Ƴanbindiga sun buɗe sabuwar daba a jihar Zamfara

Asalin hoton, OTHER
Al'ummar Kuryar Madaro da ke karamar hukumar Kauran Namoda na korafi game da wani sabon sansani da suka ce ƴanbindiga sun kafa kuma su ke ci gaba da taruwa, ƙarƙashin shugabansu mai suna ɗan Sa'adi.
A cewarsu, wannan ɗan bindigar duk da ayukkan samar da tsaro da jami'an tsaro ke ci gaba da yi amma bai sassauta da hare-harensa ba.
"Yanzu haka wasu baƙin ƴanbindiga banda wanda muke da su, suna kafa sabbin sansanoni, wani Ɗan Sa'adi ne yake jagorantarsu, kusan ya mamaye ko ina saboda yadda yake daukar mutane, yana karɓar maƙudan kuɗaɗe."
Baya ga wannan ma Dan Sa'adi na ci gaba da tattaro ƴan uwansa mahara, musamman wadanda aka tarwatsa yana sake hada kansu, domin ci gaba da kaddamar da hari.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa har yanzu hankalinsu ba a kwance ya ke ba muddin wadannan mahara suka ci gaba da taruwa a kusa da su.
"Mutanen nan sun matsa mana iya matsi, suna kafa sabbin sansanoni, duk wanda ke yankin nan babu wanda bai san shi ba, kuma jami'an tsaronmu na iya bakin ƙoƙarinsu."
BBC ta tuntubi kakakin rundunar Fansar Yamma, Laftanar-Kanal Abubakar Abdullahi ta waya domin jin ko sun san da wannan sabon sansani, sai dai ba mu same shi ba, duk na tura masa sakon kar-ta-kwana game da lamarin.
A kwanan nan dai rahotanni daga jihar ta Zamfara na cewa ana ci gaba da samun gagarumar nasara wajen yaƙi da 'yan bindiga, sai ga shi yanzu wasu al'umma na bayyana cewa sabbin mahara na sake dawowa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kazalika, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya sha nanata cewa ba zai yi sulhu da ƴan fashin daji ba.
A wata zantawarsa da BBC Hausa gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matsaya ne ganin cewa a bayan an sha yin sulhu da 'yan bindigar, amma ba su mutunta alƙawurran da aka yi da su.
Sai dai a wata tattauna ta baya-bayan nan da BBC ta yi da gwamna Dauda ya ce zai iya yin sulhu da ƴanbindiga da ke addabar jihar ne kawai idan har sun ajiye makamansu.
Hakan na zuwa ne yayin da wani sulhu da gwamnatin jihar Kaduna - wadda ke fama da matsalar tsaro iri ɗaya da ta Zamfara - ta yi da irin waɗannan ƴan fashi, lamarin da ake ganin ya kawo zaman lafiya a sassan jihar da suka daɗe suna fama da tashin hankali.
Batun yin sulhu da ƴanbindiga lamari ne da ke haifar da zazzafar muhawara a Najeriya, bayan shafe sama da shekara 10 ana fama da ayyukan ƴan fashin daji a arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa dubban rayuka da tarwatsa al'umma da durƙusar da ilimi da kasuwanci.











