Naana Jane: Mace ta farko da za ta zama mataimakiyar shugaban ƙasar Ghana

Asalin hoton, Naana Jane Opoku-Agyemang/facebook
Al'ummar Ghana, musamman mata na murna kasancewar tsohuwar ministar ilimin ƙasar, Naana Jane Opoku Agyemang za ta kafa tarihin zama mataimakiyar shugaban ƙasa ta farko, bayan zaɓen da aka kammala a ƙasar.
Farfesa Opoku-Agyemang ta yi takara ne tare da John Mahama a ƙarƙashin jam'iyyar National Democratic Party (NDC), wadda ta yi nasara, kuma za su shiga fadar shugaban ƙasa a watan Janairun 2025.
Matar mai shekara 73 da haihuwa ta shiga fagen siyasar Ghana ne lokacin mulkin farko na shugaba John Mahama daga 2013 zuwa 2017 lokacin da ya naɗa ta ministar ilimi.
A lokacin da take minista ta kawo sauye-sauye, ta hanyar gina azuzuwa na zamani da samar da takardun karatu da kayan makaranta kyauta ga ɗalibai.
Mahama ya zaɓe ta a shekara ta 2020 a matsayin abokiyar takararsa, sai dai ba su yi nasara a zaɓen ba.
Ta kafa tarihi a ɓangarori daban-daban na ilimi, inda ta zama mace shugabar jami'ar Cape Coast ta farko daga 2008 zuwa 2012.
Haka nan ta samu kyautuka da dama daga ɓangarori daban-daban na duniya.
Farfesa Opoku-Agyemang ta kasance mai rajin kare hakkin bil'adama, inda take ƙoƙarin ganin an samar da ingantaccen ilimi da kuma kawar da cin zarafi mai alaƙa da jinsi a kan matan Ghana.
Tarihin Naana Jane Opoku-Agyemang

Asalin hoton, Prof. Opoku-Agyemang/X
An haifi Naana Jane Opoku-Agyemang ne a ranar 22 ga watan Nuwamban 1951 a yankin Cape Coast na ƙasar ta Ghana.
Ta yi karatun difloma da digirinta na farko ne kan harkar ilimi a jami'ar Cape Coast, yayin da ta yi digiri na biyu da digirin-digirgir a harkar adabin harshen Ingilishi a jami'ar York University da ke Canada.
Tana cikin jagororin hukumar kula da ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO).
Ta wallafa rubuce-rubuce a kan mata masu nazari kan adabi, da waƙe a Afirka.
Farfesa Naana Jane Opoku-Agyemang ta yi aure ne shekara 40 da suka gabata inda take da ƴaƴa uku da jikoki biyu.
Kasancewar ta a siyasa ya zamo mai ƙarfafa wa matan Ghana gwiwa inda take bai wa mata shawarar shiga harkar siyasa.
Ta taɓa lashe kyautar minista mafi ƙwazo a lokacin da take riƙe da muƙami.







