Ndume ya ce kara harajin kaya zai jefa rayuwar talaka cikin mawuyacin hali

Asalin hoton, Other
Dan majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Muhammad Ali Ndume, ya shawarci gwamnatin Najeriyar game da yunkurinta na kara harajin kaya domin samun karin kudi yana mai cewa a maimakon haka, kamata ya yi gwamnatin ta bijiro da tsarin karbar haraji daga masu amfani da waya.
Sanata Ndume ya ce idan har gwamnati ta aiwatar da Karin harajin kaya, toh kuwa talaka ne zai shiga halin ni-'ya-su ta yadda farashin komai a kasuwa zai daga kama daga farashin mai da magani da mota da abinci.
Sanatan mai wakiltar Borno ta kudu a zauren majalisar dattawan ya bayar da misali da kasar Ghana da ita ma cikin 2008 ta samar da tsarin kara haraji ga masu amfani da waya inda masu amfani da wayar ke biyan kashi shida, a baya-bayan nan kuma, suna biyan kashi tara cikin dari.
Ya ce bayan da gwamnatin Ghanar ta samar da wannan tsari, ta rage harajin kaya (VAT) saboda talaka ya samu sauki ta wata fuskar.
A cewar Ndume, mutane kusan miliyan 60 ne suke amfani da waya a Najeriya wanda a ganinsa, wannan ce hanya mafi sauki da gwamnati za ta tara kudade.
Ya kara da cewa, ''duk wani mai waya a tsarin Najeriya ba talaka ba ne, idan kuma gwamnati ta yanke shawarar kara VAT, toh matakin zai fi shafar talaka ne.''
Ndume ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta talaka ce kuma kamar yadda ya ce, tuni marasa karfi a Najeriya suka fara yi wa wannan yunkuri na gwamnati kallon karin nauyi ne a garesu duk da ya ce wannan tsarin ba zai tabbata ba har sai gwamnatin ta gabatar wa majalisar dokokin kasar kudiri game da bukatar a kara harajin VAT, kudirin da zai zama doka idan majalisar ta amince da shi.
Sanatan ya ce kamata ya yi a gudanar da bincike domin zabo masu hali da ke amfani da waya wadanda su gwamnati za ta rika caja.
A cewar sanatan daga Borno, kamfanonin waya ma tuni suka fara sukar wannan kira nasa sai dai ya ce a kasar Ghana da take karbar haraji daga masu amfani da waya, irin wadannan kamfanoni sun shafe tsawon lokaci suna biyan harajin ba tare da tirjiya ba inda ya ce a Najeriya ma, bai ga dalilin da zai sa kamfanonin su bijire wa tsarin ba.










