Ko cire harajin shigo da kayan abinci zai sauƙaƙa rayuwa a Najeriya?

Hatsi

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Gwamnatin Najeriya ta ce za a gudanar da shirin ne har zuwa watan Disamban 2024
    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Bayan sama da wata ɗaya da fitar da sanarwar yafe harajin shigo da wasu kayan abinci Najeriya, a ƙarshe dai gwamnati ta ce an fara aiwatar da shirin.

Wata sanarwa da hukumar kwastam mai kula da safarar kaya ta fitar ranar Laraba ta ce shirin ya fara aiki tun daga ranar 15 ga watan Yuli kuma zai ƙare a ranar 31 ga watan Disamban 2024.

Kwastam ta ce an ƙaddamar da shirin ne bayan samun izini daga Ministan Kuɗi Olawale Edun, kuma an tsara shi ne da zimmar sauko da farashin kayan abinci cikin ƙanƙanin lokaci.

Tun a watan Yuli ministan noma ya ce an cire dukkan haraje-haraje kan shinkafa shanshera ko samfarera (wadda ba a gyara ba), da masara, da alkama, da wake, da jar dawa.

Sai dai hukumar kwastam ta ce kamfanoni ne kaɗai za su ci gajiyar shirin bisa wasu sharuɗɗa.

Matakin na zuwa ne mako ɗaya bayan zanga-zangar da 'yan ƙasar suka gudanar game da tsadar rayuwa, inda dubban matasa a duka jihohin Najeriya suka hau kan tituna.

Sai dai tambayar da 'yan ƙasar ke yi ita ce; ko hakan zai taimaka wajen cimma manufar gwamnatin ta sauƙaƙa farashin abinci a Najeriya?

Sharuɗɗan da aka saka kan shirin

Domin amfana da wannan shiri, hukumar kwastam ta zayyana sharuɗɗa aƙalla biyar da ta ce wajibi ne a cika su kamar haka:

  • Dole ne kamfanin da zai shigo da kayan ya zama mai rajista a Najeriya da ya shafe shekara aƙalla biyar yana aiki. Wajibi ne sai yana da bayanan ribarsa, da shaidar biyan haraji na shekara biyar ɗin.
  • Kamfanonin da za su shigo da shinkafa shanshera, da jar dawa, da gero, dole ne sai suna da kamfanin sarrafa su da ke iya sarrafa aƙalla tan 100 a kullum, kuma sai ya shekara biyar tare da mallakar isassun gonakin noma.
  • Waɗanda za su shigo da masara, ko alkama, ko wake, dole ne su zama kamfanonin noma da ke isassun gonaki
  • Tsarin ya tanadi cewa za a sayar da aƙalla kashi 75 na kayan da aka shigo da su ta wani keɓantaccen tsari, inda za a dinga ajiye rahoton duka hada-hadar da ake yi.
  • Wajibi ne kamfanonin su dinga adana rahoton duk ayyukan da suke yi waɗanda gwamnati za ta nema domin tabbatar da bin ƙa'ida.

"Idan kamfani ya gaza bin waɗannan ƙa'idoji, zai rasa damar kuma dole ne ya biya harajin fito, da na VAT, da sauransu," a cewar kwastam cikin wata sanarwa.

Ta ƙara da cewa: "Haka nan, za a hukunta duk kamfanin da ya fitar da kayan a gyare ko a ɗanyensu zuwa wata ƙasa bayan an shigo da su Najeriya."

'Ba su ne kayan abincin da talaka ke buƙata ba'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Babbar manufar gwamnatin Najeriya a kan wannan shiri ita ce sauko da farashin kayan abinci da za su sa yunwa ta ragu.

Sai dai wasu 'yankasuwa da manoma na cewa kayan da aka cire wa harajin ba su ne talaka ya fi buƙata ba.

"Talakawa fa abin da kawai suke dubawa shi ne shinkafa, da taliya, da semovita, da mai, amma babu ko ɗaya cikin waɗannan da aka cire wa haraji," a cewar Aminu Dan Iya shugaban ƙungiyar masu fiton kaya a arewacin Najeriya.

"Duk wani abu da za ka je kasuwa ka sayo yanzu-yanzu ka girka ka ci babu shi a cikin abubuwan da aka janye wa haraji. Masu kamfanoni ne kawai za su amfana a yanzu."

Ya ƙara da cewa da ma can shansherar shinkafa ba wani haraji ake biya mata ba saboda tana cikin kayan da ƙasashen ƙungiyar Ecowas suka amince da sauƙaƙa harajinsu.

"Da ma muna da yarjejeniya tsakanin ƙasashen Ecowas, inda ba a biyan harajin fito kan kayayyakin da ke iya lalacewa idan aka shigo da su daga ƙasashen ƙungiyar," in ji shi.

Ya ce sun daɗe suna fama game da yadda gwamnati ke ƙara kuɗin fito akai-akai, wanda ake aunawa da darajar canji tsakanin naira da dalar Amurka.

'Tsarin zai iya karya manoman cikin gida'

Duk da cewa tsarin ba dawwamamme ba ne, ƙungiyoyin manoma a cikin Najeriya na cewa hakan zai yi mummunan tasiri a kan ayyukansu.

Muhammad Magaji, shi ne sakataren yaɗa labarai na haɗaɗɗiyar ƙungiyar manoma ta All Farmers Association of Najeriya (Afan), ya faɗa wa BBC cewa zuwa lokacin da za a fara shigo da kayan manoma sun riga sun yi noma mai tsada.

"Babbar illarmu yanzu ita ce, idan aka fara kawo kayan zuwa watan Disamba to kayan za su yi yawa kuma hakan zai sa su yi sauƙi sosai saboda a lokacin ne manoma suke girbe amfaninsu kuma su kai kasuwa.

"Amma a lokacin ne ya kamata amfanin gona su yi daraja saboda manoma su mayar da kuɗaɗen da suka kashe wajen sayen kayan noma masu tsada a wannan lokaci.

"Da a ce za su sauya lokacin shigo da kayan zuwa kafin a fara shuka to zai iya taimakawa. Amma yanzu sai da muka gama kashe kuɗi wajen yin noma, wannan zai iya karya manoma da yawa."

To me ya kamata a ce gwamnatin ta yi? Sai Muhammad Magaji ya ce:

"A bai wa manoman rani manoma na gaskiya ba masu karɓa su sayar ba - famfon ban-ruwa mai aiki da hasken rana saboda mai ya yi tsada sosai. A ba su taki mai rahusa.

"Kuma yakamata a ce zuwa watan Oktoba an gama bai wa manomi duk wani tallafi da za a ba shi, saboda indai ya wuce wannan lokacin ba shi da amfani."

Za a ƙayyade farashin kayan

Tun a watan Yuli gwamnati ta ce tana sane da irin damuwar da ake da ita a kan nagartar abincin da za a iya shigowa da su daga waje ƙasashen waje.

Amma dai duk da haka za su ƙayyade wani yanki na farashi.

A cewar Ministan Noma Abubakar Kyari: "Duka kayan da aka shigo da su za a saka su a tsarin ƙayyade wani yanki na farashi [Recommended Retail Price (RRP)].

"Muna sane da damuwar da ake nunawa game da kayayyakin da ake shigowa da su, musamman game da hanyoyin da ake bi wajen girbe su. Gwamnati na tabbatar da cewa za a bi duk hanyoyin da suka dace na tabbatar da tsafta da lafiyar kayan abincin."