Matsalar tsaro: 'Yan bindiga sun kashe kusan mutum 1,500 cikin wata guda a Najeriya'

Wani rahoto kan sha'anin tsaro ya ce an kashe kusan mutum 1,500 cikin watan jiya a Najeriya, sanadin ayyukan taɓarɓarewar tsaro da hare-haren 'yan fashin daji.

Bayanin na ƙunshe ne cikin rahoton tsaro wanda wani kamfanin harkokin tsaro mai suna Beacon Consulting yake wallafawa duk wata uku.

A cewarsa, ƙoƙarin gwamnati na hana ƙaruwar hare-hare da kashe-kashe da satar mutane don neman kuɗin fansa ya gaza a watan Maris, inda aka sace mutum 702.

Rahoton ya ce sakamakon tabarbarewar tsaro a kasar ta Najeriya musaman a yankin arewa maso yammacin kasar an samu mace-macen mutum 1,497.

Rahoton ya ce alkaluman da aka samu na da nasaba da yadda mahara suka fara amfani da bama-bamai wadanda ake sarrafawa a gida da ake kira IED.

Shugaban kamfanin na Beacon, wanda kwararre ne kan harkar tsaro, Dr Kabiru Adamu, ya shaida wa BBC cewa abubuwa da dama ne suka janyo taɓarɓarewar tsaron.

"Abubuwa da yawa ne suka janyo wadannan mace-mace, to amma wanda ya fi tasiri a cikinsu shi ne hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa kauyuka" in ji shi.

Rahoton ya kuma ce 'yan bindiga na kai wa jami'an tsaro da matafiya hare-haren kwanton-bauna kuma a yanzu suna amfani da bama-bamai tare da bude wa mazauna kauyuka wuta.

Nazarin da suka yi ya nuna cewa an samu karin sace-sacen mutane domin karbar kudin fansa da kashi 41 da digo 1 cikin 100 kuma a mace-macen mutane an samu kari na kashi 68 da digo 8 cikin 100 a tsakanin watan biyu da watan uku.

Rahoton ya bayyana rashin ingantaccen tsaro a kauyuka a matsayin babban dalilin da ya sa aka samun karuwa.

A cewar Dr Kabiru "Tsarin da ake bi a kasa yanzu bai ba ma kauyuka muhimmanci ba saboda haka akwai gibi."

Sai dai masanin ya ce wani abu da ya ba su mammaki shi ne a kaso na farko na wannan shekara na nazarin da suka yi sun ga cewa a watanni uku an samu mace-mace dubu 3,586 a kasar baki daya - amma a gefe daya an samu kashe-kashe na mutum 1,373 a arewa maso yamma, yayin da aka samu 958 a yankin arewa maso tsakiyya, a yankin arewa baki daya kuwa adadin ya karu da kashi 87 da digo 1.

Rahoton na zuwa a daidai lokacin da 'yan fashin daji ke ci gaba da kai hare-hare a yankin arewa maso yamma da jihohin da ke tsakiyar kasar.

Na baya-baya nan shi ne harin a 'yan bindiga su ka kai a wasu kauyuka a jihar Filato da ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 150.