Majalisar tsaron Isra'ila ta amince da shirin 'ƙwace' Zirin Gaza

Hoto na nuna tankar Isra'ila na shiga Gaza (18 March, 2025)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Rundunar sojin Isra'ila ta kira dubun dubatar sojojin kar ta kwana, tana mai cewar tana shirin kara matsa wa Hamas lamba
    • Marubuci, David Gritten
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Jerusalem
  • Lokacin karatu: Minti 5

Majalisar tsaron Isra'ila ta amince da faɗaɗa hare-harenta na soji kan Hamas, wanda suka haɗa da "kama" Gaza, tare da ci gaba da riƙe iko da zirin, a cewar wani jami'in Isra'ila.

Haka kuma, an ce cikin shirin nata har da mayar da Falasɗinawa miliyan 2.1 da ke Gaza zuwa kudancin zirin, wanda hakan ka iya ƙara haifar da ƙalubale ga ayyuakan jin ƙai.

Jami'in dai ya ce Firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana hakan a matsayin "shiri mai kayu" saboda hakan ya ce zai ba shi damar cimma burinsa na murƙushe Hamas, tare da dawo da sauran fursunonin da take riƙe da su gida.

Majalisar ta kuma amince da ƙa'idoji, da shirin kai kayan agaji ta hanyar amfani da kamfanoni masu zaman kansu, wanda zai kawo ƙarshen rufe hanyoyin da Majalsiar Ɗinkin Duniya (MDD) ta koka da cewar shi ne ya haifar da ƙarancin abincin da aka fuskanta a Gazan.

MDD da sauran ƙungiyoyin bayar da agaji a duniya sun ce wannan buƙata ka iya zama karya ƙa'idar ayyuakan jinƙai, kuma ba za su amince da hakan ba.

Majalisar zartarwar Firaminista Benjamin Netanyahu ta gudanar da wani taro a yammacin ranar Lahadi don tattauna batun tsagaita wuta a Gaza, kuma ana sa ran za a dawo a ci gaba da tattaunawa kan lamarin, wattanin biyu bayan da Isra'ila ta kawo karshen tsagaita wutar, 18 ga watan Maris.

Wani jami'in Isra'ila da ya yi wa manema labarai ƙarin bayani a ranar Litinin ya ce minsitocin sun amince da buƙatar da babban hafsan sojin Isra'ilan Janar Eyal Zamir ya gabatar na "murƙushe Hamas a Gaza tare da mayar da fursunonin gida".

"Shirin dai ya haɗa da kame Gaza da ci gaba da iko da zirin, da mayar da Falsdinawan zuwa kudancin yankin, tare da hana Hamas raba kayan agaji, da kai tsauraran hare-hare kan Hamas," a cewar jami'in.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kafafen yaɗa labarai na Isra'ila sun ruwaito cewa shirin zai ɗauki lokaci ana yin sa, sannan matakin farko ya haɗa da kame ƙarin waurare a Gaza, da faɗaɗa wuraren da Isra'ilan ta bayyana a masatyin "sararin tsaro" a kan iyakokinta, a wani yuƙuri na ƙara wa Isra'ilar kima a teburin tattaunawa da Hamas kan sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da sakin fursunoni.

Daya daga cikin yan majalisar tsaron ta Isra'ila Zeev Elkin ya shida wa wani danjarida cewa 'har yanzu akwai damarmaki' na sakin sababbin fursunoni, kafin ziyarar Shugaba Trump a ranar 13 zuwa 16 ga watan Mayu zuwa Gabas ta Tsakiya "inda Hamas ta fahimci cewar sun ɗauki batun da mahimmancin".

A yayin wata ziyara a sansanin sojin ruwa a ranar Lahadi, Janar Zamir ya shaida wa dubun dubatar dakarun na kar ta kwana cewar an kira su ne "don kara karfafawa tare da ƙarfafa ayyukan Isra'ila a Gaza".

"Muna ƙara matsa lamba ne kan Hamas a wani yunƙuri na dawo da mutanenmu gida, da yin galaba kan Hamas. Za mu ci gaba da aiki a karin wasu wurare tare da kawar da dukkan wani sansanin yan ta'adda da ke kan ƙasa da ƙarƙashin ta.

Sai dai masu sharhi sun ce shiri ne da ba zai yi nasara ba saboda babu ko da mutum ɗaya cikin fursunonin da aka saka tun bayan da Isra'ila ta koma kai hare-hare a Gaza makonni shida da suka gabata.

Kungiyar iyalan fursunoni da wadanda suka bata da ke wakiltar wadanda ake riƙe da su a matsayin fursunonin sun ce shirin da gwmantin Isra'ilan ke amfani da shi "na fifita faɗaɗa iyakokinta ne ba wai ceto fursunonin ba" kuma hakan "ya saɓa da muradin kashi 70 cikin 100 na al'ummar" ƙasar.

Falasdinawa na raƙe da kwanukansu, yayn da kungiyar dake musu rabon abinci a Khan Younis, a Kudancin Gaza (2 May 2025)

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ƙungiyar da ke dafa abinci a Gaza ta ce 'yan kwanaki ya rage musu kafin kayan abinci su yanke musu

Jami'an Isra'ila dai sun ce majalsiar tsaron ta Isra'ilan ta amince da "da yiwuwar yin rabaon kayan jinƙai idan har ta kama, zai iya hana Hamas samun iko kan kayan jiƙan, wanda kuma hakan zai lalata dukkan wani yunƙuri na gwamantinsu, ya sami rinjaye mai yawa.

A ranar Lahadi kungiyar agaji ta Humanitarian Country Team (HCT), wadda ta kunshe hukumomin majalsiar dinkin duniya, sun ce jami'an Isra'ila na neman buƙatar a "rufe kofar dukkan wani aiki jinƙai da ake da shi" kuma "sun samu amincewa da kai kayan agaji ta cibiyoyin Isra'ila, amma bisa wasu sharuɗai da sojin Isra'ila suka gindaya, da zarara kuma gwamanti ta amince da musayar".

HCT ta yi gargadin cewar shirin na nufin yankin mai yawa a Gaza da mutanen masu rauni za su ci gaba da fuskantar ƙarancin kayan jinƙan.

"Ya ci karo da ka'idar ayyukan jinƙai, kuma hakan ya zama tamakar wata hanya da ƙarfafa kula kaya masi amfani da ake buƙata na yau da kullum a wata dabara ta matsa ƙaimi, a wani yuƙuri na abarun soji n na Isra'ilan.

"Yana da matuƙar haɗari, kora fararen hula yankin da ke ƙarƙashin sojoji,kuma barazana ne ga rayuwarsu, ciki kuma har da fararen hula wanda hakan zai shafa, yayin da hakan ke zama tamkara wata hanyar tursasa musu rabuwa da muhallansu."

Isra'ila dai ta yanke kai dukkan wani kayan agaji da sauran kayan agaji zuwa Gaza, a ranar 2 ga watan Maris, mako biyu kafin ta koma ci gaba da kai harin da ta ke.

A cewar Majalsiar Ɗinkin Duniya ta ce Falasdinawa na fuskantar sabbin haɗari na yunwa, da ƙarancin abinci mai gina jiki saboda yadda wauraren ajiye abincin sun kasance wayam, gidaje gashi sun kasance a rufe, yayin da kuma ƙungiyar da ke dafa abinci a Gaza kwanaki ya rage su ƙare.

Hana kayan agajin dai ya janyo yankewar kaya masu mahimmanci irin magani, da alurai, da sauran kayan kula da lafiya da cibiyoyin lafiya ke matuƙar buƙatar su a Gaza.

Majalisar ɗinkin duniya ta ce Isra'ila ta amince da bin dokar ƙasa da ƙasar ne, wajen ganin an shigar da kayan a gaji, zuwa ga al'ummar Gaza, wadan kusan dukkan su sun rasa matsugunensu.

Dakarun Isra'ila sun ƙadamar da shirin latata Hamas a wani martani kan wani hari na tsallaka iyaka da aka kai mata a ranar 7 ga watan Octoban 2023, kuma an halaka aƙalla mutum 1, 200, yayin da aka riƙe mutum 251 a matsayin fursunoni.

A cewar ma'auikatar lafiya ta Hamas, aƙalla mutum 52,567 aka kashe a Gaza tun lokacin, ciki har da mutum 2, 459, tun sanda Isra'ila ta dawo da ci gaba da kai hari.