Sojan ko-ta-kwanan Isra'ila ya nuna adawa da yaƙin Gaza

- Marubuci, Paul Adams
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem
- Lokacin karatu: Minti 4
Yaƙin Isra'ila a Gaza na ci gaba da wakana, yayin da adawa da shi ke ci gaba da ƙaruwa a cikin Isra'ila.
A makonnin baya-bayan nan, dubban sojoji masu jiran ko-ta-kwana daga fannoni daban-daban na rundunar sojin ƙasar ne, suka sanya hannun kan takardun buƙatar gwamnatin Netanyahu ta dakatar da yaƙin, tare da mayar da hankali wajen cimma yarjejeniyar maido da Isra'ilawa 59 da ke hannun mayaƙan Hamas.
A cikin watanni 18 da suka gabata, ƴan Isra'ila ƙalilan ne suke da shakku kan dabarar yaƙin: ''Karya Hamas tare da maido da duka Isra'ilawan da ake riƙe da su''.
Sai dai bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta watan Janairu, tare da sako fiye da Isra'ilawa 30, sai fatan kawo ƙarshen yaƙin ya ƙaru a zukatan da yawa cikin ƴan Isra'ila.
Bayan Isra'ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wutar tare da komawa yaƙi a tsakiyar watan Maris, sai fatan ya gamu da cikas.
"Mun yarda cewa wurin da Isra'ila ta nufa ba mai kyau ba ne,'' a cewar Danny Yatom, tsohon shugaban hukumar leƙen asirin ƙasar.
''Mun fahimci cewa abin da kawai ke gaban Netanyahu shi ne biyan buƙatar ƙashin kansa. Kuma a cikin manyan abubuwan da ya sanya a gaba, buƙatar ƙashin kansa da gwamnatinsa su ne kan gaba, ba na waɗanda ake garkuwa da su ba.''
Da dama cikin waɗanda suka sanya hannu kan takardun buƙatar kawo ƙarshen yaƙin, irin su Yatom, sun jima suna sukar firaministan.
Wasu daga ciki ma sun shiga zanga-zangar adawa da gwamnati - wadda ta gabaci ɓarkewar yaƙin ranar 7 ga watan Okotoba bayan harin Hamas a Isra'ila.
To amma Yatom ya ce ba wannan ne dalilinsa na yin magana a yanzu ba.
"Na sanya hannuna ciki, sannan na shiga zanga-zangar ce ba don dalilin siyasa ba, sai domin ƙasata," kamar yadda ya ce.
"Ina matuƙar damuwa kan yadda ƙasata ke fuskantar rashin makoma."

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Buɗaɗɗiyar wasiƙar farko da aka fara wallafa wa a farkon watan Afrilu, sojojin sama masu jiran ko-ta-kwana da waɗanda suka yi ritaya 1,000 ne suka sanya mata hannu.
"Ci gaba da yaƙin ba shi da wani amfani,'' kamar yadda suka rubuta, ''kuma hakan zai haddasa mutuwar waɗanda ake garkuwa da su a Gaza''.
Waɗanda suka sanya hannun sun buƙaci ƴan Isra'ila su bi sahunsu kafin lokaci ya ƙure wa waɗanda aka yi garkuwa da su, 24 da aka yi ƙiyasin cewa suna raye a Gaza.
"A kowace rana rayuwarsu na ƙara shiga cikin hatsari. Kowane lokaci abubuwa na ƙara dagulewa."
A cikin makonni bayan wasiƙar farkon, an yi ta samun wasu wasiƙun daga kusan ko wani fanni na sojojin ƙasar, ciki har da sashen tsoffin sojojin yaƙi da na tattara bayanan sirri.
Fiye da mutum 12,000 ne suka sanya hannu kan buƙatun.
Bayan harin 7 ga watan Octoba, dubban sojoji masu jiran ko-ta-kwana ne suka amsa kiran yaƙi, waɗanda suka zaƙu su bayar da gudunmowarsu.
Amma a yanzu, da dama cikinsu na bijirewa, yayin da rahotonni ke cewa raguwar sojojin ko-ta-kwanan a yaƙin ya kai zuwa kashi 50 zuwa 60 cikin 100.
Ga sojojin da suka dogara kan masu jiran ko-ta-kwanan domin yaƙin, adadin ya yi raguwar da ba a taɓa gani da tun bayan yaƙin Isra'ila na farko a 1982.
A wani wurin shaƙatawa mai cike da ganyayyaki a Birnin Ƙudus, na haɗu da ''Yoav'' (Ba sunansa na gaskiya ba), wanda ke cikin sojoji masu jiran ko-ta-kwana, da ya buƙaci na sakaya sunansa.
Yoav ya je yaƙin Gaza a bazarar da ta gabata, amma yanzu ya ce ba zai sake komawa ba.
"A baya na ji cewa ya kamata na je domin taimaka wa ƴan'uwana maza da mata," in ji shi.
"A lokacin na yi imanin cewa, abu mai kyau nake yi, amma yanzu ba haka nake kallon yaƙin ba."
Yoan ya ce burin gwamnati na ci gaba da yaƙar Hamas, yayin da waɗanda ake garkuwa da su ke cikin hatsarin mutuwa a hanyoyin ƙarƙashin ƙasa, kuskure ne.
"Muna da ƙarfin da za mu iya murƙushe Hamas, amma ba batun murƙushe ƙungiyar ba ne, magana ake ta tafka wa ƙasarmu asara."

Asalin hoton, Getty Images
A lokacin da ya je Gaza, Yoav ya faɗa wa BBC cewa, ya yi ƙoƙarin ''zama soja mai nagarta da ake son kowane soja ya zama''.
To amma yadda yaƙin ya tsawaita, ya sa masu suka ke cewa yana da matuƙar wahala ga Isra'ila ta ci gaba da yin iƙirarin da ta saba yi cewa sojojinta su ne mafiya nagartar soji a duniya.
Cikin wata muƙala da ya rubuta a Jaridar Haaretz, wani tsohon Janar Amiram Levin ya ce lokaci ya yi da sojojin Isra'ila ciki har da manyan kwamandoji za su fara tunanin bijire wa umarni.
A birnin Tel Aviv, inda ake yawan samun zanga-zangar fiye da shekara guda, an yi ta nuna hotunan waɗanda Hamas ke garkuwa da su , tare da rungumar hotunan ƙananan yaran Falasɗinawa da aka kashe a lokacin yaƙin.
Yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar irin waɗannan wasiƙu, nuna irin waɗannan hotuna masu sosa zuciya ka iya shafar farin jinin gwamnati.
A ranar 20 ga watan Afrilu, ƴansanda sun faɗa wa masu zanga-zanga cewa ''ba za a bari su ci gaba da riƙe hotunan ƙananan yara da jariran Gaza ba, tare da kwalayen masu ɗauke da wasu kalamai irin ''kisan ƙare dangi'' ko ''kisan kiyashi''.
Bayan nuna damuwa daga masu shirya gangamin ƴansandan sunyi gaggawar janye buƙatar.
A yanzu haka dai Netanyahu na ci gaba da magana kan burinsa na murƙushe Hamas.
Firaministan ya dage cewa matsin lambar soji ne kaɗai hanyar maido da waɗanda ake garkuwa su gida.











