Isra'ila za ta ci gaba da zama a Gaza har bayan yaƙi

A Palestinian girl walks past a destroyed building following overnight Israeli strikes on Jabalia's south-western district of Nazla, in northern Gaza (16 April 2025)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mazauna Gaza sun ce Isra'ila ta kai sabbin hare-hare a kudu masu yammacin Jabalia
    • Marubuci, David Gritten
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 2

Ministan tsaro na Isra'ila ya ce dakarun ƙasar za su ci gaba da kasancewa a Gaza, a wuraren da aka bayyana a matsayin na tsaro da aka samar bayan mamaye fili mai girma a yankin.

Israel Katz ya ce wuraren tsaron da dakarun za su zauna za su zamo "kariya" ga wasu matsugunan Yahudawa a lokacin da ake buƙatar ɗaukar "mataki na wucin-gadi ko kuma na dindindin."

Isra'ila ta shiga mako na shida da ta toshe yankin Gaza daga samun tallafi domin matsa wa Hamas ta saki mutanen da take garkuwa da su, kamar yadda ya bayyana, duk kuwa da gargaɗin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi cewar lamarin na da "mummunar illa."

A ranar Laraba Ƙungiyar Likitocin ƙasa da ƙasa (MSF) ta zamo ta baya-bayan nan da ta yi gargaɗi kan illar matakin da Isra'ila ta ɗauka kan yankin, inda ta ce "an mayar da Gaza makeken kabari binne Falsɗinawa da kuma masu zuwa kai musu ɗauki."

Tents housing displaced Palestinians in the campus of the Islamic University in Gaza City (16 April 2025)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kimanin Falasɗinawa 500,000 ne aka tarwatsa tun bayan da Isra'ila ta sake ƙaddamarwa bayan rushewar yarjejeniyar tsagaita wuta

"Abin da muke gani a zahiri shi ne lalatawa da kuma kawar da wata al'umma ala tilas a Gaza," in ji shugaban sashen ɗaukin gaggawa na ƙungiyar, Amande Bazarolle.

Ma'aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce an kashe sama da mutum 1,650 tun bayan da Isra'ila ta sake ƙaddamar da yaƙi a yankin ranar 18 ga watan Maris bayan ƙarewar matakin farko na tsagaita wuta.

Asibitoci sun ce hare-haren Isra'ila sun hallaka aƙalla mutum 24 a ranar Laraba.

Akasarin waɗanda aka bayar da rahoton kashewa sun kasance ne a birnin Gaza da ke arewaci.

Cikin su har da mutum 10 daga cikin iyalan Hassouna, waɗanda mafi yawansu mata ne da yara. Ɗaya daga cikinsu ita ce Fatema Hassouna – wadda matashiyar marubuciya ce kuma mai ɗaukar hoto.