Me ƙudirin harajin VAT ya ƙunsa kuma me ya sa gwamnonin Arewa ke adawa da shi?

Bola Tinubu

Asalin hoton, @jidesanwoolu

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wata sabuwar dambarwa ta ɓarke game da ƙudurin harajin VAT da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike majalisar dokokin ƙasar, yayin da ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta fito fili ta yi fatali da ƙudurin, musamman kan yadda za a fasalta rabon harajin.

A farkon watan Oktoban wannan shekarar ne Bola Tinubu ya aike da wasu ƙudurori huɗu kan tsare-tsaren kuɗi ciki har da ƙudirin harajin VAT gaban majalisar dokokin ƙasar domin neman amincewarta.

Mene ne harajin VAT?

Harajin Value Added Tax (VAT) wasu kuɗi ne da ake ɗora wa kan wasu kayayyaki ko abubuwa da aka sarrafa idan mutum ya saya daga kamfanoni, kamar yadda Farfesa Muhammad Muntaqa Usman na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya shaida wa BBC.

Masanin tattalin arzikin ya ce a yanzu haka a Najeriya ana biyan kashi 7.5 na kuɗin abin da mutum ya saya.

''Abin da ake yi shi ne ko me ka saya, ana lissafa maka ƙarin kashi 7.5 cikin 100 na adadin kuɗin da ka saye shi domin ka biya'', in ji shi.

''Yadda ake karɓar harajin shi ne, kamfanin da ke sayar da kaya ko samar da ayyukan ne zai tattara, sannan ya miƙa shi ga asusun ofishin hukumar karɓar haraji na ƙasa."

Abubuwan da ba a ɗora wa VAT ba

Kamar yadda yake ƙunshe cikin kudirin karin harajin VAT na 2024, ba kowane abu ne aka dora wa harajin ba, inda aka keɓance wasu abubuwan.

Daga cikin abubuwan da aka kebe akwai kayan abinci kamar hatsi, da madara, da burodi, da ruwan sha, da abubuwan da suka shafi ilimi.

Me sabon ƙudirin ya ƙunsa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙudurin harajin VAT ya ƙunshi sauya yadda ake raba harajin ta yadda za a rage kason gwamnatin tarayya daga kashi 15 cikin 100 zuwa kashi 10 cikin 100, sai gwamnatocin jihohi su samu kashi 55, yayin da ƙananan hukumomi za su samu kashi 35 cikin 100.

"Amma sai suka ƙara wani sashe da ke nuna cewa duk kuɗin harajin VAT da aka tara za a cire kashi 60 cikin 100 na duka kuɗin, a kuma raba shi kawai a wurin da aka karɓi harajin'', kamar yadda Farfesa Muntaqa - wanda ya nazarci ƙudirin - ya yi ƙarin haske.

Sannan kuma ƙudurin ya zo da sabon fasalin yadda za a kasafta kuɗin harajin tsakanin jihar da ta mallaki kamfanin, da kuma inda kamfanonin ke aiki.

Ƙudirin ya kuma yi tanadin cewa kamfanonin da ke karɓar VAT za su riƙa kai harajin jihar da shalkwatarsu take maimakon jihohin da rassan kamfanin ke aiki.

''Suna so su yi amfani da fasalin raba kuɗin ribar mai, inda ake bai wa jihohin da ke da arzikn mai kuɗaɗe masu yawa, maimakon jihohin da ba su da mai'', in ji shi.

Haka kuma ƙudurin ya yi tanadin cewa za a ci gaba da ƙara harajin VAT ɗin har nan da 2030, inda ya yi tanadin cewa za a riƙa ƙara shi zuwa kashi 10 da kashi 12 har daga baya ya koma kashi 15 cikin 100 zuwa 2030, kamar yadda Farfesa Muntaqa ya yi ƙarin haske.

Kudi

Asalin hoton, Getty Images

Me ya janyo taƙaddamar?

A wani taro da gwamnonin arewacin ƙasar suka yi a Kaduna a makon nan, sun ce sabon ƙudirin ya saɓa wa muradun jihohin arewacin ƙasar, inda suka yi kira ga ‘yan majalisar yankin su yi watsi da shi a zauren majalisar dokokin ƙasar.

“Abin da ya sa ba mu yarda ba, shi ne saboda ana karɓar harajin VAT ne a hedikwatar kamfanonin, maimakon inda sauran rassan kamfanonin ke gudanar da ayyukansu ko sayar da kayayyakinsu,'' in ji shugaban ƙungiyar gwamnaonin Arewa, Muhammad Inuwa Yahaya.

''Don haka ne ƙungiyarmu ta yi watsi da wannan sabon ƙudiri, kuma muke kira ga 'yan majalisar dokokinmu su yi watsi da shi saboda babu abin da ya ƙunsa ban da cutar da al'ummarmu'' a cewar gwamnan na Gombe.

Shi ma Farfesa Muntaqa ya ƙarfafa wannan fargabar ta gwamnonin Arewa.

''Idan ka duba inda ake karɓar harajin, za ka ga cewa ana karɓar sa ne a hedikwatar kamfanonin, kamar bankuna da sauransu. Duk VAT ɗin ana tara shi ne a hedikwatar kamfanonin, to kuma yawancinsu suna Legas ne."

A nasa ɓangare shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan sauye-sauyen harajin, Taiwo Oyedele, ya ce kwamitinsu ya ji koken gwamnonin dangane da rashin daidaito da ke cikin sabon ƙudirin rabon harajin na VAT.

Sai dai ya ce manufar sabon ƙudirin shugaban ƙasar ita ce "ɓullo da tsarin da ya dace ta hanyar la'akari da wurin da ake samar da kayayyakin da kuma inda ake sayar da su, da kuma la'akari da jihohin da ke samar da muhimman kayayyaki ko da kuwa ba a biya musu harajin VAT".

Ya ce: ''Misali, jihar da ke samar da abinci bai kamata ta yi hasara ba saboda kayayyakinta ba su da harajin VAT, amma ana amfani da su a wasu jihohin''.

"Yana da kyau a yi la'akari da irin gudunmowar da kowace jiha ke bai wa ƙasar. Haka kuma kamfanonin sadarwa ma za a yi la'akari da wurin da masu amfani da layukan suke.

''Za mu yi aiki da masu ruwa da tsaki don magance wannan damuwa da nufin samun mafita, ta yadda zai yi wa kowane ɓangare daɗi."

To sai dai ba a sani ba ko waɗannan gyare-gyaren na cikin sabon ƙudirin da aka gabatar wa majalisar dokoki, ko kuma sai a nan gaba ne za a saka su cikin ƙudirin.

Wane tasiri zai yi ga arewacin Najeriya?

Farfesa Muntaqa ya ce matsawar aka ƙaddamar da wannan dokar to jihohin arewacin ƙasar ba za su samu kuɗin shigar da suke samu ba a baya.

''Kuma ka ga yankin ne ya fi mutane masu yawa, kuma shi ne zai samu kaso mafi ƙankanta kenan'', in ji Farfesa Muntaqa.

VAT ɗin da ake karɓar a Legas ya fi VAT ɗin da ake karbar a duka jihohin Najeriya.

Don haka idan ka ce, su ne za su amfana da shai 60 cikin 100, na kuɗin harajin, kenan jihohi iri su Zamfara da Jigawa da Katsina da babu wasu kamfanoni da ake karɓar VAT ɗin, za ka ga kuɗin da za su samu 'yan kaɗan nan''.

Idan har hakan ta tabbata ko duk kuɗin harajin zai koma ne ga jihohin Legas ta Fatakwal da Ogun, saboda duk yawanci can manyan kamfanonin ƙasar nan suke.

Ya ci gaba da cewa wannan ƙuduri babu abin da zai haifar wa yankin arewacin ƙasar, sai mummunan koma baya da karuwar talauci da yunwa.