Bawumia na jam'iyyar NPP mai mulki ya amince da shan kaye a zaɓen Ghana

Bawumia

Asalin hoton, Mahamudu Bawumia/Facebook

Lokacin karatu: Minti 2

Dan takarar shugaban ƙasar Ghana na jam'iyyar NPP mai mulkin kasar, Mahamudu Bawumia ya amince da shan kaye a zaɓen.

Cikin wani gajeren jawabi da ya yi wa manema labari, mataimakin shugaban ƙasar ya ce bayan zaɓen da aka gudanar ranar Asabar a faɗin ƙasar hankulan jama'a sun karkata kan sanin samakon zaɓen.

''Kuma bisa ga bayanan da muka tattara daga cibiyoyin tattara sakamakonmu sun nuna cewa tsohon shugaban ƙasarmu, wanda ke takara a jam'iyyar NDC, John Dramani Mahama ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da gagarumin rinjaye'', in ji Bawunia.

Ɗan takarar na jam'iyya mai mulki ya kuma ce jam'iyyar hamayya ta NDC ta kuma samu gagarumin rinjaye a majalisar dokokin ƙasar.

''Duk da cewa muna dakon sakamakon wasu mazaɓun majalisar dokokin ƙasar, amma ina da yaƙinin cewa babu abin da zai sauya wannan sakamako (rinjayen NDC a majalisa)''.

''Kan haka ne na kira ɗan takarar jam'iyyar hamayya ta NDC, John Daramani Mahama inda na taya shi murnar kasancewarsa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Ghana'', in ji shi.

Tun da farko wasu ministoci, jiga-jigan gwamnatin NPP, sun sha kaye a kujerun majalisar dokokin ƙasar.

Kawo yanzu dai hukumar zaɓen ƙasar na kan aikin tattara sakamakon domin sanar da shi a hukumance kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

Zaɓen na Ghana na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsain tattalin arziki da hauhawar farashin kayyaki.

Wani abu da masana da dama ke ganin zai zame wa NPP barazana a lokacin zaɓukan.

Amincewa da shan kaye wani baƙon al'amari ne tsakanin 'yan siyasa a nahiyar Afirka, to sai dai a baya-bayan na wasu 'yan siyasar nahiyar sun fara rungumar wannan ɗabi'a, da masana siyasa ke ganin za ta taimaka wajen farfaɗo da ƙimar ɗan siyasa a idon duniya.

Ko a 2015 ma tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya amince da shan kaye tare da taya wanda ya kayar da shi - Muhammadu Buhari - murnar lashe zaɓen.

Haka ma a watan Maris ɗin da ya gabata ɗan takarar jam'iyya mai mulki a zaɓen shugaban ƙasar Senegal, Amadou Ba ya amince da shan kaye a hannun ɗan takarar jam'iyyar hamayya, Bassirou Diomaye Faye tare da taya shi murna.