan da nan ya fara haƙa domin ciro shi daga ramin.
Lokacin da ya juya wajen mahaifansa domin ceto su, sai ya tarar da wani ƙaton dutse ya danne su.
"Dole na zaɓa tsakanin iyayena da ɗana," ya bayyana hakan cikin hawaye.
"Na gaza taimaka wa iyayena saboda katangar ta fado a rabin jikinsu, ina kallon iyayena suka mutu."
Tayen ya nuna wani jirwaye a jikin wandonsa yana cewa wannan jinin iyayena ne.
Duka suturarsa na cikin gidan, tun bayan lokacin da wannan musifa ta faru bai iya sauya kaya ba.
Yanzu haka iyalansa na zaune ne a wani tanti na abokan arziki da ke kusa da gidansu. Tayeb ya ce duka dukiyarsa na gidan, kuma duka awakin da yake kiwo sun mutu.
"Kamar sake haihuwa ta aka yi. Babu iyaye, babu gida, babu abinci, kuma babu kayan sawa," in ji shi. "Yanzu shekarata 50 a duniya, kuma komai zai dawo farko ke nan.
Ba zai iya daina tunanin yadda zai ci gaba ba, amma ko da yaushe yana tuna darasin iyayensa a kansa. "Suna cewa na zama mai haƙuri, na yi aiki tukuru sannan kada na taba yanke ƙauna ko da yaushe."
Yayin da muke magana, ɗan nasa Adam yana ta kaiwa da kawowa, sanye da rigar ƙungiyar kwallon kafa ta Juventus mai ɗauke da sunan Ronaldo.
"Babana ne ya cece ni daga mutuwa," ya faɗi hakan yana ɗaga kai yana kallon mahaifin nasa.
Tafiyar 'yan mintina idan mutum ya yi a gefen titin Amizmiz, zai sake ganin wani mahaifin da ɗansa sun rike hannuwansu.
Abdulmajid ait Jaefer ya ce yana gida da matarsa da yaransa uku lokacin da girgizar ta faru.
Ɗansa Muhammad mai shekara 12 ya yi maza ya fice daga cikin ginin amma sauran ƴan'uwansa na ciki a maƙale.
Abdulmajid ya ce shi ma sai da ƙafarsa ta maƙale cikin ɓaraguzai, amma wani maƙwafcinsa ya zo ya ciro shi daga nan sai da ya shafe sama da awa biyu yana ƙoƙarin ceto matarsa da ƴarsa.
Dukkansu sun mutu lokacin da suka ciro gawarsu.
Washe gari aka zaƙulo gawar ɗaya ƴar tasa daga cikin ɓaraguzai.
Yanzu Abdulmajid mai shekara 47, yana kwana ne a kan titi gefen gidansa.

Yana kallon ɗakin girkinsa da firji da sauran kayan ɗakin a maƙale.
Yace ba zai iya barin unguwar ba saboda ya kare kayayyakinsa kada a sace, da kuma tunawa da matarsa da ta rasu.
Kafin Juma'a, Abdulmajid bai taba tunanin wani abu mai kama da girgizar ƙasa ba. Kuma har yanzu ji nake kamar mafarki."
Muna cikin magana sai wata mota ta tsaya a inda muke suna yi masa gaisuwa.
"Mutum biyar ne a gidana amma yanzu mun koma mu biyu," ya shaida mana cikin damuwa.
"A duniyar nan yanzu abu guda nake tunawa: ɗana."














