Yadda girgizar ƙasa ta kashe mutum 160 a Indonesia

Bayanan bidiyo, Bidiyon yadda girgizar ƙasa ta kashe mutum 160 a Indonesia
Yadda girgizar ƙasa ta kashe mutum 160 a Indonesia

Wata girgizar ƙasa da ta faru a yankin tsibirn Java na Indonesia ta yi sanadin mutuwar a ƙalla mutum 160 tare da jikkata da dama, kamar yadda jami’ai suka ce.

Gigizar ƙasar mai girman maki 5.6 ta faru ne a garin Cianjur da ke yammacin Java, inda ta rarake ƙasa da zurfin kilomita shida, kamar yadda bayanan Sashen Nazarin Ƙasa na Amurka ya nuna.

An garzaya da ɗumbin mutane asibiti, inda da yawansu ma sai a waje aka dinga duba su.

Ba dare ba rana masu aikin ceto na ta ƙoƙarin ceto mutanen da ake zaton sun maƙale a cikin ɓaraguzan gine-gine.