Yadda nahiyar Afirka za ta hade da Asia da Turai

Taswirar katafariyar nahiya
Bayanan hoto, Tekun Pacific zai bace yayin da katafariyar nahiyar ke haduwa

Doron kasa wanda kamar yadda aka sani yana da koguna da tafkuna da manyan teku-teku a nahiyoyi manya daban-daban, yana sauyawa sannu a hankali bayan wasu dimbin shekaru.

Mutum zai iya fahimtar haka idan dai zai hada hoton taswirar duniya, inda zai ga yadda kasa ta dare ruwa ya shiga tsakani, wanda hakan ya haifar da nahiyoyi daban-daban da tsibirai.

Wata taswira da masu bincike a kasar Australiya suka fitar ta yi hasashen cewa tekun Pacific zai bace, inda nahiyoyin da ya ratsa za su hade wuri daya a samu wata katafariyar sabuwar nahiya da za a kira ta Amasia, can a bangaren arewacin duniya.

To amma fa wannan abu ba zai faru ba nan da wasu shekaru miliyan 200 ko 300.

Abin da masana kimiyyar na jami'ar Curtin ta Australia da jami'ar Peking ta China suka yi hasashen zai faru shi ne, nahiyar Amurka ta Arewa da ta Kudu za su karkata zuwa yamma, sannan nahiyar Asia za ta nufi gabas.

Nahiyar da take kuryar kudu a duniya wadda kuma ita ce ta fi karancin mutane a cikinta, wato Antarctica za ta nufi nahiyar Amurka ta Kudu wato Latin Amurka.

Ita kuwa nahiyar Afirka ta gefe daya za ta hade da Asiya, sannan ta daya bangaren za ta hade da Turai a samu wata katafariyar nahiya da za a kira ta Amasia.

An wallafa sakamakon wannan bincike ne a mujallar kimiyya ta National Science Review.

Samuwar katafariyar nahiya

Jagoran masu binciken Dr Chuan Huang, daga jami'ar Curtin ya ce, "Sakamakonmu ya nuna mana cewa yadda saman duniya ke sanyi karfin tekuna gaba daya na raguwa.

Sannan kuma Tekun Pacific zai motse, ya ragu sosai ta yadda zai kankance, fiye da Tekun Atalantika da Tekun Indiya wadanda su kuma suke kara girma.

Taswirar duniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duniyar da muke gani yanzu, sakamakon wargajewar katafariyar nahiya ne
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An yi hasashen samun sunan 'Amasia' ne inda za a same shi daga hasashen hadewar nahiyar Amurka ta Arewa da ta Kudu wadanda ake kiran hadakarsu biyu America, da nahiyar Asiya.

Katafariyar nahiya ta karshe da aka sani ita ce Pangea, wadda ta dare zuwa wasu nahiyoyin daban, can baya shekaru miliyan 180 da suka gabata.

Wannan nahiya kusan ta hada duniya gaba daya a dunkule, kuma a lokacin tana zagaye ne da wani teku guda daya na duniya baki daya da ake kira Panthalassa.

Masanan sun yi amfani da wata babbar kwamfuta ne inda suka fahimci yadda manya-manyan nahiyoyi ke iya faruwa.

Ta irin wannan nazari ne da suka yi a kwamfuta suka ga cewa tuni ma Tekun Pacific yana tsukewa a duk shekara.

Ko da yake kadan ce tsukewar, amma hakan na nuna cewa zuwa miliyoyin shekaru nan gaba hasashen da suka yi a kan tekun zai iya kasancewa.

Dr Huang ya yi hasashen cewa nahiyar Australia za ta yi karo da Asiya da farko sannan kuma daga karshe ta hade da nahiyoyin Amurka ta Arewa da ta Kudu, bayan Tekun Pacific ya bace.

Wani hasashen na daban

A baya ma masu bincike sun taba yin irin wannan hasashe na samun wasu manya-manyan nahiyoyin uku, kafin wannan da wadannan masanan suka yi a yanzu na samun Amasia.

Wadanda aka yi hasashen a wancan lokacin su ne Novopangea da Pangea Ultima da kuma Aurica.

Taswirar kasa da teku da karakashin teku

Asalin hoton, Getty Images

Wannan nazarin ya nuna shakku a kan kasancewar wasu hasashen na daban.

Tabbaci dari bisa dari kusan abu ne da za a iya cewa ya yi karfi sosai wanda ba a saba amfani da shi ba a al'amarin da ya shafi kimiyya ba.

Musamman ma idan ana magana a kan sauyin doron duniya, wanda a yanzu ne muka ma fara fahimtar yadda yake gaba daya,'' in ji Zheng-Xiang Li, daya daga cikin wadanda suka samar da rahoton.

Masanin ya kara bayani da cewa, ''Dukkanin wannan abu da muke gani zai faru da ma wadanda wasu suka yi a baya, hasashe ne kawai a kan doron ilimin da muka fahimta a yanzu.'' An yi kiyasin cewa duniya ta kai kusan shekara biliyan hudu da rabi ( 4.5 ). A irin sauyin da duniya ke yi, motsin da take yi da kuma ballewar nahiyoyi abu ne da ke faruwa kusan a duk bayan wani lokaci mai tsawo.

Li ya yi bayanin yadda suka kai wannan hasashe inda ya ce su nahiyoyi suna tafiya ko matsawa ne a sakamakon motsin da wasu manyan farantai da ke karkashin tekuna suke yi.

Masaniin ya yi bayanin cewa sun yi amfani da kwamfuta inda suka samar da yanayi daidai da na duniya gaba daya, wanda ya kunshi doron duniyar kansa wanda ya hada da tekuna, da kuma wadandan manyan farantar da ke karkashin tekuna.

Daga nan ne suka rika nazari domin gano abubuwan da ke iya haifar da ,manya-manyan nahiyoyi.

Motsi a karkashin tekuna

Sakamakon da masu binciken suka samu ya nuna karfin motsin wadannan manya-manyan farantai da ke karkashin teku na taka gagarumar rawa wajen samuwar katafariyar nahiya.

Dr Chuan Huang a dakin bincikensa

Asalin hoton, Dr Chuan Huang

Bayanan hoto, Dr Chuan Huang ya ce katafariyar nahiya ta gaba za ta samu a sanadiyyar bacewar Tekun Pacific

Yadda duniya ke rasa zafin da take da shi a can cikinta sannu a hankali a tsawon biliyoyin shekaru, doron kunya-kunyar da ke karkashin teku wadda take da kaurin kilomita 7 zuwa 8 yana raguwa sannu a hankali saboda wannan zafi na duniya da ke raguwa, inda kuma hakan ke samar da wasu kunya-kunyar.

Masanin ya ce to wannan abu da ke faruwa ya sa suka yi hasashen cewa za a iya samun wannan katafariyar nahiya ne a dalilin rufewar Tekun Pacific.

Samuwa da kuma wargajewar katafariyar nahiya har kullum suna da babban tasiri a kan yanayi da kuma muhalli.

A takaice samuwar katafariyar nahiya za ta kai ga raguwar zurfi ko yawan ruwan teku, wanda shi kuma hakan zai kai ga karuwar doron kasa, inda hakan zai sa wata nahiya ta hade da wata a samu katafariyar nahiya, maimakon da yadda ake da su daidai.

 Zheng-Xiang Li a gaban gona

Asalin hoton, Zheng-Xiang Li

Ta daya bangaren kuma, kishiyar abin da muka bayyana, a yayin wargajewar katafariyar nahiya, yawan ruwan teku zai karu, za a samu bunkasar rarrabe-rarrabe na halittu wanda hakan abu ne da zai amfani rayuwa.

Dr LI, ya ce, ''abu ne mai wuya a iya hasashen yadda mutum zai zama nan daruruwan miliyoyin shekaru masu zuwa,

Amma a matsayin mutum na kasancewa mai matukar muhimmanci a duniya, mutun zai ci gaba da kasancewa kamar yadda rayuwa take.

Ya kara da cewa, ''na yi amanna basira da kwarewarmu za su sa mu iya jurewa tare da tafiya da kowa ne irin sauyi aka samu a duniya a nan gaba, kamar yadda ya kasance a baya.''