Dokar Haraji: Matakan amincewa da ƙudurin doka a Najeriya

Ginin Majalisar dokokin Najeriya

Asalin hoton, NASS

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 6

Ana ci gaba da tattaunawa tare da nuna yatsa tun bayan da ƙudurin dokar haraji da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike wa majalisar dokokin ƙasar domin yin muhawara a kansa ya tsallake karatu na biyu a ranar Alhamis.

Ƙudurin - wanda ke ci gaba da janyo taƙaddama tsakanin ƴan ƙasar - gwamnatin ƙasar na ganin cewa zai taimaka wajen inaganta tattalin arzikin Najeriya.

An dai yi zazzafar muhawara a zauren majalisar dattawan ƙasar a ranar ta Alhamis tsakanin masu goyon bayan ƙudirin da masu adawa da da shi - da suka riƙa kiraye-kirayen watsi da shi.

Ƙudurin ya fuskanci turjiya mai ƙarfi musamman daga jihohin yankin arewacin ƙasar, waɗanda ke fargabar idan an amince da shi, zai mayar da yankin baya ta fuskar tara kuɗaɗen shiga.

Bayan muhawarar mai zafi tsakanin 'yan majalisar a ranar Alhamis- wadda har ta kai ga nuna yatsa tsakanin wasu 'yan majalisar - ƙudurin ya samu tsallake karatu na biyu a majalisar.

Tsallake karatu na biyu da ƙudurin ya yi a zauren majalisar, wani mataki ne na kama hanyar amincewa da shi domin ya zama doka a ƙasar.

Kan haka ne muka duba matakan da ƙudiri ke bi kafin ya zama doka a Najeriya.

'Sai ƙudiri ya bi matakai shida kafin ya zama doka'

Matakai shida da ƙudiri ke bi

Asalin hoton, Getty Images

Barista Sanusi Musa SAN, wani babban lauya masanin kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce akwai matakai da dama da ƙudiri ke bi kafin ya zama doka a Najeriya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mataki na farko: Tsohon ɗan majalisar dattawan ƙasar mai wakiltar Bauchi ta Arewa, Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa, ya ce a matakin farko shi ne idan aka kawo ƙudirin akan sanya shi cikin abubuwan da za a yi a wannan rana da ake kira 'Order Paper'

''Idan aka zo kansa shugaban majalisa ko shugaban masu rinjaye ko shugaban kwamitin da ƙudirin ke ƙarƙashinsa zai karanta a gaban majalisar, daga nan sai akawun majalisa ya sake karantawa, to wannan shi ake kira karatu na farko'', in ji Sanata Bulkachuwa.

Barista Sanusi Musa SAN ya ce ''Abin da kawai ake yi a wannan mataki shi ne a karanta ƙudirin a zauren majalisar, cewa ga ƙudirin da shugaban ƙasa ya aiko," in ji shi, inda ya ƙara da cewa a wannan mataki ko muhawara ƴan majalisar ba za su yi a kan kuɗirin ba.

Daga nan kuma sai a buga ƙudirin a mujallar majalisa domin kowane ɗan majalisa ya samu damar karantata ya kuma samu cikakken nazari a kansa kafin a je karatu na biyu.

Mataki na biyu: Mataki biyu shi ne yi wa ƙudiri karatu na biyu a zauren majalisar, kamar yadda Sanata Bulkachuwa ya bayyana.

''A wannan mataki ne wanda ƙudirin ke ƙarƙashinsa zai yi wa majalisa cikakken bayani kan abin da ƙudiri ya ƙunsa daga nan kuma sai a buɗe ƙofar muhawara a kansa, masu suka su yi, masu goyon baya su nuna'', in ji shi.

Bayan muhawara kan ƙudiri a karatu na biyu, daga ƙarshe sai shugaban majalisa ya tambayi ƴan majalisa cewa sun amince ya wuce wannan mataki na karatu na biyu, sai su amsa.

''Idan masu son ƙudirin ya wuce suka fi rinjaye a majalisar, shi ke nan sai ƙudirin ya wuce karatu na biyu zuwa mataki na gaba, idan kuma masu adawa suka fi yawa, to daga nan sai majalisa ta yi watsi da shi, shi ke nan ƙudiri ya mutu'', in ji Sanusi Musa SAN.

Mataki na uku: A wannan mataki ne za a miƙa wa kwamitin da ke da alaƙa da ƙudirin ko kuma kwamitoci masu alaƙa da shi a majalisa, inda su kuma za su shirya jin ra'ayin jama'a game da ƙudirin.

Sanata Bulkachuwa ya ce a wannan mataki sai an buga a jaridu da gidajen radiyo, duk wanda ke sha'awar cewa wani abu kan ƙudirin zai aike da takarda, kuma a kira shi a wajen jin ra'ayin domin ya bayar da cikakken bayanin abin da yake son cewa.

''Daga nan kafin ma a tashi za a so sanin inda ra'ayoyin jama'a ya karkata, kuma shi ne kwamitin zai tattara zuwa majalisa domin karatu na uku,'' in ji Sanata Bulkachuwa.

Kwamitocin za su ci gaba da aiki kan ƙudirin har zuwa lokacin da za su kammala tattara komai domin gabatar wa majalisa da rahoto, kamar yadda Barista Sanusi Musa ya bayyana.

Shugaban Majalisar Dattawa

Asalin hoton, President of the senate

Mataki na Huɗu: Matakin gaba shi ne karatu na uku, inda da farko majalisar za ta zauna a matsayin kwamiti, (Committe of The Whole).

''A wannan mataki shugaban majalisar zai sauko ya dawo cikin majalisar a zauna tare, duka ƴan majalisar, za su tsafe sashe-sashe na ƙudirin ɗaya-bayan ɗaya majalisar tana amincewa da shi, har a gama da duka sashe-sashe da ke cikin dokar'', in ji shi.

Bayan kammala wannan sai shugaban majalisar ya tashi ya koma kan kujerar shugabancinsa ya karanto rahoton abin da 'Commitee of Whole' ya amince da shi, sannan ya tambayi amincewar ƴan majalisar ko akasin haka.

Sanata Bulkachuwa ya ce daga nan sai shugaban majalisa ya nemi amincewar ƴan majalisar kan wannan ƙuduri domin ya wuce karatu na uku, ta hanyar tambayarsu da 'Yes ko No'.

Sai dai tsohon ɗan majalisar ya ce idan ƙudurin yana da zafi, to akwai hanyoyi uku da majalisa ke bi don tabbatar da amincewarsu kan ƙudirin.

''Mataki na farko shi ne 'Division' wato za a buƙaci ƴan majalisar da suka amince su ware gefe, waɗanda ba su amince ba su ware gefe, don a ƙirga a ga waɗanda suka fi yawa''.

''Ko kuma a riƙa kiran sunayen ƴan majalisar ɗaya bayan ɗaya ana tambayar ra'ayinsu game da amincewa da ƙudurin, ko kuma mataki na uku wanda shi ne za a yi amfani da ƙuri'ar ƴan majalisar,'' in ji Sanata Bulkachuwa.

Idan suka amince shi ke nan majalisa ta gama nata, inda kuwa suka ƙi amincewa da ƙudurin to nan ma ƙudirin ya mutu.

Mataki na biyar: Bayan ƙudiri ya zarce karatu na uku a duka majalisun dokoki biyu, sai majalisun biyu su kafa wani kwamiti da ake kira 'Commitee of Harmonization' inda za a warware duka saɓanin da aka samu a majalisun biyu kan ƙudiri.

Sanata Bulkachuwa ya ce daga nan sai majalisun su sake komawa su amince da bambance-bambancen da suka samu tun a farko, kamar yadda tsohon ɗan majalisar dattawan ya yi bayani.

''Daga nan kuma sai akawun majalisa ya rubuta wa shugaban ƙasa wasiƙa cewa majalisa ta amince da wannan ƙudiri domin sanya hannunsa'', in ji Barista Sanusi.

Shugaba Tinubu

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

Mataki na shida: Wannan shi ne matakin ƙarshe na yadda ƙudiri ke zama doka, wato matakin sanya hannun shugaban ƙasa, inda daga nan kuma ya zama doka a Najeriya.

''Idan aka kawo wa shugaban ƙasa, ƙudurin da majalisa ta amince da shi, to yana da kwana 30 ko dai ya amince da doka ko kuma ƙi amincewa da ita''.

Barista Sanusi ya ƙara da cewa idan shugaban ƙasa ya ƙi amincewa da doka, to zai rubuta wa majalisa dalilinsa na ƙin amincewa da ita, su kuma sai su sake nazarin dokar, ta hanyar biyo duka waɗancan matakai.

Me zai faru idan majalisa ɗaya ta amince da ƙudiri ɗayar kuma ta yi watsi da shi?

Yadda dokoki ke tabbata a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Barista Sanusi Musa SAN ya ce idan majalisar dattawa ta amince da ƙudiri ya wuce karatu na biyu ko na uku, amma majalisar wakilai ta yi wasti da shi a ɗaya daga cikin wadanann matakai, to ƙudiri ya mutu kenan.

''Haka ma idan ƙudiri ya wuce karatu na biyu ko na uku a majalisar wakilai, amma majalisar dattawa ta yi watsi da shi, to nan ma ƙudiri ya mutu,'' a cewar masanin shari'ar.

Ya ce dole ne sai duka majalin ƙasar biyu sun amince da ƙuduri a duka matakan kafin ya samu karɓuwa har ya isa teburin shugaban ƙasa domin sanya masa hannu.

A nasa ɓangare Sanata Bulkuwa ya ce idan aka samu saɓani a majalisun biyu, to wadda ta yi watsi da shi za ta yi ɗaya majalisar bayanin dalilanta na yin watsi da ƙudurin tare da kiranta da ta amince da ita.

''Idan ta gamsar da ita shikenan, idan kuwa ba ta iya gamsar daita ba, to shikenan ƙudiri ya mutu, domin kuwa majalisa daya ba ta doka'', in ji Sanata Bulkachuwa.