Ko Atiku zai sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a 2027?

Atiku Abubakar

Asalin hoton, Atiku Abubakar/X

Lokacin karatu: Minti 4

Ziyarce-ziyrace da ganawar da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ke yi na ƙara sanya wa ƴan ƙasar shakku kan haƙiƙanin manufarsa inda suke tambayar ko jagoran hamayyar zai sake yin takara a jam'iyyar PDP ko kuma a'a.

Atiku Abubakar dai ya yi takarar neman shugabancin ƙasar a ƙarƙashin babbar jam'iyyar hamayya ta PDP har karo biyu wato 2019 da 2023.

Kafin nan ya kuma yi takarar a ƙarƙashin jam'iyyarAC a 2007 lokacin da ya ƙalubalanci marigayi tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa Ƴar'adua na PDP.

Atiku mai shekara 78, zai zama ɗn takarar shugaban ƙasa na farko mai shekara 80 idan har jam'iyyar PDP ta amince da sake tsayawarsa a kakar zaɓe ta 2027.

BBC ta yi nazari kan ko Atikun zai sake tsayawa takara ko kuma a'a.

Biri ya yi kama da mutum - Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Abdulƙadir, malami a jami'ar jihar Kaduna ya ce alamu na nuna Atiku ka iya sake takara.

"Za a iya cewa biri ya yi kama da mutum idan ka dubi irin rawar da yake takawa musamman ta fuskar hamayya da kuma irin yadda yake ta kai komo wurin sasanta wa da mutanen da ya ɓata da su, za ka iya cewa daga dukkan alamu Atiku na shirin tunkarar takarar shugaban ƙasa a 2027."

Sannan kuma idan ka duba, Atiku ku san shi ne mutumnin da idan jam'iyyun hamayya na son yin haɗaka za su saka a gaba wajen tunkarar jam'iyya mai mulki ta APC a zaɓen na 2027, duk da cewa dai yanzu ba shi da kwarjini a idanun ƴan siyasa kamar irin wanda yake da shi a baya." In ji farfesa Tukur Abdulƙadir.

Shi ma Malam Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen jami'a ta Kano, CAS ya ce yana kyautata zaton Atiku zai yi takara.

"Lallai abubuwan da Atiku Abubakar ke yi yanzu na nuni ne da yunƙurin haɗa kan abokan hamayya a shirye-shiryensa na sake takarar a 2027. Yana son ya nuna cewa babu gajiyawa daga ɓangarensa kamar yadda wasu ke hasashe. Yana dai nuna cewa har yanzu yana nan kuma duk abin da za a yi nan gaba to da shi za a yi."

Manyan ƙalubalen da Atiku zai fuskanta

Farfesa Tukur Abdulƙadir ya ce duk da cewa alamu na nuna Atiku Abubakar ka iya sake tsayawa takarar neman shugabancin Najeriya a 2027, ya lissafa wasu ƙalubale da ya ce zai iya fuskanta idan har zai yi takara.

  • Raɗe-raɗin shirinsa da Umaru Fintiri: Zai wuya Atiku ya samu irin damar da ya samu a baya a wurin ƴan siyasa da mabiya. Misali yanzu haka akwai raɗe-raɗin cewa ba sa tafiya tare da gwamnan jihar Adamawa mai ci Umaru Fintiri, wadda jihar Atiku ce.
  • Takarar Bala Muhammad: Zai fuskanci turjiya daga ƴan jam'iyyar da ke da burin tsayawa takara. Misali gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad na son kujerar. Ka ga kenan za a iya samun karo. Za su ga lokaci ya yi da zai bar na ƙasa su yi takara ko a samu a kai ga nasara.
  • Rikicin jam'iyyar PDP: A yanzu haka jam'iyyar PDP na fama da rikicin cikin gida wanda ka iya kai jam'iyyar ƙasa. Zarge-zargen da ake yi cewa jam'iyya mai mulki na amfani da tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike wajen rura wutar rikicin PDP. Sannan kuma Wike yana da tabon cewa Atiku bai masa daidai ba a zaɓen 2023.

'Ya yi wuri a yi batun 2027'

Abdulrasheed Shehu Sharaɗa mai taimaka wa Atiku Abubakar kan harkokin yaɗa labarai ya ce ya yi wuri a fara maganar takara a 2027.

"Ai yanzu gwamnatin Tinubu take shekara biyu saboda haka ba lokaci ba ne na batun wane ne zai zama shugaban ƙasa a 2027. Lokaci ne na sanya ido domin ganin jam'iyya mai mulki ta yi wa talakawa aiki. Idan ba ta yi ba, mai girma Atiku Abubakar ba zai fasa yi musu gyara domin hakan ne demokraɗiyya." In ji Abdulrasheed.

Dangane kuma da tambayar da aka yi masa cewa ba ya ganin lokaci ya yi da uban gidan nasa zai bar wa matasa masu jini a jika su nemi takarar? Sai ya ce:

"Atiku Abubakar bai taɓa hana wani mutumin da ke son yin takara ba tunda dai shi ɗan dimokradiyya ne na asali. Kuma yanzu ba zai hana kowa fitowa takara ba.

Batun kuma shekaru, ai kuna ganin dai irin abubuwan da yake yi. Da gani kun san mutum ne mai jin karfi mai jini a jika." In ji Abdurrasheed Shehu Sharaɗa.

Wane ne Atiku Abubakar a siyasance?

Atiku Abubakar

Asalin hoton, AFP

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Atiku Abubakar ya tsunduma harkokin sisaya a 1989, kuma yana cikin makusantan tsohon mataimakin shugaban kasa na mulkin soji, Janar Shehu Musa Yar'adua.

Ya shiga jam'iyyu daban-daban tun da ya shiga harkokin siyasa.

An zabi Atiku Abubakar a matsayin gwamnan Jihar Adamawa a 1998, ko da yake daga bisani Cif Obasanjo ya zabe shi domin kasancewa mataimakinsa.

Ya zuwa 2023, karo uku Atiku Abubakar ke tsayawa takarar shugaban kasa, ko da yake ya tsaya zaben fitar da gwani sau uku.

A shekarar 2007, jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) ta tsayar da shi takara inda ya sha kaye a hannun dan takarar PDP, Umaru Musa Yar'adua.

Kazalika a shekarar 2019 ya fafata da Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC amma bai yi nasara ba.

Sai kuma a 2023 da PDP ta sake tsayar da shi takara domin fafatawa a zaben da ya bai wa Bola Tinubu nasara.

Idan har Atiku Abubakar zai sake tsayawa takarar a 2027, zai zama karo na huɗu kenan da zai tsaya a babban zaɓe sannan kuma karo na bakwai a zaɓen cikin gida na jam'iyya.