Ko majalisa za ta amince da sabuwar dokar haraji da ke tayar da ƙura a Najeriya?

Shugaba Tinubu

Asalin hoton, BAT

Lokacin karatu: Minti 3

Ƙudurin dokar da ta shafi harajin na ci gaba da tayar da ƙura a Najeriya inda wasu bayanai ke cewa shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da kamun ƙafa ga ƴan majalisar dokokin ƙasar domin ganin sun amince.

Bayanai na cewa shugabannin majalisun na ci gaba da wani zaman tattaunawa domin shawo kan sauran ƴan majalisar su amince da kudurin dokar, wanda shugaban kasa ke neman a gaggauta domin ta soma aiki daga ranar 1 ga watan Janairun 2025.

Sai dai ƴan adawa da wasu shugabanni musamman daga shiyar arewa na ganin dokar tamkar wani yankan baya ne na neman jefa yankinsu cikin karin wani kuncin talauci.

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ce tana son tabbatar sabon tsarin harajin daga cikin cikin matakan da take ɗauka na saita tattalin arzikin kasar duk da shawarar majalisar kula da tattalin arzikin Najeriya na dakatar da kuɗirin.

Yanzu kallo ya koma kan ƴan majalisa ko za su amince da kudirin dokar harajin da ake ci gaba da cecekuce?

Gwamnati ta ce babban dalilin sabuwar dokar harajin shi ne sake fasalin yadda ake karɓar harajin domin kawo ƙarshen ƙalubalen da gwamnati ke fuskanta kamar harajin birane daban-daban, rage nauyin harajin daga kan ɗaiɗaikun 'yan ƙasa da kasuwanci tare da taimakwa wajen kasuwanci domin samar da tattalin arziki da makoma mai kyau ga Najeriya.

Sai dai ƴan'adawa kamar Alhaji Buba Galadima jigo a jam'iyar NNPP ya ce suna kallon dokar ne kan cewa ƴan Najeriya sun hau kan siradi, "Allah kadai zai iya kuɓutar da mu sai ƴan majalisa da muka zaɓa."

Buba Galadima ya ce an matsawa ƴan majalisar lamba, "Ana amfani da dukkan wata dama, har da ta kuɗi don a shawo kan su, su tabbatar da wannan doka, wadda za ta cutar da al'ummar Najeriya ba ƴan arewa kaɗai ba."

"Duk ɗan majalisar da ya goyi bayan wajen tabbatar da wannan doka to maƙiyin al'ummarsa ne," cewar Buba Galadima.

Tuni dai gwamnonin jihohi arewa suka bayyana adawarsu da kudurin, tare da yin umarni ga wakilan yankin a majalisar tarayya su yi watsi da kudirin.

Rikicin kan harajin VAT tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya ya haifar da wasu manyan hukunce-hukuncen kotu da wasu da har yanzu ake shari'arsu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rashin ambatar harajin VAT a kundin tsarin mulkin 1999 ya ƙara rikita lamarin wanda hakan ya haifar da gibi. Bincikenmu ya gano tattara harajin a tarayya ya fi sauki da alfanu.

Da zarar an shawo kan taƙaddamar da ake yi, za a sanya batun VAT a tsarin mulki.

Yadda ake raba shi a yanzu tarayya 15 jihohi kashi 50 sai kuma ƙananan hukumomi kashi 35 zai dakata zai koma tarayya 10 jihohi 55 sai kuma ƙananan hukumomi kashi 35 cikin 100.

Daya daga cikin abubuwan da ke janyo cecekuce a kudurin dokar shi ne batun harajin da ake cirewa daga kuɗin da mutum ke samu wato Personal Income Tax a Turance.

A sabon ƙudurin dokar, an sake fasalin harajin da ake cirewa daga aljihun jama’a inda gwamnatin tarayya ta yi iƙirarin cewa za a ɗauke nauyin haraji daga kan masu ƙaramin ƙarfi.

Ƙudurin dokar dokar ya ce ba za a buƙaci mutanen da ke samun kudaden da suka yi kasa da naira 800,000 a shekara su biya haraji kan wadannan kudaden ba, har sai kuɗn da ake samu a shekara ya kai milaiyan 2.2 kafin ya fara biyan harajin kashi 15 cikin 100 a kai.