Yadda ake gane an samu matsalar gani
Latsa alamar lasifika da ke sama don sauraron hira da Dr. Fatima Kyari, likitar ido a Hukumar yaki da makanta ta duniya
Wasu alkalumman sun nuna cewa mutum biliyan daya ne basa iya gani garau.
Masu bincike sun ce kashi 4 cikin mutum dari na fama da cutar makanta musamman manya da suka haura shekara 40.
Taken ranar ta bana shi ne ''Gani shi ne gaba da komai'', kuma bikin zai mayar da hankali ne wajen lalubo hanyoyin tabbatar da ganin cewa kowanne mutum, a duk inda yake a duniya na iya samun hanyar inganta ganinsa.