Takarar 2027 : 'Bai kamata a yi wa Atiku riga-mallam-masallaci ba'

Atiku Abubkar

Asalin hoton, OTHERS

Lokacin karatu: Minti 3

Bayan ɓullar wani bidiyo a kafafen sada zumunta da ke nuna nan gaba kaɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar zai bayyana aniyyarsa ta tsayawa takara a zaɓen 2027 a hukumance, masu magana da yawunsa sun ce tsohon bidiyo ne tun na shekarar 2022 da ake amfani da shi wajen kawo rarrabuwar kai a tsakanin al'umma.

Mataimaki na musamman kan kafafen yada labarai ga Atikun, Abdurrashid Shehu Uba, ya ce, wannan ba sabon abu ba ne, kutingwila ce irin ta siyasa kawai.

''Ba wani sabon abu ba ne, amma abin da muke so al'umma su fahimta shi ne bai kamata a yi mana riga-mallam-masallaci ba. Abu ne wanda komai ake binsa daki-daki,'' in ji Uba.

''Ina mai tabbatar ma wannan bidiyon an amfani da shi ne a matsayin cimma wani buri na kai amma mu ba mu san da shi ba.'' In ji shi.

Ya kara da cewa, kowa ya ga yadda Atikun ya jagoranci tabbatar da jam'iyyar hadaka ta ADC a wannan kasa.

''Kowa ya ga musamman al'ummar Arewa suna cikin halin rashin tsaro da tabarbarewa da kuma tsadar rayuwa da al'umma ke fuskanta, wadannan su ne abubuwan da a yanzu ya kamata mu kalla,'' ya ce.

Ya kara da cewa, '' shi wannan bidiyo kwarai da gaske muna zargin wasu kafafen yada labarai suna amfani da shi ne domin kawo rarrabuwar kai musamman a lokacin da ake kokarin ganin wannan hadaka ta kara karfi.''

Kakakin na Atiku ya ce, yanzu ba batu ake na takara ba batu ake na ganin wannan sabuwar jam'iyyar hadaka ta mayar da hankali wajen tabbatar da shugabanci wanda za a samu matasa.

''Atiku bai bayyana takararsa a yanzu ba zuwa wani lokaci in Allah Ya yarda, komai lokaci ne in lokaci ya yi ai al'ummar Najeriya za su ji kai tsaye daga wurinsa,'' ya ce.

Dangane da ko Atikun na ganin kansa a matsayin wanda zai yi wa jam'iyyar hadakar ta ADC takara a 2027.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai kakakin tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya ce, ''babu batun dantakara a jam'iyyar hadaka a yanzu.

''Jam'iyyar hadaka ta bayyana kuma ta kara bayyanawa ta bakin kakakinta Mallam Bolaji Abdullahi, magana ake ta tabbatar da wannan jam'iyya ta shiga lungu da sakon dukkanin wannan kasa a yanzu. Ko da za a zo maganar shugaban kasa batu ne da za a yi bisa tsari na dimukuradiyya,'' ya ce.

Abdurrashid ya kara jaddada cewa a yanzu ba su fara maganar takarar Atiku ba tukuna.

''Ina mai tabbatar maka a yanzu babu batun za mu yi maganar takara batu muke na inganta jam'iyyar ADC ta hadaka daga kowa ne bangare na Najeriya domin tunkarar babbar nasarar da muke sa ran al'ummar Najeriya za su sahale wa wannan jam'iyya ta ADC,'' in ji shi.

''Amma a yanzu Atiku Abubakar bai ce komai ba kuma bai nuna wani yatsa ko na ganin cewa zai danne hakki ko kuma zai tsauye hakkin na wani da ke sha'awar neman kujerar shugaban kasa a jam'iyyar ADC ba.'' Ya ce.

Ya kara da cewa, ''yarjejeniya ce wadda sun riga sun bayyana wa kansu cewa duk wani dantakara da da ya samu nasara a jam'iyyar ADC za a bi shi.''