Wane ne ɗan siyasar Birtaniya Nigel Farage?

Kusan shekara 30, Nigel Farage ya kasance jagoran masu adawa da kasancewar Birtaniya cikin ƙungiyar Tarayyar Turai. Ya jagoranci yaɗa manufar ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, shi ne kuma jagoran Jam'iyyar sauyi a Birtaniya.
Ya kasance mutum da ya riƙe muƙaman siyasa daban-daban da shiga harkar yaɗa labaru, sannan kuma ya sauya jam'iyyu a tsawon tarihinsa.
An haife shi a Kent, ya yi karatu a kwaleji mai zaman kanta a Dulwich da ke Kudancin birnin Landan, abokanan karatunsa na tuna shi da yadda ya riƙa ba malamai da ɗalibai haushi saboda maganganunsa masu janyo cece-kuce.
A lokacin da ya cika shekara 18 da haihuwa, ya yanke shawarar ba zai je jami'a ba, inda ya koma harkar kasuwanci.
Gwagwarmayar siyasa
Mista Farage ya fice daga jam'iyar Conservatives ta ƴan mazan jiya bayan da Birtaniya ta sanya hannu kan yarjejeniyar ƙasashen nahiyar Turai ta 'Maastricht Treaty' ta 1992, wadda ta ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashen Tarayyar Turai.
Yana cikin wanda suka kafa jam'iyar UK Independence Party (UKIP), daga nan kuma sai ya yi takarar ɗan majalisa a 1994, sai dai bai yi nasara ba.
A 1999 an zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar Tarayyar Turai mai waklitar Kudu maso Gabashin Birtaniya, inda ya kasance kan muƙamin har zuwa shekarar 2020.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan ya zama shugaban jam'iyyar UKIP a 2006, ya riƙa bayyana sosai a kafafen talabijin, kuma jam'iyarsa ta samu ƙuri'u sama da wanda jam'iyyun Labour da Lib Dems suka samu a zaɓen Tarayyar Turai na 2009.
Ya taka muhimmiyar rawa a tsare-tsaren ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, sai dai bayan da aka samu nasara a ƙuri'ar da aka kaɗa ta ficewa daga tarayyar Turai, sai ya fice daga jam'iyar UKIP.
Bayan da aka samu amincewar al'umma kan ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, ya ƙaddamar da jam'iyya mai ra'ayin ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai a watan Afirilu, 2019.
A lokacin da Birtaniya ta fice daga Tarayyar Turai, jam'iyyarsa ta sauya suna zuwa Reform UK. Mista Farage ya bar siyasa, inda ya koma mai gabatar da shirye-shirye a wani sabon gidan Talabijin na GB News
Gabanin zaɓen 2024 ya rinƙa iƙirarin cewa ba zai tsaya takarar majalisar dokoki ba.
Sai dai a ranar 3 ga watan Yuni, ya ce shi ne ɗan takarar jam'iyar Reform a mazabar Clacton kuma zai sake zama shugaban jam'iyar.
Manyan Alƙawurransa
Wasu daga cikin manyan alƙawurran da jam'iyar Reform UK ta yi:
- Shigowar baƙi: Dakatar da shigar baƙin da ba a buƙata da mayar da ƴan asalin ƙasashen ƙetare da suka aikata laifi gida, da kuma dakatar da masu tsallakowa cikin ƙasar ta kwale-kwale.
- Harkokin ƙasashen waje: Soke dokar Windsor Framework kan safarar kaya wadda aka ƙulla bayan ficewar Biratniya daga Tarayyar Turai. Fitar da Birtaniya daga yarjejeniyar kare hakkin bil'adama ta nahiyar Turai (ECHR), da kuma rage tallafin kuɗi da ƙasar ke bai wa ƙasashen ƙetare da kashi 50 cikin 100.
- Haraji da tattalin arziƙi: Ɗaga mafi ƙarancin kuɗin kamfanoni da za a iya cire wa haraji zuwa fan 100,000; ɗaga mafi ƙarancin kuɗin shiga na al'umma da za a iya cire wa haraji zuwa fan 20,000, soke harajin gado kan kadarorin da darajarsu ba ta kai fan miliyan biyu ba; soke "ƙa'idojin da ba a buƙata" kan haraji tare da sauƙaƙa tsarin biyan haraji.
- Aikata laifuka da shari'a: Ƙara yawan jami'an ƴansanda da kuma gina gidan yari 10,000.
To sai dai waɗannnan alƙawurra ne da za ta iya canzawa. Kwana ɗaya bayan da Mista Farage ya sake komawa kan shugabancin jam'iyyar Reform UK, an ga alamar yunƙurinsa na jingine ɗaya daga cikin manufofin jam'iyyar kan kwashe ƴan cirani zuwa wasu ƙasashe.
Ya ce a ba shi lokaci domin yin nazari.







