Girgizar-ƙasa ta kashe sama da mutum 7,200 a Turkiyya da Syria

Asalin hoton, Getty Images
Masu aikin ceto na ci gaba da fafutikar ganin ko za a samo wasu da ransu a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine bayan mummunar girgizar-ƙasa da ta faru a wasu yankunan ƙasashen Turkiyya da Syria.
Sai dai ruwan sama mai ƙarfi da dusar ƙanƙara wadda ke zuba na kawo cikas ga aikin a kudu maso gabashin Turkiyya.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar yawan waɗanda suka rasa ransu a lamarin zai yi matuƙar ƙaruwa.
Masu aikin ceto dai na ƙara himma, a washe-garin rannar da lamarin ya faru.
Mutane da dama a yankunan da lamarin ya faru na jin tsoron komawa cikin gine-gine da suka rage.
Masu nazari kan motsin ƙasa sun ce girgizar ita ce mafi girma da aka taɓa samu a Turkiyya.
Al’ummar yankin sun ce an kwashe minti biyu ƙasa na jijjiga kafin lamarin ya dakata.
Alkaluma daga Turkiyya da Syria na nuna cewa kawo yanzu mutum fiye da dubu shida ne suka mutu, sannan fiye da dubu 15 suka jikkata sakamakon ibtila'in girgizar kasa da ke wakana a kasashen Turkiyya da Syria.
Shugabanni kasashen duniya sun yi alkawarin aikewa da tawagar ma'aikata da kayan aikin ceto ya zuwa Turkiyya sakamakon ibtila'in girgizirar kasar.
Rahotanni na cewa an ƙara samun girgizar ƙasa karo na biyu cikin kwana guda a kudu-maso-gabashin Turkiyya.
Hukumar lura da yanayin ƙasa ta Amurka ta ce ƙarfin girgizar ƙasar ya kai 7.5 a kan ma’auni.
Lamarin ya faru ne a gundumar Elbistan na lardin Kahramanmaras.
Wani jami’in Hukumar Lura da Bala’o’i na Turkiyya ya tabbatar da cewa "wannan wata sabuwar girgizar ƙasa ce ba ragowar wadda ta faru ne a farko ba."
Wani faifan bidiyo ya nuna yadda mutane ke gudu cikin ruɗewa a lokacin da girgizar ta biyu ta faru.
An ga mutanen suna ihu, suna gudu a kan tituna a lokacin da ƙura ke lafawa bayan gine-gine sun rufta.
Girgizar kasar mai karfin maki 7.8 ta afkawa yankin Gaziantep da ke kudancin Turkiyya a tsakiyar daren Litinin.
Kuma an jiyo ruguginta har daga Gaza. An kuma samu rushewar gidaje a Lebanon.
Turkiyya dai ta ayyana dokar ta baci tare da kira ga mutane su dakatar da amfani da wayoyinsu, saboda masu aikin agaji su samu damar kai wa ga wadanda suka makale a cikin baraguzai.
A 1999, irin wannan mummunar girgizar kasar tayi ajalin mutane dubu 17.

Taimakon kasashen duniya
Shugaba Biden na Amurka ya yi alkawari ga takwaransa na Turkiyya, Recep Erdogan cewa Amurkar z ata aike da tawagoginta ba tare da bata lokaci ba.
Korea ta Kudu ce kasa ta baya-bayan nan da ta aike da tata gudunmowar ga Turkiyya.
To amma kasashen na shelar cewa aikewa da tawagar da kayan aikin ceto ka iya samun cikas sakamakon rashin kyan hanyoyi da girgizar kasar ta lalata.
To sai dai yayin da ake ta tururuwar taimaka wa Turkiyya, ita kuwa Syria ba ta samu tallafin azo-a-gani ba saboda takunkumin da ke bakinta duk da cewa wasu kawayenta kamar Iran sun aike da nasu tallafin.
Ana can dai ana cigaba da aikin ceto a Kudancin Turkiyya da kuma arewacin Syria kamar yadda wani dan Najeriya mazaunin Turkiyya ya shaida wa BBC.
Kawo yanzu girgizar kasar ta yi sanadiyyar mutuwar mutum sama dubu 5,000.











