Yakin Ukraine: Me ya sa Ukraine ke son shiga Tarayyar Turai?

Asalin hoton, Getty Images
Ukraine na fatan zama cikakkiyar mamba a kungiyar Tarayyar Turai, nan da watan Yuni mai zuwa.
A ranar Litinin 18 ga watan Afrilu, Shugaba Zelensky ya mika wa wakilin Tarayyar Turai a kasar, Matti Maasikas, cikakkiyar takardar neman amincewar shiga kungiyar, wadda Mista Matti ya ce shi ne matakin farko a hukumance da zai kai Ukraine ga cika burinta.
"Shekaru aru-aru, mutanenmu na daukar kansu a matsayin 'yan Tarayyar Turai", in ji Zelensky.
Sai dai Ukraine na tsaka-mai-wuya, ko dai ta zama aminiya makusanciya ga Tarayyar Turai, ko kuma ta yi bakin-jini sannan ta zama nama a hannun Rasha.
Don haka me ya sa Zelensky ke son ta kasance mamba a Tarayyar Turai?
'Sabuwar' Ukraine
Shugaba Zelensky ya ce: "Kawunan al'ummar Ukraine a hade yake kan wannan batun, muna son jin mu a Turai kuma wani bangare na Tarayyar Turai."
"Ba da damar shiga cikin Tarayyar Turai zai ba mu dama da samun karin damarmakin sake ginawa da zamanantar da Ukraine bayan mun kammala yakin nan.
"Muna sasantawa da tattaunawa da sauran kasashe, domin ganin yadda za a ba mu tallafin kudade, da kwarin gwiwa da kuma taimakawa ayyukan farfado da kasarmu. Tabbas, dole za mu janyo 'yan kasuwa na kasashe daban-daban domin hada hannu a wannan aikin ci gaba."
"Amma muna da burin samar da ayyukan yi da za su kara wa Ukraine martaba."

Asalin hoton, EPA
Kamar yadda majalisar Turai, da bayanan da Tarayyar Turai suka fitar, kashi 40 cikin 100 na 'yan kasuwar Ukraine na da alaka da Turai.
Akwai kuma wasu karin bayanan na alakar kud-da-kud. Tun a shekarar 2017 aka amince 'yan Ukraine su shiga Tarayyar Turai ba tare da sun nemi biza ba.
Tun shekarar 2015, sama da dalibai 'yan Ukraine 11,500 ne suka ci gajiyar shirin musayar dalibai da takwarorinsu na Tarayyar Turai.
Taimakon da Tarayyar Turai ke bai wa Ukraine sun kara sauyawa ta fuskoki da dama, daga taimako na kai tsaye, zuwa zuba jari domin bunkasa tattalin arziki, ba da tallafin kudade, bunkasa fannin wutar lantarki, da taimako a lokacin annobar korona.
Huldar siyasa da kasuwancin maras shinge tsakanin Tarayyar Turai da Ukraine, an kuma sanya wannan cikin yarjejeniyar mu'amalar kasashen, wadda ta sanya an shimfida wasu dokoki da ka'idoji ciki har da fannin makamashi, da ilimi da sufuri.
Haka kuma an bukaci Ukraine ta fara amfani da sauye-sauye ta fuskar habaka dimukuradiyya, da kare hakkin dan adam da doka da oda.
Wannan yarjejeniya dai 'yan a-waren Ukraine masu goyon bayan tsohon shugaban kasar Victor Yanukovich sun yi watsi da ita, lamarin da ya haddasa zanga-zangar kokarin kifar da gwamnatinsa, hakan ta sanya ya tsere Rasha.
Tsakanin Rasha da kasashen yamma
Shekaru da dama an gano tashin hankali da dangantaka tsakanin Ukraine da Rasha, da alakar Rasha ta kasashen yamma.

Asalin hoton, Reuters
Ukraine ta samu 'yanci ne bayan rushewar Tarayyar Sobiyet a shekarar 1991.
Kungiyar Tarayyar Turai ta samo asali ne bayan cimma yarjejeniyar Roma a shekarar 1957, a lokacin da ake kiran kungiyar cinikayya ta Tarayyar Turai, mai mambobi shida. Zuwa shekarar 1993 ta kara fadawa da kasashe goma sha biyu.
Kasashen Austria, Finland da Sweden sun shige ta a shekarar 1995, yayin da kungiyar ta samu mambobi masu yawa a shekarar 2004, lokacin da kasashen Baltic da wasu na Turai suka shige ta.
Fadada ta karshe da kungiyar ta yi shi ne a shekarar 2007, lokacin Bugaria da Romenia suka shiga ciki, sai kuma na shekarar 2013 da Croatia ita ma ta shiga tsundum a cikin kungiyar.
A shekarar 2004 Ukraine ta dauki hanyar shiga kungiyar, lokacin da akai ta zanga-zangar nan mai lakabin "Juyin-juya halin Lemo" ko Range revolution a turance, wadda ta tilasta sauya gwamnatin da akai zargin rashawa ta dabaibaye ta. Sabuwar gwamnatin ta fi kusanci da Turai, idan aka kwatanta da wadda ta gabace ta.
Shugaba Viktor Yushchenko, da ya yi nasara a zaben 2004, yace; "Ukraine kasar dimukradiyyar turai ce."
Amma ya sha kaye lokacin da ya tsaya takara a karo na biyu a shekarar 2010, inda Yonukovich da yake kokarin kusanta kasar da Rasha ya yi nasara.
Watsi da yarjejeniyar alakar kud-da-kud da Turai da Yanukovich ya yi, ta janyo gagarumar zanga-zanga, inda aka mamaye dandali Maidan da ke birnin Kyiv, masu boren suka yi zaman dabaro a wajen da aka sanyawa su na cibiyar boren Euromaidan.
Bayan hambarar da gwamnatin Yanukovich, ya tsere zuwa Moscow, inda Rasha ta mayar da martani ta hanyar kwace yankin Crimea na Ukraine da marawa 'yan a-waren yankin baya.
Wannan ya sanya aka samar da yankuna biyu da suka balle da 'yanta kansu wato Donetsk da Luhansk.
Mamayar Rasha

Asalin hoton, Reuters
Zelensky ya ce mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu, ya nuna karara kokarin kasar na shiga Turai na kara girmama.
Ya ce samun damar Ukraine na shiga Turai ya kara kusantowa, da kuma salon da ake bi na inganta 'yan kasar idan sun kai gaci.
Shugabannin Turai sun yi shelar marawa Ukraine baya da burinta. Sai dai ba su yi abin azo a gani ba na ganin sun janyo ta cikinsu, abin da masana ke cewa ya kamata ayi gaggawar yin haka saboda yadda ake daukar lokaci kafin a kammala yarjejeniyar shiga kungiyar.
Karin kasashe kamar, Albania, Macedonia ta Arewa, Montenegro, Serbia da Turkiyya da ke neman shiga kungiyar shi ma wani batu ne na daban.
Tuni kasashen Ukraine, Georgia da Moldova, suka mika takardar son shiga kungiyar da amfani da mamayar Rasha domin cimma manufa.
Zelensky ya amince cewa kowacce kasa da ta shiga kungiyar Tarayyar Turai, sai da ta sha wuya, da bin ka'idar cike takarda da makanata, amma sun dade ba su kai matakin da Ukraine ke kai a yanzu ba.
"Sama da mako guda kena da muka kammala cikewa. Za mu samar da bangare na biyu na bukatar nan ba da jimawa ba. Mu na kuma fatan Turai za ta dauki matakin gaggawa domin sanin makomarmu''.
Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Ukraine Andriy Yermak, ya ce jami'an gwamnati na fatan za su samu damar shiga tattaunawar hukumar tsaron Tarayyar Turai a watan Yuni mau zuwa, domin sake tattaunawa, "hakan zai faru cikin wani yanayi ba a saba ganin irin shi ba".










