Hanyoyi biyar na yadda za ki zama uwa ta gari
Lahadi ta biyun watan Mayu ɗin kowace shekara ce ranar iyaye mata ta duniya.
An ware ranar ce domin tunawa da iyaye mata da hidimar da suke yi cikin al'umma.
A wannan shekara mun gayyato Jidda Mahuta, wata mai bai wa al'umma shawarwari kan rayuwa a Najeriya domin bayar da shawara ga mata kan yadda za su zama iyaye na gari.
Matashiyar ta zayyano wasu hanyoyi biyar na yadda mace za ta bi domin zama uwa ta gari
Kula da kai
Jidda Mahuta ta ce yana da kyau mace ta riƙa kula da kanta, domin kuwa sai ta kula da kanta ne za ta iya kula da 'ya'yan.
''Wajibi ne mace ta riƙa kula da kanta da lafiyar jikinta, domin samun ingantacciyar lafiya ne zai ba ta damar kula da kanta da ma 'ya'yanta'', in ji matashiyar
Kula da lafiyar ƙwaƙwalwa
Mai bayar da shawarwarin ta ceyana da kyau mace ta riƙa kula da lafiyar ƙwaƙwalwarta da na tunaninta domin samun damar shirya tunanin 'ya'yanta.
''Duka matar da ta ji ta fara samun matsala da lafiyar ƙwaƙwalwarta, to yana da kyau ta tuntuɓi likitan ƙwaƙwalwa''.
Sanin ilimin addini
Jidda Mahuta ta ce ilimin addini na da matuƙar muhimmanci wajen zama uwa tagari.
''Duk macen da take ƙoƙari wajen aiki da ilimin addini take kuma kare kanta da abubuwan da ddini ya haramta, za ku ga tana ƙoƙarin saka 'ya'yanta kan tarbiyya irin ta addini'', in ji Jidda.
Ta ce ko da 'ya'yanta sun kauce hanya za ta yi ƙoƙarin dawo da su kan hanya.
Ƙarfafa wa 'ya'yanta gwiwa
Uwa ta gari ita ce wadda ke ƙoƙarin ƙarfafa wa 'ya'yanta gwiwwa wajen cimma muradunsu.
''Duk uwar da take jajirtacciya wajen cimma burukanta, to za ku ga tana ƙoƙarin ƙarfafa wa 'ya'yanta gwiwa wajen cimma wannan ƙuduri''
Matashiyar ta ƙara da cewa a nan ya haɗa da koya wa 'ya'yanta ayyukan gida kamar girke-girke, da ladubban rayuwar rayuwa.
Iya zama da mutane
Uwa ta gari ita ce matar da ta ƙware wajen iya zama da mutane.
Jidda Mahuta ta ce duk uwar da ke da ilimin iya zama da mutane za ta yi ƙoƙarin koyar da ilimin ga 'ya'yan da ta haifa.
''Duk uwara da ta iya zama da mutane, za ta yi ƙoƙarin ɓoye duk wani abu na ɓacin rai da ke damunta ba tare da ta nuna wa wani ba, koda ta samu saɓani da mai gidanta, 'ya'yansu ba za su iya ganewa''.



