Wagila: Yadda ake kera bindigogi domin tunkarar 'yan fashin daji a Sokoto

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Da alamu al'ummomin yakunan karkara a shiyar arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba amsa kiran da wasu mahukunta suka yi na su yi tattalin makamai domin kare kansu daga hare-hare ‘yan bindiga saboda yadda abin ke son gagarar kundila.

A yayin wata ziyara da ya kai a wasu kauyuka a jihar Sakkwato kwanakin baya, abokin aikinmu Haruna Shehu – Tangaza ya lura da yadda mutane musamman ‘yan banga ke tanadar wata bindigar gargajiya mai hadarin gaske da ake kira "wagila" domin kare garuruwansu.

Kan haka ne ma ya samu zantawa da daya daga cikinsu wanda ya fi son a bayyana shi da kawai Sarkin Bindiga yayin da shi ma ya sayo tasa wagilar.