Su wane ne gwamnatin Najeriya ta yafe wa biyan haraji?

Takardun Naira

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Da yawan masu ƙananan sana'o'i a Najeriya sun karye saboda hauhawar farashi

Gwamnatin Najeriya ta amince da soke harajin cinikayya ga masu ƙananan sana'o'i, ciki har da rage haraji kan sana'o'in da ba su samun riba mai yawa, da kuma soke harajin baki ɗaya ga wasu masu masana'antu da manoma.

Shugaban kwamatin shugaban ƙasa kan harkokin haraji da hada-hadar kuɗi, Taiwo Oyedele, ya ce matakin wani ɓangare ne na sauye-sauye a harkokin harajin da zimmar shawo kan matsalolin haraji da aka daɗe ana fuskanta a ƙasar.

Ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo a shafinsa na dandalin X - wanda aka sani da Twitter a baya - ranar Talata.

Mene ne harajin 'withholding tax' da aka yafe?

Harajin da ake kira "withholding tax" a Turance shi ne kuɗaɗen da ake cirewa daga uwar kuɗi na mutane kamar 'yankwangila da dillalai da msu sarrafa kaya da masu gidan haya da sauransu.

Gwamnati ce ke karɓar harajin kai-tsaye a madadin waɗanda za su amfana da shi.

An ƙirƙiro shi ne a shekarar 1977 da nufin samar wa gwamnati kuɗaɗen shiga da kuma kare zirarewar kuɗaɗen na haraji.

Adadin abin da ake biya na withholding tax yanzu yana tsakanin kashi 5 zuwa 10 ne cikin 100, wanda ya danganta da nau'in cinikin da aka yi kamar biyan kuɗin haya, da kuɗaɗen da aka biya, da kuɗinj ruwa, da kuɗin aiki, da ribar da ake samu daga hannun jari.

Me ya sa gwamnati ta cire harajin?

Gwamnatin Najeriya ta ce a yunƙurinta na kawo a harkokin harajin ƙasar, an gano akwai matsala wajen fayyace irin mutanen da suka kamata su dinga biyan harajin.

Sauran matsalolin sun haɗa da halastattun ciniki, ko yawan abin da za a biya, da lokacin da za a biya.

Ta kuma ce ana kallon withholding tax a matsayin haraji na daban, wanda hakan ke nufin ƙarin haraji da kuma ta'azzara yawan abin da ake kashewa wajen yin kasuwanci, har ma da faɗaɗa rashin daidaito.

Gwamnati ta fahimci cewa cire wa masu sarrafa kaya harajin - kamar manoma - zai taimaka wajen rage hauhawar farashin abinci.

Hukumomi sun ce wannan sabon tsari zai taimaka wajen yakice wasu cin karo a cikin tsare-tsarenta, musamman waɗanda suka shafi masu ƙananan sana'o'i da aka cire su daga biyan haraji saboda ƙarancin ribar da suke samu.

Wane ne ke amfana da harajin kuma me zai faru da su yanzu?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A Najeriya, ana kallon masu ƙananan sana'o'i a matsayin 'yankasuwar da ba su samun ribar sama da naira miliyan biyar a shekara (kwatankwacin dala miliyan 16,500), da kuma ma'aikata ƙasa da 50.

Ƙasar mafi yawan al'umma a Afirka na fuskantar matsalolin tattalin arziki mafi muni cikin shekaru, inda hauhawar farashi ta kai kashi 33 cikin 100, ga kuma hauhawar farashin kayan abinci da kuɗin gudanar da ayyuka.

Farashin kayan miya ma ya yi mummunan tashi cikin shekara ɗaya sakamakon cire tallafin man fetur, da kuma faɗuwar darajar naira.

A ƙarƙashin wannan dokar, an tsame masu ƙananan sana'o'i daga biyan harajin na withholding tax. Sannan an rage yawan abin da za a dinga biya ga masu ƙaramar sana'ar.

Duk da cewa Najeriya za ta dinga rasa kuɗaɗen haraji daga wajen ƙananan 'yan kasuwar, Dr Olusegun Vincent yana ganin tsarin yana da tasiri na gajere da kuma tsawon lokaci a kan masu sana'o'i ƙanana.

"Gwamnati na mayar wa masu ƙananan sana'o'i kuɗinsu. Hakan zai sa su samu ƙarin kuɗin haɓaka harkokin kasuwancinsu ta hanyar ɗaukar ƙarin ma'aikata, wanda zai ƙara yawan arzikin da ake samarwa a cikin Najeriya [Gross Domestic Product] wanda ke fama da matsala," kamar yadda ya shaida wa BBC.

A shekarar 2020, kamfanin Price Water Coopers (PwC) ya ba da rahoton cewa ƙananan sana'o'i a Najeriya ne ke riƙe da kashi 96 cikin 100 na dukkan kasuwancin ƙasar; su ke da kashi 84 na ma'aikatan ƙasar; kuma su ne ke samar da kashi 49 na kuɗaɗen harajin ƙasar.

"Abu ne mai kaifi biyu. Gwamnati na neman kuɗaɗen haraji amma kuma zai fi kyau a bar sana'o'i su sakata su wala saboda hakan zai sa su cigaba da rayuwa duk ƙanƙantarsu. Zai kuma taimaka wajen rage hauhawar farashin abinci," in j Dr Vincent.

Zuwa yanzu hukumomi ba su saka ranar fara aiki da wannan sabon tsari ba, amma manoma da masu ƙananan sana'o'i za su yi murna da matakin.