Me taƙaddama kan takarar shugabancin Najeriya a 2027 ke nufi?

Asalin hoton, Social media
Har yanzu kalaman sakataren gwamnatin Najeriya kan takarar shugaban ƙasar a 2027 na ci gaba da janyo martani da muhawara daga ƴansiyasa da masu sharhi.
A farkon makon nan ne Gorge Akume cikin wata hira da gidan talbijin na TVC ya ce duk wanda ke neman shugabancin Najeriya daga yankin arewacin ƙasar a 2027 ya jira zuwa 2031.
A cewar sakataren gwamnatin, daga yankin kudancin Najeriya ya kamata a fitar da shugaban ƙasa a 2027.
"Shugaba Tinubu ɗan kudanci ne, kuma a bar shi ya kammala wa'adinsa na biyu. Ya kamata a bar ƴan kudu su yi mulki na shekara takwas, daga nan sai a koma arewa. In ba haka ba to za a lalata ƙasar nan'', kamar yadda ya bayyana cikin hirar.
Sai dai waɗannan kalamai na Akume sun janyo zazzafan martani daga 'yansiyasar arewacin ƙasar, waɗanda da alama furucin bai yi musu daɗi ba.
Paul Ibe, mataimaki na musamman ga jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar, ya ƙalubalanci Akume da cewa ina batun bai wa kowa dama?
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, hadimin Atikun ya ce zuwa 2027 yankin kudancin Najeriyar ya zarta arewacin ƙasar adadin shekaru a shugabancin ƙasar.
Paul Ibe ya ce zuwa 2027 yankin kudancin Najeriya na da shekara 17 da 'yan yankin ke mulkar ƙasar tun bayan komawarta kan tafarkin dimokuraɗiyya, yayin da zuwa lokacin yankin arewaci ke da shekara 11 tun 1999.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Cikin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels, Paul Ibe ya ce Atiku Abubakar na ƙoƙarin haɗa kan jam'iyyun hamayya wajen ganin sun kawar da gwamnatin APC a 2027.
''Saboda yana ganin haɗin kan jam'iyyun hammaya ne kawai hanya mafi sauƙi na kawar da wannan gwamnati da ta gaza'', in ji Paul Ibe.
A nata ɓangare, jam'iyyar APC mai mulki ta ce haɗewar jam'iyyun adawar ba zai yi wani tasiri ba a zaɓen 2027 mai zuwa.
Sakataren Yaɗa labaran jam'iyyar Bala Ibrahim ya ce haɗewar manyan 'yan hamayyar ciki har da Atiku Abubakar da Peter Obi ba zai hana Tinubu zarcewa ba, kamar yadda ya bayyana wa jaridar Punch.
Wannan dambarwar ta musayar kalamai tsakanin jam'iyyun siyasar Najeriya kan takara tun lokacin zaɓe bai zo ba abu ne da koyaushe ake yinsa a Najeriya, kamar yadda masana siyasa a ƙasar suka bayyana.
Farfesa Abubakar Kari masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Abuja ya ce 'yansiyasar Najeriya a wannan jamhuriya ta huɗu sun yi shuhura da irin wannan ɗabi'a.
'An buga gangar siyasar 2027'
Farfesa Kari ya ce irin wannan ta sha faruwa a siyasar Najeriya.
"Na tuna a 2002 lokacin da shugaban jam'iyyar PDP na wancan lokaci, Anthony Anenih, ya fito ya ce 'kada ma kowa ya yi tunanin cewa zai yi takara da Olusegun Obasanjo'," in ji farfesan.
''Haka ma an faɗa a lokacin Jonathan da Buhari cewa za su zarce, kada wanda ya yi tunanin tsayawa."
Shi ma Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami'ar Bayero ta Kano ya ce a tsarin siyasar Najeriya kowace rana ma lokacin yaƙin neman zaɓe ne.
"Saboda siyasar Najeriya ta biyan buƙatar ƙashin kai ce, shi ya sa za ka ga kusan kullum kamar gobe ne za a yi zaɓe, ana ta ka-ce-na-ce, ba a mayar da hankali wajen yi wa talakawa aiki'', in ji shi.
Farfesa Kari ya ƙara da cewa a siyasar Najeriya tun kafin lokacin zaɓe ya yi 'yansiyasa da jam'iyyu da masu mulki da muƙarrabansu suke shirye-shiryen zaɓe.
"A taƙaice dai a iya cewa an buga gangar siyasar 2027", a cewar Farfesa Kari.
Shi ma a nasa ɓangaren, Farfesa Fagge ya ce a aikace za a iya cewa an buga taken 2027.
''Ko ma dai a hukumance ba a buga ba, to a aikace an buga saboda ayyuka da kalaman 'yansiyasar sun nuna haka'', in ji shi.
'Ta haka ne wasu ke bayyana aniyarsu'
Farfesa Kamilu Fagge ya ce a wasu ƙasashen ba haka tsarin siyasa yake ba, amma a Najeriya lamarin ya sha bamban.
''A wasu ƙasashen idan an rantsar da gwamnati, takan mayar da hankali ta yi wa mutane aiki, ta tsahirta daga harkokin siyasa. Amma a Najeriya kowane lokaci ma na yaƙin neman zaɓe ne'', in ji Farfesa Fagge.
Shi kuwa Farfesa Kari cewa ya yi dama haka tsarin siyasar Najeriya yake, domin tun ranar da wani ya hau wata kujera to daga ranar ne wani kuma zai fara hango wannan kujera.
Kari ya ce wasu 'yansiyasar ma ta wannan hanya suke bayyana wa al'umma aniyarsu ta tsayawa takara a zaɓen da ke tafe.
Amma a cewar Farfesa Fagge, bai kamata 'yansiyasar Najeriya su fara batun takarar 2027 ba a wannan lokaci, domin "zai janye hankalin gwamnati tare da rura wutar siyasa tsakanin 'yansiyasar".
Hakan zai iya ɗauke wa APC hankali?
Farfesa Kamilu Fagge na ganin hakan ka iya ɗauke wa jam'iyyar APC mai mulki hankali daga gudanar da harkokin da suka shafi gwamnati.
''Gaskiya hakan ba shi da alfanu, domin in dai kishin ƙasar ake yi to za ka ga da zarar an gama zaɓe, kowa zai mayar da hankali wajen aiwatar da alƙawuran da ya yi wa 'yan ƙasa."
Sai dai Farfesa Abubakar Kari ba haka yake kallon lamarin ba.
''Ba na tsammanin hakan zai zamo wata barazana ga gudanar da gwamnati, don kawai mukarraban shugaban ƙasar sun fara maganar zarcewarsa a 2027'', in Farfesa Kari," a cewarsa.
''Hakan zai zama damuwa ne kawai idan shi kansa shugaban ƙasar ya mayar da hankali kacokam kan zaɓen na 2027 maimakon harkokin gwamnatinsa."











