Abin da ya kamata ku sani kan babban zaɓen Birtaniya na 2024

uk flag and ballot box

Asalin hoton, Getty Images

Firaiministan Birtaniya, Rishi Sunak, ya sanar da cewa za a gudanar da babban zaɓen ƙasar a ranar 4 ga watan Yuli. Hakan na nuna cewa an matso da ranar zaɓen ba kamar yadda aka yi tsammani ba a baya, inda tun da farko aka buƙaci gudanar da shi a watan....

Mun yi duba ga wasu tambayoyi da kuke buƙatar sanin amsarsu kan zaɓen.

Yaushe ne za a gudanar da zaɓen na Birtaniya?

Za a gudanar da babban zaɓen Birtaniya ranar 4 ga watan Yulin 2024. Wa'adin shekara biyar ne jam'iyya ke yi kan mulki a Birtaniya, kuma jam'iyyar Conservative ce ta lashe zaɓen ƙasar da aka yi a watan Disamban, 2019, a dokance ya kamata a gudanar da babban zaɓen ƙasar a watan Janairun 2025.

Birtaniya ta kasu zuwa yankuna 650, waɗanda ake kira mazaɓu. Masu zaɓe a waɗannan mazaɓu na zaɓar ɗan majalisa guda ɗaya zuwa majalisar dokokin ƙasar domin ya wakilce su.

Yawancin ƴan takara na wakiltar jam'iyya ɗaya, sai dai wasu lokutan wasu na tsayawa a matsayin masu zaman kansu.

Me ya sa Rishi Sunak ya kira zaɓe da wuri?

Rishi Sunak, announcing the election day under heavy rain in London

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rishi Sunak, ya sanar da gudanar da zaɓen ne a Landan cikin tsananin ruwan sama

Jam'iyyar Conservative ta Rishi Sunak na rasa goyon baya a kuri'ar ra'ayin jama'a tun 2021.

Wasu ƴan siyasa a jam'iyyar na jin "abubuwa ba za su kyautata yadda ake buƙata, kuma suna ganin cewa buƙatar bai wa masu zaɓe damar yin zaɓe da wuri zai iya yin barazana ga faɗuwar jam'iyyar Conservative maimakon tura zaɓen gaba," in ji editan BBC kan harkokin siyasa Chris Mason.

"Hakan na nufin, a yi shi yanzu ko kuma komai ya taɓarɓare.

"Firaiministan zai iya jin cewa ya cimma wasu burikansa, ko kuma yana kan hanyar cimma su.

"Alkaluman hauhawar farashi za su iya zama a matsayin nasara. Duk da cewa ba abubuwan da gwamnati ta yi bane ya saka haka. Sai dai ana ɗora laifi kan gwamnatoci idan aka samu hauhawar farashi, don haka za a yi tsammanin cewa za su yi ƙoƙarin yaba kansu idan hauhawar ta faɗi - kuma ta faɗi.

Ta yaya za a kwatanta karfin jam'iyyun gabanin zaɓe?

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan ya nuna cewa tuni jam'iyyar Conservative ta Mista Sunak ta fara yaƙin neman zaɓe inda ta ɗara gaban abokiyar karawarta, Labour.

Hakan abin yake sama da shekara guda, inda jam'iyyar Labour ta ci gaba da samun kuri'u sama da kashi 40.

Voting intentions chart

Duk da cewa kuri'ar jin ra'yin jama'a wani lokaci ba za su iya kasancewa ba daidai ba, kuma Mista Sunak zai yi fatan raguwar farashi da kuma mayar da hankali kan tsare-tsaren kawo sauyi na jam'iyyar, za su taimakawa Conservatives samun nasara yayin da ake ci gaba da kamfe.

Duba da yadda abubuwa suke yanzu, jam'iyyar Labour za ta fara kamfe ne a sahun gaba kamar yadda kuri'ar ra'yin jama'a ta nuna.

Reform UK - wata jam'iyya mai ra'ayin rikau da ke adawa shigowar bakin haure - na a matsayi na uku, duk da cewa suna da magoya baya a faɗin ƙasar, amma hakan ba zai sa su samu kujeru a majalisar dokokin ƙasar ba.

Jam'iyyar Liberal Democrats - wadda a baya ta kasance jam'iyyu ta uku mafi girma a ƙasar - ba ta gaza samun kur'iu kashi 10 a kodayaushe, sai dai suna fatan ta hanayr mayar da hankali kan kujerun da suke buƙata, za su iya samun wani abun kirki a zaɓen da ke tafe.

Me zai faru da shirin Rwanda na Rishi Sunak?

A baya, Rishi Sunak ya yi alkawarin tura masu neman mafaka zuwa Rwanda kafin babban zaɓen ƙasar. Ya ce ɓullo da wani tsari zai zama jigonsa, inda ya ce hakan zai saka mutane su daina tsallakawa ta teku da ƙananan jirage zuwa Turai.

Sai dai bayan kiran zaɓe da wuri, ya ce tsarin zai fara aiki ne idan aka sake zaɓarsa ranar 4 ga watan Yuli.

Jam'iyyar Labour ta sha alwashin soke shirin na tura masu neman mafaka idan ta lashe zaɓe, abin ya aza ayar tambaya cewa ko za a iya tura ko da mutum ɗaya.

Shirin na Rwanda, wanda tuni ya lakume kuɗi dala miliyan 305, zai iya zama abin da zai raba jam'iyyun biyu cikin makonni shida na yaƙin neman zaɓe.

Su wane ne manyan ƴan takara?

Jam'iyyun biyu waɗanda ake sa rai za su samu yawan kuri'un da za a kaɗa, sun haɗa da jam'iyya mai mulki ta Conservatives da kuma ta Labour.

Firaiminista Rishi Sunak, mai shekara 44, shi ne ke jagorantar jam'iyyar Consrvatives. Yana da shekara 42 lokacin da ya zama Firaiminista a 2022, abin da saka ya zama mutum mafi kankantan shekaru da ya rike muƙamin a ɗan tsakanin nan. Shi ne kuma ɗan Birtaniya ɗan asalin Indiya na farko da ya taɓa zama Firaimin

Jagoran jam'iyyar Labour kuwa shi ne Sir Keir Starmer, mai shekara 61. An zaɓe shi shugaban jam'iyar ne bayan Jeremy Corbyn a 2020. A baya ya rike muƙamin babban mai gabatar da ƙara.

Me zai faru da majalisa da kuma ƴan majalisa kafin zaɓe?

british flag and the parliament building

Asalin hoton, Getty Images

Firaiminista ya buƙaci Sarkin Ingila da ya rusa majalisar ƙasar - domin rufe shi gabanin zaɓe.

Hakan zai faru ne ranar Alhamis, 30 ga watan Mayu.

Ƴan majalisa za su rasa ikonsu kuma za su tafi domin neman kuri'ar sake zaɓarsu idan suna ci gaba da zama a majalisar ƙasar.

Sama da ƴan majalisa 100 ne suka ce ba za su sake tsayawa takara ba a zaɓen da za a yi.

Gwamnatin ta shiga lokaci na kafin zaɓe, wanda ya hana duk wani aiki na ministoci da kuma hukumomi yayin yaƙin neman zaɓe.

Me zai faru bayan sanar da sakamakon zaɓe?

Bayan kirga kuri'u, Sarki zai buƙaci jagoran jam'iyyar da tafi yawan ƴan majalisa ya zama Firaiminista da kuma kafa gwamnati.

Shugaban jam'iyya ta biyu da ke da yawan ƴan majalisa, zai zama jagoran ɓangaren adawa.

Idan babu jam'iyyar da ta samu rinjayen ƴan majalisa - abin da ke nufin ba za a zartas da doka ba da ƴan majalisar ta kaɗai.

A wannan yanayi, jam'iyya mafi girma za ta yanke shawarar kafa gwamnatin haɗaka tare da wata jam'iyya ko kuma ta yi aiki a matsayin gwamati mara rinjaye, inda za ta dogara da kuri'u daga sauran jam'iyyu kafin zartas da doka.