‘Rayuwata ba ta da sauran amfani’

Iyalan Rahmat Gul na ta kokarin kafa tanti daga cikin tantunan da wani dan siyasa na kasar Afghanistan ya bayar da gudumawa.
Daga gefe kuma akwai wani tantin wanda kungiyar agaji ta Red Crescent ta bayar da gudumawa.
Suna kafa tantunan ne a filin wani gida da babu kowa, inda yanzu ya zamo masu muhalli.
Mummunar girgizar kasa da ta afka wa kudu-maso-gabashin Afghanistan ce ta yi raga-raga da gidajensu da ke a lardin Gayan, a kusa da tsakiyar inda girgizar kasar ta faru.
Mutum 7 ne suka mutu lokaci guda a gidan nasu.
Rahmat Gul ya ce "Rayuwata ba ta da sauran amfani.”

Ya kara da cewa "A kan idona yarana mata guda uku da jikokina hudu suka mutu, ina cikin matukar damuwa.”
To sai dai har yanzu yana da sauran yaran da zai kula da su.
Iyalin nasa sun shafe daren washe-garin girgizar kasar a filin Allah yayin da ruwa ya masu mugun duka.
“Muna bukatar taimako, ba mu da komai, duk abin da muka mallaka sun salwanta,” in ji shi.

Shi ma Zarma Gul yana Daya daga cikin wadanda girgizar kasar ta yi kaca-kaca da gidansa.
A lokacin da abin ya faru ya shiga rudani a kan wane ne zai ceta daga cikin iyalansa?
Ya ce “A lokacin da rufin dakuna da bangwaye suka rikito, sai matata ta ce na cece ta, to amma akwai yarinyata ita ma a cikin dakin, sai na fara fitar da ita.”
Daga nan sai ya ruga dayan dakin domin duba sauran ‘yayansa. A lokacin da ya dawo wurin matarsa ta riga ta rasu.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yanzu haka dai ana samun taimakowa daga majalisar dinkin duniya, da kungiyoyin agaji na kasa da kasa da kuma gwamnatin Taliban.
A wurin da iyalain Rahmat suke, kungiyar agaji ta Red Crescent na raba abubuwan bukata kamar mai na girki da bargunan rufa.
Daya daga cikin mutanen da ke cikin cincirindon wadanda ke jira a ba su agaji ya ce “Muna bukatar ko mene ne domin kasa ta danne duk abin da muka mallaka.”
Yanzu haka dai akwai yara kanana da dama wadanda suka raunata.
Sai da aka yi amfani da jirgi mai saukar ungulu na sojoji domin daukan wasu marasa lafiyar zuwa Kabul domin samun kulawa.
Kauyukan da girgizar ta fada ma wa akasarin su suna da nisan kimanin awa uku a mota tsakaninsu da birni mafi kusa, sannan hanyoyi ba su da kyau ko kadan.
Sama da mutum dubu daya ne suka mutu sanadiyyar girgizan kasar da kuma mrka-markan ruwa da aka tafka.
Likitoci a kasar ta Afghanistan sun shaida wa BBC cewa da alama akwai kananan yara da dama wadanda suka mutu sanadiyyar girgizar kasar wadda ta faru a ranar Laraba.











