John Mahama ya lashe zaɓen shugaban Ghana a hukumance

John Mahama na jam'iyyar NDC mai adawa riƙe da tutar Ghana

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, John Mahama ya lashe zaɓen da kashi 56.55
Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon Shugaban Ghana John Mahama ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.

Ya lashe zaɓen ne da kashi 56.55 na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen, inda ya kayar da Mataimakin Shugaban Ƙasa Mahamudu Bawumia na jam'iyyar NPP mai mulki.

Bawumia ya samu kashi 41.6, kuma ita ce tazara mafi yawa da aka samu a zaɓen ƙasar cikin shekara 24.

Tun da farko, an ruwaito cewa Bawumia ya taya Mahama murna ta waya tare da amsa shan kaye.

Shugabar hukumar zaɓe ta Ghana, Jean Mensa, ta ce kashi 60.9 cikin 100 na mutum fiye da miliyan 18 ne da ke da rajista suka fita kaɗa ƙuri'ar.

'Yantakara 12 ne suka fafata a zaɓen, sai dai takarar ta fi zafi tsakanin tsohon John Dramani Mahama na jam'iyyar NDC mai hamayya, da kuma mataimakin shugaban ƙasa mai-ci, Mahamudu Bawumia na NPP mai mulki.

Akwai kuma kujerun majalisar dokoki 275 da ake fafatawa a kansu.

Shugaban Ƙasa Nana Akufo-Addo zai sauka daga mulki ne bayan ya yi wa'adin shekara huɗu sau biyu.

Duba sakamakon zaɓen kai-tsaye