Yakin Ukraine: ‘Yan Ukraine nawa ne suka tsere daga gidajensu, ina suka tafi?

Mariupol

Asalin hoton, Reuters

Rasha ta mayar da daukacin hankalinta a gabashin Ukraine bayan janye dakarunta daga kusa da birnin Kyiv.

An umarci mutane su fice daga yankin gabanin Ukraine ɗin saboda fargabar sabbin hare-hare.

Mutane fiye da miliyan 11 ne aka yi amanna sun tsere daga gidajensu a Ukraine tun bayan da aka fara rikicin, a cewar Majalisar Dinkin Duniya (MDD).

Baya ga mutum miliyan biyar da suka fice zuwa kasashe makwabta, karin wasu miliyan shida da dubu dari biyar ne aka yi amanna sun rasa matsugunansu a cikin ita kanta kasar da yaki ya ɗaiɗaita.

Ina mutane ke tserewa a cikin kasar Ukraine?

Mataimakiyar Firaministan Ukraine, Iryna Vereshchuk, ta yi gargadin cewa ko mutanen gabashin kasar su fice gabanin sabbin kai hare-hare ko su jefa rayuwarsu cikin hadari.

Ba a san yawan adadin wadanda suka iya ficewa ba.

Magajin garin Mariupol Vadym Boichenko ya shaida wa gidan talabijin na kasar cewa mutane 100,000 ne ke makale a cikin birnin.

Ya ce gwamnati na fatan aikewa da manyan motoci 90 don kwashe mutane 6,000 a ranar Laraba.

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya na miliyan shida da dubu dari biyar an samo su ne daga binciken da aka Hukumar Lura ta Kaurar Jama'a ta Kasa da Kasa (IOM) ta gudanar tsakanin 9 zuwa 16 ha watan Maris.

Akwai yiwuar aihinin jimilar ta karu a cikin makonni masu zuwa.

A cikin mutane 2,000 da suka rasa matsugunansu da hukumar ta IOM da gudanar da bincike a kai:

  • kusan kashi 30 bisa dari sun fito ne daga birnin Kyiv, fiye da kashi 36 bisa dari sun tsere daga gabashin Ukraine kana kashi 20 bisa dari sun fito ne daga arewaci
  • kusan kashi 40 bisa dari yanzu sna yamamcin Ukraine, da kasa da kashi 3 bisa dari a birnin Kyiv
  • kashi 5 bisa dari kacal ne suka bar gidajensu saboda tunanin yiwuwar kutsen, inda akasari suka tsere a farko fara yakin ko kuma lokacin da ya kai yankinsu

IOM ta kididdige cewa fiye da rabin adadin mutanen da suka rasa matsugunansu mata ne, kana da dama na fuskantar barazana saboda suna dauke da juna biyu, ko makasa ko kuma wadanda aka ci zarafi.

Wadanne abubuwa aka yi ga mutanen da ke tserewa a cikin Ukraine?

Majalisar Dinkin Duniya wacce ke aiki tare da sauran kungiyoyi wajen tallafa wa mutane a Ukraine, ta ce tana samar da agajin jin kai "a duk inda ya kamata". Wannan ya kunshi:

  • bayar da kudade ga mutane don biyan muhimman bukatu kamar abinci da haya
  • kai kayan agaji daga yammaci zuw gabashi, da suka hada da abinci da tamfol ga gidajen da suka lalace saboda lugudan wuta
  • samar da gadajen da ake iya nadewa ga mutanen da ke zaune a wuraren fakewa daga harin bama-bamai
  • kafa cibiyoyin karbar mutanen da suka rasa matsugunansu

Mutane miliyan 12 ne su ma ake tunanin sun makale ko sun kasa ficewa daga yankunan da yakin ya shafa.

Wani dan gudun hijira daga A Ukraine ya isa Poland a ranar 27 ga watan Maris

Asalin hoton, Reuters

Ina 'yan gudun hijirar Ukraine ke tafiya?

'Yan gudun hijrar na kuma tsallakawa zuwa kasashe makwabta da ke yamma, akasari kasar Poland.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa tun a ranar 19 ga watan Aprilu, mutane fiye da miliyan biyar ne suka fice daga kasar Ukraine:

  • Poland ta karbi 'yan gudun hijira 2,825,463
  • Romania 757,047
  • Rasha 549,805
  • Hungary 471,080
  • Moldova 426,964
  • Slovakia 342,813
  • Belarus 23,759

Wasu mutane sun yi tafiya daga kasar Moldova zuwa Romania don haka an hada su cikin jimilar duka kasashen biyu.

Kasashen Poland, da Hungary da Slovakia na cikin yankunan Schengen, inda a can babu tsarin kan iyakoki.

Kana da dama wadanda aka lissafa lokacin da suka ketara cikin wadannan kasashe mai yiwuwa tuni suka fice zuwa saura kasashen.

'Yan gudun hijira nawa ne suka fice daga kasar Ukraine?

Jiragen kasa da ke tunkarar kan iyakar kasar Ukraine sun cika, kana akwai dogayen layuka na ababan hawa a kan hanyoyin fita daga kasar.

, Ukraine

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Majalisar Dinkin Duniya ta kididdige cewa mutane akalla milyan shida da dubu dari biyar ne suka rasa matsugunansu a kasar Ukraine

'Yan gudun hijira ba sa bukatar duka taradunsu, amma zai taimaka idan za su bayar da takardun shaida ko fasfo, da takardun haihuwa na kananan yaran da ke tafiya tare da su, da kuma takardun kiwon lafiya.

Kafin ka samu matsayin 'yan gudun hijira, suna bukatar kasancewa 'yan asalin kasar Ukraine ko mutanen da ke zaune a Ukraine a bisa doka, kamar daliban kasashen waje.

Wane irin taimako ne kasashen ke yi wa 'yan gudun hijira?

A kasashe da ke kan iyaka da kasar Ukraine, 'yan gudun hijira za su iya zama a cibiyoyin karbar baki idan ba za su iya zama tare da abokai da 'yan uwa ba.

Kungiyar Tarayyar Turai ta bai wa 'yan kasar Ukraine da suka tsere wa yaki damar zama su yi aiki a cikin duka kasashe 27 mambobi har na tsawon shekara uku.

Za kuma su samu kulawa da kuma gidajen zama, da kiwon lafiya da makarantu.

Gwamnatin kasar Poland, wacce ta karbi adadi mafi yaw ana 'yan gudun hijira, ta ce za ta bukaci karin kudi fiye da wanda Kungiyar Tarayyar Turai da ke bayarwa don karbar bakuncin mutanen da ke isa can.

Kasar Moldova, ita ma tana neman taimakon kasashen duniya wajen kokari kulawa da 'yan gudun hijra.

Moldova

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Daruruwan 'yan gudun hijira ne ke zaune a wannan cibiyar wasannin a kasar Moldova

Shin me Birtaniya ke yi a taimaka wa 'yan gudun hijirar Ukraine?

Birtaniya ta kaddamar da tsarin yi wa iyalai takardar biza ga 'yan Ukraine da ke da 'yan uwa a Birtaniyar.

Bayan sukar lamirin gwamnatin Birtaniya kan gaggautawa da yanayin daukar matakanta, ta kuma kaddamar da tsarin samar da gidaje ga 'yan kasar Ukraine.

A karkashin wannan tsari, mutane a Birtaniya za si iya zabar daidakun mutane ko iyalai su zauna tare da su a matsayin haya a kyauta har na tsawon watanni shida.

'Yan gudun hijirar da suka zo a kan wannna tsari za su iya zama su yi aiki a Birtaniya har na tsawon shekaru uku, kana sun samu kulawa ta kiwon lafiya da makarantu da kyautata jin dadinsu.

Ana rubuta neman ta shafin yanar gizo kana za a tantance duka masu karbar bakin da 'yan gudun hijirar.

Masu karbar bakin za sus amu fan 350 (£350) a ko wane wata, kana babu wata iyaka kan adadin wadanda za su iya shiga Birtaniya.

Amma kuma, wasu iyalan da suka nemi kasancewa masu daukar dawainiya sun koka cewa tsarin na tafiyar hawainiya kana akwai sarkakiya.

Sakatariyar harkokin cikin gida Priti Patel ta nemi afuwa kan jinkirin da ya haifar da damuwa.

Daga ranar 13 ga watan Aprilu an samar da takardar izinin shiga kasar wato visa kimanin 56,500 a karkashin duka tsare-tsaren biyu, a cikin mutane 94,700 da suka nema