Yadda Rasha ke ɗaukar ƙarin sojoji don yaƙar Ukraine

Rahoto daga Will Vernon

BBC News, Volosovo, yammacin Rasha

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dubban dakarun Rasha aka kashe ko aka raunata tun ɓarkewar faɗan, in ji jami'an ƙasashen Yamma

Garin Volosovo da ke kusa da St Petersburg, na samun ci gaba. Ba wai ta fuskar tattalin arziki ba - batun lasifika ne.

Kamar wasu garuruwa da dama a Rasha, a Volosovo an sanya lasifika da dama kan dogayen sanduna da ke kan kan titi.

A yanzu, ana amfani da su wajen sauraron waƙa ta kishin ƙasa a ranakun hutu. Sai dai a yanzu, ana amfani da su ne kan wani dalili na daban.

"An samar da makaman atilari. Mun gayyaci maza masu shekaru tsakanin 18 zuwa 60 su bi sahu," irin wannan sanarwa ake ji ta lasifikokin.

Saƙo ne da ake ta maimaitawa a ƙasar. A kafafen sada zumunta da Talabijin da allunan sanarwa, an buƙaci maza su rattaba hannu kan wani kwantiragin aiki da rundunar soji domin yaƙi a Ukraine.

Yayin da ƙasar ke tafka gagarumar asara a yaƙin, hukumomi sun ƙaddamar da shirin ɗiban sabbin sojoji aiki.

Na tambayi wani mutum a Volosovo ko yana goyon bayan samar da ƴan sa-kai. "Eh! Da a ce matashi ne ni, zan je, amma yanzu na tsufa," kamar yadda ya faɗa min yana dunƙule hannu. "Mu afka musu da bama-bamai!"

Amma akasarin mutanen da ke garin ba su nuna ƙaguwa. "Akwai raɗaɗi idan aka yi maganar [Yaƙin]," in ji wata mata. "Bai dace a riƙa kashe mutane ba." Na tambaye ta abin da za ta ce idan ɗaya daga cikin ƴan uwanta ya nuna sha'awar shiga aikin. "Me ya sa za su je? Gawarwakinsu kawai za a dawo da su."

Kuma da yawa dawo da su za a yi.

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Bidiyon da ake yaɗawa na jan hankalin matasa maza su shiga rundunar sojin Rasha
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rasha ba ta fitar da kididdiga amma jami'ai daga ƙasashen Yamma sun ce sojojin Rasha tsakanin 70,000 zuwa 80,000 ne aka kashe ko aka raunata tun bayan da ƙasar ta mamaye Ukraine wata shida da suka gabata.

Hukumomi a yanzu suna bai wa masu sha'awar aikin maƙudan kuɗaɗe da filaye da kuma bai wa 'ya'yansu gurbi na musamman a makarantun Rasha duk domin ƙara kwaɗaitar da wasu.

Jami'ai an ziyartar gidajen gyaran hali na Rasha domin rubuta sunayen fursunoni inda suka yi musu alƙawarin ba su ƴanci da kuɗi.

Ɗan jarida mai binciken ƙwaƙwaf Roman Dobrokhotov ya ce yadda ake tururuwar nemo mutane ya nuna yadda hukumomi suka damu: "Waɗan nan ba su ne sojojin da ake buƙata ba domin samun nasara a yaƙi. Fadar Kremlin har yanzu tana da yaƙinin samun nasara. Cewa za su share wa dubban mutanen da bashi ya yi wa katutu hawayensu, su kuma samu damar aike su zuwa filin daga."

Duk da irin tagomashin da ake yi musu tayi - har kusan $5,700 duk wata a wasu lokutan - Roman ya ce abin da yake faruwa a zahiri ya banbanta.

"Mutane ba sa kallon kuɗin. Suna dawowa daga Ukraine kuma suna faɗa wa ƴan jarida yadda aka yaudare su. Wannan ma yana tasiri kan lamarin, rashin yadda a gwamnati, don haka bana tunanin za a yi nasara a wannan tsarin."

Amma wasu na murnar shiga.

Ɗan Nina Chubarina, Yevgeny ya fice daga ƙauyensu da ke yankin Karelia da ke arewaci domin ya shiga cikin ƴan sa-kai. Nina ta ce an bai wa ɗanta wanda ba shi da kwarewa a aikin soja bindiga aka kuma tura shi Ukraine.

Ƴan kwanaki bayan nan kuma aka kashe shi yana da shekara 24.

.
Bayanan hoto, Nina Chubarina ta ce ta yi ƙoƙarin hana ɗanta zuwa Ukraine domin yaƙar Ukraine

Nina ta yadda ta hau da ni a wani wajen shaatawa da ke kusa da Moscow inda ta samu aiki a wata masana'antar buga biredi. Ta ce aikin aikin zuba biredin a leda na taimaka mata ta ɗauke zuciyarta daga rashin ɗanta.

Ta tuna yadda ta riƙa roƙon ɗan nata kada ya je Ukraine.

"Na yi ƙoƙarin yi masa magana. Na yi kuka; Na ce 'Ana yaƙi, kashe ka za a yi!' Ya ce 'Mama, komai zai tafi lafiya."

Nina ta caccaki yadda hukumomi ke ɗaukar ƴan sa-kai su yaƙi Ukraine.

"Kawai suna tura su ne kamar ƴan tsaki! Wasu ma ba su taɓa riƙe bindiga ba . Sojojin na tunanin sun samu ƴan sa kai; da suka shirya zuwa filin daga.

Ba kowa ne ya ƙagu ya shiga aikin ba kamar Yevgeny.

Idan ka zagaya cikin ƙasar nan, babu abin da zai nuna maka cewa al'ummar Rasha na goyon bayan samamen na musamman ɗari bisa ɗari," kamar yadda Kremlin take jin daɗin kiran sa.

An kashe Yevgeny Chubarin an kwanaki da shiga rundunar sojin Rasha domin yaar Ukraine
Bayanan hoto, An kashe Yevgeny Chubarin an kwanaki da shiga rundunar sojin Rasha domin yaar Ukraine

An samu raguwar motocin da ke kan titunan Rasha da suka zana alamar "Z".

Ƙwararru sun ce yawan mutanen da ke shiga aikin sojan ba su taka kara sun karya ba.

Wani mai nazari kan ayyukan sojoji Pavel Luzin ya ce mutane a nan ba su shirya sadaukar da kansu ba ga Shugaban ƙasarsu.

"Matsalar Kremlin shi ne akasarin al'ummar Rasha ba za su sadaukar da kansu ba ga Putin. Ɗaukan aiki ba zi yiwu a yanayin da ake ciki ba saboda babu haɗin kai tsakanin ƴan Rasha game da yaƙin.

"Ka kwatanta yanayin da Ukraine. Ƴan Ukraine a shirye suke su yi yaƙi."

Godiya ga Alla Konstantinova daga Mediazona.