Kada a cutar da wasu jihohi a sabuwar dokar haraji - Atiku

Atiku Abubakar

Asalin hoton, Atiku Abubakar

Lokacin karatu: Minti 4

Jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi kira ga majalisar dokokin ƙasar ta yi aiki bisa gaskiya da riƙon amana wajen shirya taron jin ra'ayin jama'a kan sabon ƙudirin harajin ƙasar da ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar.

A makon da ya gabata ne majalisar dattawan ƙasar ta yi wa ƙudirin karatu na biyu, inda kuma yanzu ta miƙa shi ga kwamitin kuɗi na majalisar domin shirya taron jin ra'ayin jama'a kan ƙudurin.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, ya ce kan 'yan ƙasa ya haɗu wajen yin kira a samar da tsare-tsaren kuɗi bisa adalci da daidaito ga kowane yanki.

''Mun faɗa da babbar murya cewa bai kamata tsare-tsaren kuɗi da gwamnatin ƙasar ke son ingantawa su fifita wasu jihohin ƙalilan ta hanyar ruguza sauran ba'', in ji Atiku Abubakar.

''A matsayina na mai ruwa da tsaki, na yi imanin cewa gaskiya da adalci da riƙon amana da kyakkyawan shugabanci, na da matuƙar muhimmanci wajen tsara manufofi''.

Majalisar dattawan ƙasar ta ce ta amince da ƙudirin ne a karatu na biyu domin bayar da dama a shirya sauraron ra'ayin jama'a a kansa.

A hirarsa da BBC, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan ƙasar, Sanata Barau Jibril ya ce majalisar ta bayar da shawarar miƙa wa kwamitin kuɗi ya duba tare da shirya jin ra'ayin jama'a, kuma hakan ba zai yiwu ba har sai an yi wa ƙudirin karatu na biyu.

To sai dai tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce dole ne majalisar ta sauƙaƙa tsarin sauraron ra'ayin jama'ar ta yadda masu ruwa da tsaki za su samu damar zuwa su bayyana ra'ayoyinsu game da sabon ƙudirin.

''Dole ne sauraron ra'ayin jama'ar ya bayar da cikakkiyar dama, ta yadda kowa zai iya shiga ciki har da ƙungiyoyin fararen hula da sarakunan gargajiya, da 'yan siyasa da jami'an gwamnati da talakawa da ƙwararru'', in ji Atiku Abubakar.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya kuma yi kira ga majalisar dokokin ƙasar ta sake duba shawarar majalisar tattalin arziki kan ƙudirin.

''Ina so majalisa ta sake nazarin shawarar Majalisar tattalin arziki, wadda kundin tsarin mulkin kasa ya ba ta damar bai wa shugaban kasar shawara kan batutuwan da suka shafi tattalin arzikin ƙasa'', in ji shi.

A watan da ya gabata ne dai majalisar tattalin arzikin ƙasar - ƙarƙashin jagorancin mataimakin hugaban ƙasar da duka gwamnonin jihohin ƙasar 36 a matsayin mambobi - ta bai wa gwamnatin tarayya shawarar jingine sabon ƙudirn domin sake nazari a kansa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A farkon watan Oktoban wannan shekarar ne Bola Tinubu ya aika da wasu ƙudurori huɗu gaban majalisar dokokin ƙasar domin neman amincewarta.

Ƙudirin ya gamu da suka mai yawa musamman daga yankin arewacin ƙasar da al'ummar yankin ke zargin zai cutar da jihohin arewacin ƙasar.

Yayin wani taro da ƙungiyar gwamnonin arewacin ƙasar ta yi a Kaduna a ƙarshen watan Oktoba, sun ce sabon ƙudirin ya saɓa wa muradun jihohinsu, kuma suka yi kira ga ‘yan majalisar yankin su yi watsi da shi a zauren majalisar dokokin ƙasar.

“Abin da ya sa ba mu yarda ba shi ne, ana karɓar harajin VAT ne a hedikwatar kamfanonin maimakon inda sauran rassan kamfanonin ke gudanar da ayyukansu ko sayar da kayayyakinsu,'' in ji shugaban ƙungiyar Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya.

''Don haka ne ƙungiyarmu ta yi watsi da wannan sabon ƙudiri, kuma muke kira ga 'yan majalisar dokokinmu su yi watsi da shi saboda babu abin da ya ƙunsa ban da cutar da al'ummarmu.”

A makon da ke ficewa kuma Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya jaddada wannan matsaya a hirarsa da BBC, inda ya gargaɗi Bola Tinubu game da batun.

"Mun yi tir da wannan dokar da aka kai majalisa saboda zai kawo wa Arewa koma-baya...idan wannan ƙudirin ya wuce (nasara) ko albashi ba za mu iya biya ba," in ji shi.

"Ya kamata Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya duba wannan lamari, saboda kashi 60 cikin 100 na ƙuri'un da ya samu daga Arewa ne. Idan an yi mana abin da muke so to shi ke nan; abin da muke so yanzu shi ne a jingine maganar wannan haraji."

Sai dai gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na cewa sauye-sauyen za su rage wa ɗaiɗaikun 'yan ƙasa kuɗin haraji, da kuma buɗe sabbin ƙofofin tara kuɗaɗe daga harajin.