Karin harajin kaya a Najeriya zai shafi talaka - Ndume

Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattijan Najeriya, Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce kara haraji kan kayayyaki da gwamnatin kasar ke shirin yi zai jefa talaka a cikin mummunan hali.
Tun dai bayan da majalisar dattawan kasar ta yi wa kudirin kara haraji kan kayayyaki karatu na uku a ranar Alhamis, al'amarin ke ci gaba da tayar da kura.
Sanata Muhammad Ali Ndume na daya daga cikin 'yan majalisar dattawa da ke yi wa kudirin kallon ba zai yi wa talakawan Najeriya dadi ba.
"Na amince da wasu haraji-haraji da aka sanya amma wannan ban ga alfanunsa ba ga talakawa kasancewar talakawa ne suka zabe mu."
"Allah yana gani ba na tare da wannan karin harajin," a cewarsa.
Sanata Ndume ya ce hukumomin da ke da alhakin karbar haraji sun kasa tara kudin da ya kamata su tara.
Ndume ya kara da cewa kaso 85 daga cikin kudin za a tura wa kananan hukumomi da jihohi wadanda talaka ba zai ci moriyarsa su ba.
Sai dai ya ce akwai wasu hanyoyin samar da haraji ba lallai ta hanyar kara haraji kan kayayyaki ba.
To amma Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya ce "gwamnati ta yi la'akari da talaka kafin fito da harajin," in da ya ce "harajin zai fi shafar kamfanoni."
Masu sharhi
Masana tattalin arziki irin su Dr Shamsuddeen Muhammad na jami'ar Bayero da ke Kano, ya ce harajin na da tasiri kan 'yan kasar.
"Ana tsammanin gwamnati za ta iya samun kudin shiga ta wannan bangaren duk da ba lallai ba ne domin akwai yanayin da kudin gwamnati ke samun tawaya maimaikon su karu."
Ya kara da cewa "Yanzu idan an sa wannan haraji abin da ake tsammani shi ne kayayyakin za su kara tsada, idan kayan suka kara tsada watakila kamfanoni ba za su samu cinikin da suke samu a baya ba domin kudaden da ke hannun jama'a sun ragu saboda tsadar kayayyakin
Kuma wannan zai iya sa kamfanoni su rage yawan kayan da suke sarrafawa sannan kuma sauran nau'o'in haraji kamar wanda ma'aikata kan biya ka iya raguwa."

Gwamnatin Najeriya dai ta amince a kara haraji kan kayayyaki daga kashi biyar cikin dari zuwa kashi 7.2 cikin dari.
Mininstar kudin kasar, Hajiya Zainab Ahmed, ta shaida wa manema labarai ranar Laraba cewa an dauki matakin ne lokacin taron majalisar ministoci.
Amma wannan sabon karin haraji ba zai soma aiki ba sai ya samu amincewar 'yan majalisar dokokin kasar.
Idan suka amince da sabon karin, zai soma aiki a shekarar 2020.
Zainab Ahmed ta ce an kara harajin ne domin gwamnati ta samu damar iya biyan albashin da aka kara wa ma'aikata na dubu talatin mafi karanci.
Ko da a watan Oktoban shekarar nan sai da shugaba Buhari ya nanata a majalisar kasar lokacin da ya ke gabatar da kasafin 2020.
Sai dai shugaban ya ce ba dukkanin kayayyaki ne harajin zai hau kansu ba.
"Dokar ta harajin na VAT ta tsame magunguna da kayan koyo da karantarwa da kayan more rayuwa....."
"Sashe na 46 da dokar kudi ta 2019 ta fadada kayayyakin da karin na VAT ba zai hau kansu ba da suka hada da:
- Biredi wanda aka yi da fulawa ko wanda aka yi da garin alkama
- Masara da shinkafa da alkama da gero da dawa
- Kifi da danginsa;
- Fulawa da abinci mai sitati;
- Kayan marmari da abubuwa masu kwanso da ganyaye
- Doya da gwaza da dankalin gida da na turawa
- Nama da kwai
- Madara;
- Gishiri da kayan kamshi
- Ruwa."

Gwamnatin mulkin soja karkashin jagorancin marigayi Janar Sani Abacha ce dai ta fito da sabon tsarin haraji inda ake karbar kashi biyar cikin dari kan kayayyakin da aka saya.
Amma gabanin saukarsa daga kan mulki a shekarar 2003, tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo ya kara haraji zuwa kashi goma cikin dari.
Sai dai gwamnatin marigari shugaba Umaru Musa 'Yar Adua ya komo da harajin zuwa kashi biyar cikin dari bayan kungiyar kwadago ta bayyana rashin jin dadinta.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne yadda kudirin dokar zai kwashe a majalisar wakilan kasar. Idan ita ma majalisar ta amince da shi to za a kai wa shugaban kasa ya sa hannu domin zama doka.
Idan har kudirin ya zama doka to zai fara aiki ne a 2020.










