Hamas ta dakatar da tattaunawa da Isra'ila saboda shirinta na ƙwace Gaza

Naima, mahaifiyar Hala Zaarab da ke alhini mutuwar ƴartata da bata jima da auren ba sakamkon harin ta sama da sojin Isra'ila suka kai, inda ake rarashin ta a Khan Younis da ke Kudancin Gaza a ranar 3, ga watan Mayun, 2025.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Jmai'an Isra'ila sun ce wuraren da za su kai hare-haren ya haɗa da raba kaso mai yawa na al'ummar gaza miliyan 2.1 da muhallansu
    • Marubuci, David Gritten
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Jerusalem
  • Lokacin karatu: Minti 4

Wani babban jami'in ƙungiyar Hamas ya ce babu wani dalili na ci gaba da tattaunawa kan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya bayan da Isra'ila ta amice da faɗaɗa hare-haren da take kaiwa a Zirin Gaza.

Matakin na Isra'ila zai iya haɗawa da ƙwace yankin na Falasɗinu da kuma tilasta wa Falasɗinawan barin gidajensu.

Bassem Naim ya shiada wa BBC cewar ba za su shiga tattaunawa da sababbin buƙatu ba, alhali Isra'ila na ci gaba da azabtar da mutanen ta hanyar "amfani da yunwa a matsayin makamin yaƙi".

A ranar Litinin sojojin Isra'ila suka sanar da shirinsu na ƙara faɗaɗa hare-haren a wani yuƙuri na dawo da fursunonin da Hamas ke rike da su.

Jami'an Isra'ila sun ce hakan ya haɗa da "mamaye Gaza, raba kaso mai yawa na al'ummar yankin da matsugunensu, da karɓe ikon kula da harkokin raba kayan agaji bayan wata biyu da hana shigar da kayayyakin, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce hakan ya haifar da ƙarancin abinci.

Jami'an sun ce ba za su fara aiwatar da hakan ba har sai Shugabna Amurka Donald Trump ya kammala ziyarar da zai kai yankin a mako mai zuwa, wanda suka bayyana shi da bai wa Hamas "kofar damar amincewa" da sabuwar yarjejeiniyar.

Sai dai kalaman da Bassem Naim ya yi ranar Talata sun ci karo da hakan.

Sakatare Janar na MDD António Guterres ya yi gargadin cewa ci gaba d faɗaɗa hare-haren da Isra'ila ke kaiwa da kasancewar sojojinta tsawon lokaci a Gazan, babu makawa zai haifar da "asarar rayuka marasa adadi tare da ƙara rusa Gaza".

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Firaministan Birtaniya Sir Kier Starmer da Shugaban Faransa Emmanel Macron sun bayyana damuwarsu kan yadda al'amura ke tafiya a yankin na Zirin Gaza, inda suka amince da cewar "sake dawo da zaman lafiya a yankin ake buƙata" a cewar fadar Firaministan Birtaniya.

A washington, Shugaban Amurka Donal Trumo ya ce amurka zata taimaka wa mutanen Gaza da abinci , sai dai bai bayar da karin wasu bayanai kan me ya ke nufi da hakan ba.

"Mutane na fama da yunwa kuma zamu taimaka musu wajen ganin sun samun abinci. Mutanen masu yawa na sa lamarin an kazanta,' a cewar a. "Hamas ba zasu sa hakan ya zama abin wahala ba, kasancewar duk abin da aka shigar musu da shi."

Isra'ila ta dai yanke dukkan wasu kaya d ake shigar da su Gaza tun a ranar 2 ga watan Maris, sannna ta dawo da kai hare-hare makonni biyu da lalacewar yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma wattani biyu kafin lokacin, tana mai cewar tana masatwa Hamas lamba wajen sako fursum=nonin da ta ke riƙe da su.

Haka kuma ta zargi Hamsa da sacewa tare da ajiye kayan agaji, wani zargi da Hamsa ɗin ta musanta.

Hukumomin bayar da agaji sun yi gargaɗin cewar idan har ba a sami wani sauyi ba kan wannan manufa ta Isra'ila ba, babu makwa za a sami ƙaruwar yanuwa.

Haka kuma sun yi Allah wadai da buƙatar Isra'ila na kai kayan agaji Gaza ta hanyar amfani da kamfanonin ayyuakan jinƙai masu zaman kansu, ƙarƙshin cibiyoyin da sojojin Isra'ila ke kula dasu, tana mai cewar hakan zai zama karya ƙaidojin jinƙai na duniya, wand ako kaɗan ba zasu basu haɗin kai ba.

Majalisar ɗinkin duniya ta ce tilasa ne ISra'ila ta bai dokar ƙasa da ƙas, wajen barin a shigar abinci da magani zuwa ga al'ummar Gaza. Isra'ila ta ce tana bin dokar ne saboda babu ƙarancin kayan jiƙan.

Sojojin Isra'ila sun kadamar da wani shiri na rusa Hamsa, a wani martani na harin da Hamsa ta kai mata na ranar & ga wtaan Octoban 2023, da ya janyo mutuwar mutum 1, 200, yayin da aka kama fursunoni 251.

Hukumar lafiya ta Hamsa ta ce aƙalla mutum 52, 567 ne suka mutu a Gaza tun wanna lokaci, yayin da kuma mutum 2, 459 ne suka mutum bayan da Isra'ila ta dawo da kai hare-hare na baya bayan nan.