Afghanistan: Taliban ta ce za ta dawo da zartar da hukuncin kisa

Taliban patrol in Kabul on 23 September 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mullah Nooruddin Turabi, not pictured, said punishments such as amputations were "necessary"

Shugaban Hisba na Taliban a Afghanistan ya ce gwamnatinsu za ta dawo da hukunce-hukunce masu tsauri da suka hada da hukuncin kisa da kuma datse hannu.

Mullah Nooruddin Turabi wanda shi ke kula da gidajen yari ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa datse hannu ya zama dole saboda dalilan tsaro.

Amma ya ce ba lalle ne a zartar da hukunci a bainar jama'a ba kamar yadda ake yi a karkashin mulkin Taliban a shekarun 1990.

Ya kuma yi martani ga ce-ce-ku-cen da a ke yi na zartar da hukunci da suke yi cikin jama'a a baya, inda ya ce "babu wanda zai fada mana yadda dokokinmu za su kasance."

Tun bayan kwace mulki a ranar 15 ga watan Agusta Taliban ta yi alkawarin sassauta tsaurin da aka san kungiyar da shi a baya wurin gudanar da mulki.

Sai dai tun ba a je ko ina ba an fara ba da rahotannin cin zarafin al'umma a fadin Afghanistan.

A rabar Alhamis kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta yi gargadin cewa Taliban na neman wasu sanannun mata a Herat, tana kuma hana mata fita ko ina da kuma kakaba rufe jiki gaba daya.

A watan Agusta ma Amnesty International ta ce mayakan Taliban ke da alhakin kisan wasu mambobi tara 'yan kabilar Hazara.

A cewar Sakatare-Janar ta Amnesty International Agnes Callamard "kisan da ke faruwa a Afghanistan tuni ne na kaurin sunan da kungiyar ta yi na kashe-kashe a baya, sannan wata manuniya ta yadda sabon mulkin kungiyar zai kasance.

Women walking down the street in Kabul

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Rahotanni na cewa an muzguna wa mata

'Yan kwanaki kafin Taliban ta kwace Kabul, alkalin kungiyar Taliban a yankin Balkh Haji Badruddin ya fada wa BBC cewa yana goyon bayan hukunce-hukunce masu tsauri a sabuwar gwamnatin.

"A Shari'armu a bayyane take karara cewa duk wanda ya yi jima'i ba tare da aure ba, mace ko namiji hukuncinsu bulala 100 ne kuma a bainar jama'a," in ji Badruddin.

"Amma ga duk wanda ke da aure ya aikata irin wannan laifi za a jefe shi ne har ya mutu.

"Ga kuma wadanda suka yi sata aka tabbatar da hakan to za a datse musu hannu," a cewar alkalin.

To sai dai a yanzu kungiyar ta fara sassauci kan akidojinta, a wani yunkuri na samun karbuwa ga kasashen duniya, kuma tun da ta karbi mulki, Taliban na kokarin nuna wa duniya cewa ta sauya.

Ko a shekarun 1990 Turabi ya yi kaurin suna wurin hukunta wadanda a ka kama suna sauraren wakokin da ba na Musulunci ba, da kuma wadanda suka rage gemunsu.

A lokacin ana zartar da hukuncin kisa a filin wasan Kabul cikin bainar jama'a, a lokacin Turabi na Ministan Shari'a.

"Kowa na sukarmu da zartar da hukunci a filin wasan Kabul, amma mu ba mu taba cewa komai ba game da dokokinsu da hukunce-hukuncen da suke zartarwa."

Ko a farkon wannan makon Taliban ta bukaci a ba ta damar gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a birnin New York.

A cewar Ministan Harkokin wajen Jamus Heiko Masa, duk da cewa yana da muhimmanci a tattauna da Taliban, amma dai zauren Majalisar Dinkin Duniya bai yi dai-dai da inda za a yi hakan ba.

Ita ma Amurka wadda ita ke tantance wanda zai iya magana a zauren ta ce ba za ta yanke hukunci game da bukatar Taliban ba a wannan gabar.