Yaƙin Ukraine: Me ake nufi da kasa 'yar ba-ruwanmu da Ukraine ke son zama?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Pablo Uchoa
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce Ukraine na iya amince ta kasance kasa 'yar baruwanmu a wani bangare na tattauna kan kawo ƙarshen yankinsu da Rasha.
Amma kuma hakikanin me yake nufi da kasa 'yar baruwanmu?
'Yadda aka fasarar kalmar'
Kasa 'yar baruwanmu ba ta daukar ɓangaranci tsakanin ƙasashe biyu ko sama da hakan a yaƙi. Ba sa bada taimako ko barazana ga ƙasashen da ke cikin fusata - waɗanda suke wannan yaƙi - ko amincewa a yi amfani da yankinsu a wasu ayyukan soji.
Kasashe da dama na amfani da wannan tsari har a kundin tsarin mulkinsu, musamman ƙasashe irinsu Turai da Tsakiyar Asiya.
Wasu kuma sun sanar da kansu a matsayin 'yan kallo, ma'ana babu wani ɓangare da suke nunawa goyon-baya idan ana rikici.
"Akwai tarihi mai tsayi kan batun kasancewa 'yar baruwanmu, amma a ƙarshe, kalmar ko abin da ƙasashe da dama ke fakewa kenan a kai," a cewar Owen Greene, farfesa kan tsaron ƙasashe da ci gaba a Jami'ar Bradford da ke Birtaniya.


Switzerland kasa 'yar ba-ruwanmu

Asalin hoton, Getty Images
Switzerland ta kasance kasa mafi daɗewa kuma misali mafi girma ga kasancewa 'yar baruwamu. Wannan ya kasance tsarin Swiss kan harokin ƙetare tun 1815.
Switzerland ta kasance tana da wannan aƙida tun kafin yaƙin duniya na biyu, kuma akwai lokacin da aka zargeta da kasancewa tuddun tsira ga 'yan Nazi da suka aikata laifuka.
Ƙasar ba ta taɓa shiga ƙungiyar Tarayyar Turai ba, duk da cewa ta sanya hannu a yarjejeniya da Turai kan 'yan cin kasuwanci da zirga-zirga.
Ba ta taɓa zama mamba a ƙungiyar tsaro ta kawancen ƙasashen yamma ba, Nato, kuma ba ta shiga Majalisar Dinkun Duniya ba sai a shekara ta 2002.
Amma Farfesa Greene ya ce salon Swiss na 'yar baruwanmu na kasancewa yanayi mai wahala na ci gaba da kasancewa a hakan a duniyar wannan zamani.
Tunda harkokin EU na ketare ya kunshi batun tsaro da karfin soji, Rasha na yiwa Switzerland kallon abokiyar ƙasashen yamma saboda shaƙuwar alaƙarsu.
Farfesa Greene ya ce, Switzerland sannu a hankali na barin hanya na ɗaɗɗadun aƙidunta kan 'yar baruwanmu.
Kuma misali na baya-bayanan a kan wannan shi ne, bayan mamayar Rasha a Ukraine, Gwamnatin Swiss ta bi sahun sauran ƙasashen Turai wajen kakabawa Rasha da kamfanoninta takunkumai har da daidaikun 'yan kasar.

Sassauta tashin hankali
Amma Switzerland ba ita kaɗai bace ƙasar Turai da ke da ra'ayin kasancewa 'yar baruwanmu ba a harkokin ƙetare. Wasu ƙasashen sun yi haka a baya a kokarin sassauta tashin hankula a yankunansu.
Bayan yaƙin duniya na biyu, Austria ta fuskanci mamaya daga Tarayyar Soviet da Amurka da Burtaniya da Faransa. Kasancewarta 'yar baruwanmu na cikin sharudan da Tarayyar Soviets suka bijiro da shi domin tabbatar da an samu daidaito tsakanin USSR da sauran ƙasashen yamma.
Kasar ta amince da wannan tsari da kuma sanya shi a kundin tsarin mulkinta na 1955 a wani ɓangare na yarjejeniyar tarihin samun 'yancinta bayan samun haɗin-kai daga Jamus kafin yaƙin duniya na biyu da mamaya daga dakarun kawance bayan yakin.

Asalin hoton, Getty Images
Farfesa Greene ya ce kasancewar Austria 'yar baruwanmu "ya samo asali ne sakamakon wasu rikici" kuma nata bai yi tsanani irin na Switzerland ba.
Duk da cewa Austria ta shiga Nato kuma ba za ta amince da dakarun ketare su kafa sansani a yankinta ba, a matsayinta na Mamba a EU ta goyi-bayan takunkumin da aka kakabawa Rasha kan mamaya a Ukraine.
"Duk da cewa Austria kasa ce 'yar baruwanmu daga ɓangaren soji, ba wai muna kasancewa 'yan baruwanmu ba ne a fanin rikici," a cewar Ministan Harkokin wajen Austria, Alexander Schallenberg.
Kasashen Turai shida ba sa cikin Nato: Finland da Sweden da Ireland da Malta da Cyprus da Austria.
Amma dukkanisu banda Cyprus, na bai wa Nato haɗin-kai ta shirinsu na kawance kan tsaro, wadda ke basu damar alaƙa da kawayensu na yammaci.

Shinge
Pacal Lottaz, mai bincike a Switzerland kan darrusan 'yan baruwanmu a kwalajen Waseda ta Tokyo, ya ce ƙasashen da ke bin wannan tsari ba su fiye cimma manufofinsu ba.
Tsohuwar yankin jamhuriya a tarayyar Soviet ta Moldova ta sanya dokikin bin tsarin 'yar baruwanmu a kudin tsarinta a 1994.
A Turkmenistan, kasar da ta kasance wata tsohuwar mamba a jamhuriyar Soviet, an ware ranar da ake bikin 'yar baruwanmu a kowacce 12 ga watan Disamba, a bikin zagayowar 'yar baruwanmu ta hakika da ta cimma a 1995.

Asalin hoton, Getty Images
Mongolia, da ake yawan samunta da laifukan rikicin diflomasiya tsakanin China da Tarayyar Soviet lokacin yakin cacar-baka, ta ayyana kanta a matsayin 'yar baruwanmu a taron Majalisar Dinkin Duniya a zaurenta a 2015.
Tsakhia Elbegdorj, tsohon shugaban Mongolia a wannan lokaci, ya ce "tarihin Mongolia, da yankunan da muka fito da tsarinmu da ya bambanta na cigaba sun sha gaban kowa a fanin nuna 'yar baruwanmu."
Ya tunatar da sauran kasashe, cewa kasashen da ke kasancewa cikakun 'yan baruwanmu na da karfin ikon kare kansu.

Karfin soji
Farfesa Greene ya ce rashin fahimta ne a yi tunanin kasashe 'yan baruwanmu ba su cika nuna damuwa kan batun tsaronsu ba.
"Zancen gaskiya, akasarin waɗannan kasashe sun fi zuba kudade a fanin tsaro da karfin soji sama da wadanda komai da ruwansu domin dole su yi dogaro da kansu a fanin tsaronsu," a cewarsa.
Ana yiwa dakarun Swiss kallon mafiya kwarewa a Turai. Dukkanin mazan kasar masu lafiya na ayyukan soji kuma duk ana basu bindiga na kansu da suke ajiyewa a gida.
"Zaɓin kasancewa 'yar baruwanmu a wannan zamanin na nufin bamu yarda cewa yaƙi na iya barkewa ba. Amma suna cewa da gangan muke yin wannan zabi, a cewar Farfesa Greene.
Don haka akwai bambanci tsakanin kasa 'yar baruwanmu da rashin tanadin soja.

Asalin hoton, Getty Images
Costa Rica ta rusa sojojinta a 1949 amma sai ta ci gaba da aiki da 'yansandanta da ke da karfi sosai kamar jami'an ƙasashe makwabta, a cewar Farfesa Greene.
Ya ce ƙasar da ke tsakiyar Amurka na ganin kanta a matsayin wadda ke duba bukatun kowanne ɓangare da manufar siyasa ta hanyar rusa sojointa a yankunan da ake fuskantar juyin-mulki a baya.
Duk da cewa kundin tsarin mulkinta ya haramta mata shiga harkokin yaƙin ketare, Farfesa Greene ya ce: "Duk wanda ya yi kokarin yi musu mamaya, za su ba da mamaki."
Kudin tsarin Japan ya haramta mata ita ma shiga harkokin yaƙi, sai dai akwai alaƙa mai karfi na soji da tsaro tsakaninta da Amurka.
Kuma ita ma 'yar karamar kasar nan Lichtenstein, na samun taimako ne tsakanin Austria da Switzerland, kuma ta dogara kan tsaro daga Switzerland, bayan rusa sojinta a karni na 19.

Daidaituwa
A karshe dai, akwai wani irin salon 'yar baruwamu na siyasa da wasu kasashe ke nema domin cimma burikansu na alaƙa tsakanin kasa da kasa wanda bai kunshi wasu abubuwa na shari'a da dokoki ba.
Singapore da musamman Taiwan misalai ne na gwanatocin da suka gaggara daidaita kansu tsakanin abokan hamayya irinsu Amurka da China da Japan a Asia.
Singapore tayi kokarin mutunta tsarin na tsawon loakci na 'yar baruwanu da Amurka da China. Sai dai barazanar da China ke yi wa Taiwan na haifar da wasu matsaloli da tsare-tsare masu sarkakiya wajen cimma wasu batutuwan.

Asalin hoton, Getty Images
Kusan ƙasashe 120 ke yiwa kansu kallon 'yan baruwanmu kan kasancewa tare da akasin haka da duk wata kungiya mai karfi.
Amma wannan wani tsari ne na siyasa, wanda tsohon shugaban Yugoslavia ya runguma a matsayin mamba a gidauniyar kasahen 'yan baruwanmu da aka kafa a 1961.
Serbia, wanda a baya ake kiranta Jamhuriyar Yugoslavia, ta kaddamar da yanke kanta daga kasashe 'yan baruwanmu a 2007 inda a yanzu take kokarin daidaita yada za ta shiga Tarayyar Turai.
Bayan kisan kare dangi na 1994 a kasar, Rwanda ta sanar da kasancewa a jeren irin wadannan kasashe 'yan baruwanmu a 2009 bayan shiga kungiyar kasashen Commonwealth.

Ya Ukraine za ta kasance a matsayin 'yar ba-ruwanmu?
Wannan zai danganta ne kan yarjejniyar da aka cimma tsakanin jami'an diflomasiyar Ukraine da Rasha.
Lottaz da na yaƙinin cewa Ukraine ta kasance 'yar baruwanmu wasu sharuda ne da ba a iya tattaunawa ba a kan su ga Rasha. "Wannan ya kunshi rubuta wannan a kudin tsarin mulkin Ukraine da sanya hannu kan yarjejeniya tsakaninta da Rasha," a cewarsa.
Amma Farfesa Greene na cewa kalmar kasancewa 'yar baruwanmu na tattare da sharuda masu sarkakiya da nake ganin Ukraine za ta nuna rashin wayewa idan ta amince ta kasance 'yar baruwanmu kan komai."
"Wannan na nufin Rasha za ta fayyace komai kan batutuwan da ba lallai Ukraine ta aminta ba ko ya yiwa kowanne ɗan kasar dadi," a cewar Farfesa Greene.

Asalin hoton, Getty Images
A fayyace, kasancewa 'yar baruwanmu a wannan yanayi na nufin Ukraine ta alkawarta ba za ta shiga kungiyar tsaro ta Nato ba ko bai wa dakarun Nato ko Rasha damar shiga yankinta.
Sai dai makomarta na kasancewa mamba a Tarayyar Turai na iya zama wani batu na daban nan gaba.
Wasu ƙwararru na shawartar cewa Ukraine na iya rungumar salon tsarin Austria na 'yar baruwanmu da kuma zama mamba a Tarayyar Turai amma babu ruwanta da Nato.
Amma tunda zama mamba a EU na nufin wannan zai kasance da tabbacin tsaro, Farfesa Greene na da yaƙinin cewa "Rasha na iya ganin wannan a matsayin wani abu da ya sabawa yarjejeniyarta".
Lottaz, a wani ɓangaren, na da yaƙinin cewa ƙasashen biyu na iya ficewa daga Tarayyar Turai a wani mataki a yanzu domin lalubo hanyar zaman lafiya.
A farkon yaƙin, Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce yana son kwance karfin sojan Ukraine, amma bai tantace abin da yake nufi da wadannan kalamai ba kai-tsaye.
Farfesa Green ya ce batun "kwance karfin sojan Ukraine ba zai ɗaure ba."
Amma Lottaz na da yaƙinin Rasha ba wai tana nufin Ukraine ta tarwatsa karfin sojinta ba.
Ya ce Rasha da Ukraine na iya amincewa da rage yawan sojin Ukraine, haramta amfani da manya da makaman nukilliya, da wasu shiga kowacce yarjejeniya da Nato.
"Wannan shi ne batu mafi muhimmanci kan kwance karfin soja ta fanin babu amfani da manyan makai," a cewar Lottaz. Amma yana jaddada cewa duk wadannan batutuwa sun ta'alaka ne kan yarjejeniya."











