Me ya kai Atiku wurin Obasanjo?

Atiku ya gana da Obasanjo

Asalin hoton, Abdurrasheeth/FB

Lokacin karatu: Minti 3

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya kai wa tsohon ubangidansa kuma shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ziyara a gidan da ke Otta a jihar Ogun.

Mai taimaka wa Atiku Abubakar a harkokin ƴan jarida, Abdurrashid Shehu Uba ne ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook cewar Atiku ya sami rakiyar fitattun ƴansiyasa da suka haɗa da tsohon gwamnan jihar Cross River, Sanata Liyel Imoke da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da kuma sanata Abdul Ningi, ɗan majalisar dattawa daga jihar Bauchi.

Alaƙar Atiku da Obasanjo

Sheikh Gumi da Rabaran Hassan Kuka sun sulhunta Atiku da Obasanjo a 2018.

Asalin hoton, TWITTER/ATIKU ABUBAKAR

Atiku ya zamo mataimakin Cif Obasanjo tsakanin shekarar 1999 zuwa watan Mayu na 2007, bayan da Cif Olusegun Obasanjo ya zaɓo shi a matsayin wanda zai taimaka masa a lokacin da aka zabe shi a matsayin gwamnan Jihar Adamawa.

To sai dai alaƙar mutanen biyu ta yi tsami lokacin da Obasanjo ya nemi ya tazarce a karo na uku.

To sai ƴunkurin Atikun na maye gurbin Obasanjo a karshen wa'adin mulkinsa, 2007 ya ci tura sakamakon takun saka tsakaninsa da Obasanjon.

An yi ta ci gaba da samun takaddama tsakanin Obasanjo da tsohon matakimakinsa Atiku na tsawon shekaru har bayan komawa jam'iyyar APC da Atikun ya yi a 2015.

An taba ruwaito Obasanjo na cewa "zai yi iya bakin kokarinsa don ganin Atiku Abubakar bai shugabanci Najeriya ba."

Sai dai a wata hira da BBC ta yi da Atiku Abubakar, ya ce "Obasanjo ba shi ne Allah ba, kuma ba shi ne mutanen Najeriya ba."

Sai dai a 2018 dab da zaɓen 2019 an samu wasu fitattun ƴan siyasa da malamai na arewacin Najeriya da suka yi ƙoƙarin sasanta Obasanjo da Atiku.

Sheikh Ahmad Mahmud Gumi da Rabaran Mathew Hassan Kuka, na daga cikin malaman addinan da suka shaida sasantawar tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasar a jam'iyyar PDP a zaben 2019 wato Atiku Abubakar da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo da aka yi a gidansa da ke Abeokuta.

Me Atiku ya je yi wurin Obasanjo?

Obasanjo da Atiku

Asalin hoton, Abdurrasheeth/FB

Duk da cewa ganawar ta sirri ce sannan kuma babu wanda ya yi bayani dangane da abubuwan da ƴan siyasar suka tattauna, amma ganawar na zuwa ne a daida lokacin da jam'iyyun hamayyya ke ƙara fito da hanyoyin haɗa ƙarfi da ƙarfe a tsakaninsu domin tunɓuke jam'iyya mai mulki ta APC daga mulki a 2027.

Masu lura da al'amura dai na yi wa ziyarar kallon wani yunƙuri ne na ƙara neman sulhu da goyon baya da Atiku ke son samu daga Cif Obasanjo wajen tunkarar jam'iyya mai mulki ta APC a 2027.

Sai dai kuma kawo yanzu babu cikakken bayani da tabbaci dangane da ko Atiku Abubakar zai sake yin takara a 2027.

Atiku Abubakar dai ya yi takarar neman shugabancin ƙasar a jam'iyyar PDP har karo biyu.

Ana dai yi wa Cif Olusegun Obasanjo kallon babban mai hamayya da Bola Ahmed Tinubu wanda ba su taɓa haɗuwa ƙarƙashin lema guda ba a siyasance.