Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan sanda sun ceto mutum 77 daga coci a Jihar Ondo
Rundunar 'yan sandan Jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta ce ta ceto mutum aƙalla 77 akasrinsu yara ƙanana daga wata coci a jihar.
Mai magana da yawun 'yan sandan Ondo, SP Funmilayo Odunlami, ta shaida wa BBC Hausa cewa an tara mutanen ne a cocin tsawon watanni bisa alƙawarin cewa Yesu Almasihu zai sake bayyana yayin wata lacca da za a gudanar.
Ta ƙara da cewa sun kama babban faston cocin da ke yankin Valentino da mataimakinsa. Sai dai ta musanta batun cewa an ɓoye su ne a wani gidan ƙarƙashin ƙasa da ke cikin cocin.
Wasu hotuna da bidiyo da suka karaɗe shafukan zumunta sun nuna mutanen, yara da manya, a cikin motoci inda aka ce waɗanda aka ceto ne a kan hanyarsu ta zuwa hedikwatar 'yan sandan Ondo da ke Akure babban birnin jihar.
Tun farko rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Asabar cewa tana bincike kan rahoton "sace yara masu yawa" a yankin na Valentino.
Abin da ya sa mutanen suka tare a cocin
Rundunar 'yan sandan ta ce wasu daga cikin mutanen da aka ceto sun kasance a cocin tun daga watan Janairun 2022, inda suke kwana a gidan ƙarƙashin ƙasa.
"An faɗa musu cewa za a gudanar da lacca a watan Afrilu inda a wurin ne Yesu Almasihu zai dawo, " a cewar SP Odunlami. "Amma kuma daga baya aka ce musu sai Disamba za a yi laccar.
"Mahaifiyar wani yaro daga ciki ta ce ɗanta ya ɓata tun a watan Janairu kuma an gan shi a wurin."
Haka nan, wasu iyaye sun faɗa wa 'yan sanda cewa 'ya'yansu sun daina zuwa makaranta saboda jiran dawowar Yesu da cocin ta alƙawarta musu.
A watan da ya gabata ne wasu 'yan bindiga suka kashe mutum 40 a harin da suka kai kan wata coci da ke garin Owo na jihar ta Ondo.
Gwamnatin Najeriya ta ce ƙungiyar ISWAP mai iƙirarin jihadi ce ta kai harin. Sai dai ƙungiyar ta musanta zargin.
Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu ya ba da umarnin kafa kyamarorin tsaro a wuraren ibada da sauran na taruwar jama'a da zimmar inganta tsaro a jihar.