Ƴan bindiga sun kashe masu ibada da dama a wata coci a jihar Ondo

Lokacin karatu: Minti 2

Rahotanni a Najeriya na cewa wasu ƴan bindiga sun buɗe wa mabiya addinin Kirista da dama wuta a wata coci a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin ƙasar.

Rahotannin sun kuma ce ƴan bindigar sun kashe mutane da sace wasu da dama da ba a tantance adadinsu ba a harin na cocin.

Lamarin ya faru ranar Lahadi da rana a cocin mabiya Katolika ta St. Francis da ke bayan fadar sarkin garin Owo, wani babban gari mai tazarar kilomita 40 daga Akure babban birnin kasar.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa 'yan bindiga da dama ne suka mamaye cocin yayin da ake ci gaba da gudanar da ibada.

Ya ce sun yi harbi kan mai uwa da wabi, inda suka kashe wasu sannan suka yi awon gaba da wasu da ba a tantance adadinsu ba.

Gwamnatin Ondo ta yi Allah wadai da harin wanda gwamnan Jihar Rotimi Akeredolu ya bayyana a matsayin "shaiɗanci."

Shugaban cocin Father Andrew Abayomi ya shaida wa BBC cewa maharan sun abka cocin ne a yayin da yake ƙoƙarin rufe zaman ibadar a cocin.

Ya ce a lokacin da ya fara faɗawa mutane su tafi gida a lokacin suka fara jin ƙarar fashewa daga nan kuma sai suka ji harbe-harben bindiga.

"Bayan mun ji haka, na ba mutane umarnin kada su fita su ɓoye a cikin cocin, amma dole sai wasu sun fita."

"An ɗauki minti kusan ashirin, kuma daga lokacin da muka fahimci sun tafi, shi ne muka fito waje muka fara ɗaukar mutane zuwa asibiti," in ji shi.

Wani shaida ya faɗa wa BBC cewa ƴan bindiga ne da ba su rufe fuska ba suka abka cocin suka jefa abin fashewa sannan suka fara harbi.

Abin da gwamnatin Ondo ta ce

Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya siffanta harin da 'yan bindiga suka kai kan wata coci a jihar da "shaiɗanci" wanda "maƙiyan al'umma" suka kai yayin da ake tsaka da addu'o'i ranar Lahadi.

"Mummunan harin kuma na shaiɗanci wani shiri ne ɗaiɗaita zaman lafiyar mazauna Masarautar Owo da ke zaune lafiya tsawon shekaru," in ji shi.

Gwamnan wanda yanzu haka yake Abuja babban birnin ƙasar don shirye-shiryen babban taron jam'iyyar APC na ƙasa, ya ce zai katse aikin nasa don komawa gida ta'aziyya.

Zuwa yanzu babu cikakken adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai kan Cocin St Francis ta ɗariƙar Katolika da ke Ƙaramar Hukumar Owo.

Hotuna da bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta sun nuna gawarwaki cikin jini wasu kuma jibge a cikin mota.